20
Dec
Daga MUHAMMAD AMINU IDRIS Huɗubar Jumu'a ko cin muntunci? Huɗubar Jumu'a ko hassada? Huɗubar Jumu'a ko bidi'a? Na ga wani Malami kuma Dakta, ban sani ba ko na ilimi ne ko na likitanci ne, ya yi sama da awa ɗaya a kan munbarin Jumu'a yana cin mutuncin ɗan uwanshi malami kuma Farfesa, kuma wai da sunan huɗubar jJumu'a yake yi! Lallai wannan abin kunya ne, abin baƙinciki ne kuma abin a yi Allah wadarai da shi ne tunda da sunan Musulnci yake yi. Annabi (SAW) ya yi gaskiya da ya ce: "babu ilimi idan babu aiki da shi." Kuma ya…
