Editor

9375 Posts
APC zaɓe ko ƙwace?

APC zaɓe ko ƙwace?

Ga dukkan alamu jam'iyya mai mulki APC tana daf da kwace duk kujerun gwamnonin arewa. Jihar Kano ce ta farko wajen yiwuwar ta zamo ta APC amma idan Kotun Ƙoli ta tabbatar da hakan. Sai jihar zamfara wacce ga alamu sai an sake zaɓe a wasu yankuna a tsakani gwamnan PDP mai karagar mulki da kuma tsohon gwamna na APC wanda minista ne a yanzu. Jihar Filato ma a cen kotu ta kwace kujera ta gwamnan PDP ta mayar ga gwamnan APC wanda su kai takara. Amma mu kula da kyau? Dukkanin inda a ke ƙwace kujeru na gwamnoni ko…
Read More
Batun sake duba dawo da martabar noma a Nijeriya

Batun sake duba dawo da martabar noma a Nijeriya

Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa, akwai gayar muhimmanci ga gwamnati ta sake duba batun bunqasa harkokin noma a ƙasar nan, duba da rawar da ɓangaren ke takawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasa da samar da wadataccen abinci. Ayyukan noma su ne ginshiƙi kuma babbar hanyar da za ta iya jure kowace irin kwaramniya ga ci gaban ƙasa tare da al’ummarta baki ɗaya. Noma babbar abu ce a Nijeriya, ana ma kallon cewa ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwuwa ba. Haka zalika, kamar…
Read More
Euro 2024: Ƙungiyoyin da suka samu gurbin shiga gasar

Euro 2024: Ƙungiyoyin da suka samu gurbin shiga gasar

Daga MAHDI. MUHAMMAD Ƙungiyoyi 20 sun samu gurbin shiga gasar Euro 22024 kai tsaye, inda Jamus za ta karɓi baƙuncin wasannin a 2024. Ingila, wadda Gareth Southgate ke jan ragama tana cikin tawagogin da za su jira raba jadawali, bayan da ta ja ragamar rukuni na uku, itama Scotland ta samu gurbi. Dukkan wadda ta yi ta daya da ta biyu a kowanne rukuni, su ne suka samu tikiti kai tsaye a wasannin da za a fara daga Yuni zuwa Yulin 2024. Yanzu kenan saura gurbi uku ya rage, inda tawaga 12 za ta buga wasannin cike gurbin shiga Euro…
Read More
Tinubu ya garzaya Kotun Ƙoli kan wa’adin amfani da tsofaffin takardun Naira

Tinubu ya garzaya Kotun Ƙoli kan wa’adin amfani da tsofaffin takardun Naira

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta garzaya Kotun Ƙoli domin neman a ƙara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin naira fiye da wa’adin da aka saka na ranar 31 ga watan Disamba, 2023. Idan dai ba a manta ba, Kotun Ƙoli ta soke dokar hana amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200, 500, da 1000 a matsayin doka a farkon shekarar nan. Dangane da haka, gwamnati na son Kotun Ƙolin ta ɗage umarnin da ta bayar na ranar 3 ga watan Maris na cewa a cigaba da amfani da tsofaffin takardun…
Read More
Ina da ƙwarin gwiwa kan ƙwarewar Malagi – Alake

Ina da ƙwarin gwiwa kan ƙwarewar Malagi – Alake

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Ma’adanai na Nijeriya, Dele Alake, ya ce, yana da ƙwarin gwiwa akam qwarewar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a Alhaji Mohammed Idris Malagi wajen gudanar da aikin ma’aikatarsa kamar yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi. Alake ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da Malagi ya kai masa ziyarar ban girma. Ya ce, Malagi ya cancanci naɗin nasa ne saboda halayensa na jagoranci da kuma rawar da ya taka wajen fitowar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.…
Read More
An yi wa yara miliyan 1.8 allurar rigafin cutar Ƙyanda a Katsina

