Editor

9513 Posts
Da Ɗumi- ɗumi: ’Yan Majalisar Zamfara sun yi wa Kwamishinan Kasafi korar kare

Da Ɗumi- ɗumi: ’Yan Majalisar Zamfara sun yi wa Kwamishinan Kasafi korar kare

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta kori Kwamishinan Kasafi da Tsarin Tattalin Arziki na Jihar, Hon. Abdulmalik Gajam, gabanin Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya gabatar da kasafin 2024. Yayin zamansu a ranar Alhamis, ’yan Majalisar sun ce an kori Kwamishinan daga zauren ne saboda kin amsa gayyatarsu a can baya. Kazalika, ’yan Majalisar sun yi barazanar janye hurumin da ya bai wa Gajam damar zama Kwamishinan jihar. Daga bisani, Gwamna Dauda ya gabatar wa majalisar kasafin 2024 kamar yadda aka tsara tun farko.
Read More
Janar-janar 113 sun yi murabus daga Sojin Nijeriya

Janar-janar 113 sun yi murabus daga Sojin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Wata sanarwa daga rundunar Sojin Nijeriya ta yi nuni da cewa, janar-janar su 113 ne suka yi murabus ko kuma ke shirin yin murabus daga sojin Nijeriya a wannan shekara ta 2023. Sanarwar da ta yi wannan bayanin ta fito ne ta bakin Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, a ranar Laraba, 20 ga Disamban 2023. Sanarwar ta kara da cewa, Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi yabo da jinjina ga manyan jami’an sojojin da lamarin ya shafa bisa sadaukarwar da suka yi wajen yi wa kasa hidima bil hakki. Abubakar ya yi wannan yabo ne…
Read More
Gwamna Lawal ga sabbin alkalai, ku zamo masu gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da ke kanku

Gwamna Lawal ga sabbin alkalai, ku zamo masu gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da ke kanku

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya kalubalanci sabbin alkalai (Khadis) na Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci a jihar da su zamo masu gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. A ranar Laraba Babbabn Alkalin Jihar ya rantsar da sabbin Khadi a Fadar Gwamnantin jihar da ke Gusau, babban birnin jihar. Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta nuna kotunan shari’a na taka muhimmiyar rawa a tsarin shari’ar jihar. Bala Idris ya bayyana cewa a 1999 ne aka fadada kotunan shari’a a Jihar Zamfara inda…
Read More
Ilimin manya makami ne na gyara al’umma – Amina Ahmed Gumel

Ilimin manya makami ne na gyara al’umma – Amina Ahmed Gumel

"Rashin Turanci ne ke taka wa mutanen mu birki a Turai" Daga ABUBAKAR M. TAHIR Amina Ahmed Sani Gumel 'yar Nijeriya ce wanda ta ke zaune a Kasar England inda ta ke koyar da ilimin manya masu koyon yaren Turanci a matsayin yare na biyu. A cikin tattaunawarta da wakilin manhaja, ta kawo irin hanyoyin da suke bi wajen koyar da mutane baqi yaren Turanci wanda zama ya kama su a Kasar England. Haka kuma ta kawo irin qalubalen da ta fuskanta wajen yaren Turanci dama irin nasarorin da ta samu a matsayin mai koyar da yaren Turanci a Kasar…
Read More
2024: Gwamna Raɗɗa ya rattaɓa hannu kan kasafin N454.3bn

2024: Gwamna Raɗɗa ya rattaɓa hannu kan kasafin N454.3bn

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dikko Umaru Radda ba Jihar Katsina ya rattaba hannu kan kasafin 2024 ya zama doka biyo bayan amincewa da kasafin da Majalisar Dokokin Jihar ta yi. A ranar Laraba Gwamnan ya sanya wa kasafin hannu a Fadar Gwamnatin Jihar, kasafin da jimillarsa ta kai N454,308,862,113.96. Da yake jawabi bayan rattaba hannu kan kasafin, Gwamna Radda ya yi gidiya ga majalisar jihar bisa hanzarin da suka yi wajen dubawa da kuma amincewa da kasafin a cikin kwana 33. Kazalika, ya jinjina wa Mataimakin Gwamnan Jihar da majalisar zartawa da daukacin wadanda suka bada gudummuwa wajen kammaluwar kasafin.…
Read More
Ƙungiyar ‘yan jarida ta karrama Shekh Rigi-rigi Kusfa