An yi wa yara miliyan 1.8 allurar rigafin cutar Ƙyanda a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta yi wa yara 'yan kasa da shekara sha biyar su fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas allurar rigakafin cutar Ƙyanda a faɗin jihar. Babban sakatare na hukumar kiwon lafiya a mataki na farko Dr Shamsuddeen Yahaya ya faɗa wa manema labarai haka a ofishinsa. Haka ya ce yawan yara da akai wa rigakafin a faɗin jihar ya kai kashi ɗari da uku bisa ɗari. Dr Shamsuddeen ya kuma faɗa cewa an fara rigakafin ne a cikin watan jiya da ya ɗauki mako guda ana yi a ƙananan…
Read More
Ɗalibai 857 sun amfana da tallafin Cibiyar Cigaban Musulunci na Eggon, cewar Umar Galle

Ɗalibai 857 sun amfana da tallafin Cibiyar Cigaban Musulunci na Eggon, cewar Umar Galle

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Sakataren Cibiyar Cigaban Musuluncu na al’ummar ƙabilar Eggon na duniya baki ɗaya Malam Umar Galle ya ce bana kimanin ɗalibai ‘yan atsalin jihar Nasarawa dake karatu a jami’o'i daban-daban su 857 ne suka amfana da tallafin karatu da cibiyar ke basu wato Schoolarship a turance a kowace shekara don cigaba da karatunsu. Malma Umar Galle ya bayyana haka ne a wata zantawa ta musamman da yayi da ‘yan jarida a ofishin cibiyar dake Nasarawa-Eggon hedikwatar ƙaramar hukumar Nasarawa-Eggon a jihar Nasarawa ranar Talata 21 ga watan Oktoban shekarar 2023 da ake ciki. Ya ce…
Read More
Nijeriya na kashe wa duk mutum ɗaya Dala 10 a fannin lafiya kullum – Ministan Lafiya

Nijeriya na kashe wa duk mutum ɗaya Dala 10 a fannin lafiya kullum – Ministan Lafiya

Za a saka wa ƙasashen da ke kwashe likitocin Nijeriya haraji, inji shi Daga WAKILINMU Nijeriya na kashe wa kowane mutum ɗaya Dala 10 a duk ranar duniya ta fannin kiwon lafiya da inganta rayuwa. Ministan Lafiya na ƙasar, Farfesa Muhammed Ali Pate, shi ne ya bayyana haka a wani shiri da BBC Hausa ke yi lokaci bayan lokaci mai suna 'A Faɗa A Cika' da aka gudanar ranar Laraba a Abuja, lokacin da yake amsa tambayoyi game da abinda ya shafi ɓangaren lafiya, da suka shafi matsaloli, ƙalubale da kuma yadda za a magancesu. Ali Pate ya bayyana cewa…
Read More
Ɗalibar Jami’ar FUDMA ta kuɓuta daga hannun ’yan bindiga bayan kwana 50

Ɗalibar Jami’ar FUDMA ta kuɓuta daga hannun ’yan bindiga bayan kwana 50

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗaya daga cikin ɗalibai mata biyar na Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma, wato FUDMA, a Jihar Katsina da varayin daji su ka sace ta kuvuta daga hannun 'yan bindigar bayan shafe kwanaki hamsin su na garkuwa da ɗaliban. Kamfanin Dillacin Labarai na Nijeriya, NAN, ya ce ɗalibar ta samu 'yanci ne bayan da varayin suka sake ta, inda suka ajiye ta a wani gari da ake kira Kunci Kalgo dake qaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara daga nan ne kuma aka dawo da ita gida Katsina. Yanzu haka dai ɗalibar wadda ba a bayyana…
Read More
Ba za mu bari a yi zanga-zanga a Kano ba – ‘Yan Sanda

Ba za mu bari a yi zanga-zanga a Kano ba – ‘Yan Sanda

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'yan sanda a Jihar Kano, ta yi gargaɗin ba za ta bari a gudanar da zanga-zanga a jihar ba, walau ko don goyon bayan hukuncin kotu, ko kuma don adawa da hakan. Rundunar ta yi wannan gargaɗi ne musamman ga magoya bayan jam'iyyun NNPP da APC a Kano, inda aka ce magoya bayan jam'iyyun biyu sun shirya gudanar da zanga-zanga a jihar a ranar Asabar. An ce, yayin da magoya bayan NNPP za su yi zanga-zanga ne don nuna rashin yarda da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na soke nasarar Gwamna Abba, su kuwa 'yan APC za…
Read More