Ƙungiyar ‘yan jarida ta karrama Shekh Rigi-rigi Kusfa

Daga ISA GIDAN BAKKO a Zaria A makon jiya ne Kungiyar Mawallafa Jaridu ta Arewa 'AREWA PUBLISHEUM' ta karrama fitaccen malamin addinin Musuluncin da ke Zariya mai suna Malam Usman Bini Shekh Idris Kusfa, saboda jajircewarsa wajen ilmantar da al'umma ilimin addinin Musulunci a ciki da kuma wasu kasashe da ke makotaka da Nijeriya. Taron karrama fitaccen malamin ya gudana ne a Zawiyyarsa da ke Unguwar Kusfa a Birnin da kuma ya sami halartar muridansa da kuma wasu fitattun malamai da suke Zariya. Dokta Sani Garba shi ne mataimakin shugaban kungiyar da ya jagoranci karrama wannan malami, ya ce kungiyarsu…
Read More
Ƙungiyar BudgIT ta yi iƙirarin gano maimaicin ayyuka a ƙudurin kasafin kuɗin 2024

Ƙungiyar BudgIT ta yi iƙirarin gano maimaicin ayyuka a ƙudurin kasafin kuɗin 2024

Daga MADHI M. MUHAMMAD Wata kungiya mai bibiyar harkokin kasafin kudi da ake kira 'BudgIT Nigeria' ta nemi gwamnatin kasar ta sake nazarin kudurin kasafin kudin 2024 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na X, BudgIT Nigeria ta bayyana damuwar cewa bayan cikakken nazari kan abin da kudurin kasafin kudin ya kunsa, ta lura cewa gwamnatin Tinubu ta cigaba da aiki da tsarin kasafin kudi mai cutarwa daga gwamnatin da ta gabata, da ke dabbaka cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da kuma fatara. Sanarwar…
Read More
Lalong ya sha rantsawar zama Sanatan Filato ta Kudu

Lalong ya sha rantsawar zama Sanatan Filato ta Kudu

Daga BASHIR ISAH An rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, a matsayin sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya. Lalong ya yi murabus ne daga muƙamin Ministan Ƙwadago a gwamnatin Tinubu sannan ya maye gurbin Napoleon Bali na Jam'iyyar PDP wanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sauke shi biyo bayan ƙarar da Lalong ya shigar a kansa a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe. Akawun majalisar, Chinedu Akubueze, shi ne ya rantsar da Long yayin zaman majalisar a ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio. Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da Lanlon a matsayin…
Read More
‘Yan Arewa mu ci gaba da barci!

‘Yan Arewa mu ci gaba da barci!

Hari ko kuma kuskuren da sojoji suka yi na jefa bam a Kaduna ga masu yin Maulidi zai tayar wa da duk wani mai tausayi ko imani hankali. Ɗauke Batun ɗarikar Addini. Ɗauki ɗan'adamtaka (Humanity). Shin wannan mugun zubar da Jinin bayin Allah da basu ji ba, ba su gani ba. Basa fauke da makami. Bai isa mutum ya zubar da hawayen tausayi gare su ba?. Idan kana ganin ai 'yan bidi'a ne akai musu haka kana Jin daɗi a ranka. Kai ma wani lokacin ɗarikar da kake kai za a iya cimmata ta wannan ƙudurin tunda ba mu haɗa…
Read More
Yadda za ku gamsar da iyalinku yayin mu’amala ta aure (2)

Yadda za ku gamsar da iyalinku yayin mu’amala ta aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinku na zamantakewa mai zuwa kowanne mako a jaridarku ta Manhaja Blueprint. A makon da ya gabata mun kawo muku wasu bayanai a kan yadda ma'aurata za zu samu damar daɗewa a yayin da suke tarayyar aure. Ba shakka waɗannan dabaru da ƙanina ya rubuto za su taimaka matuƙa wajen samun gamsuwa tsakanin ma'aurata. A makon da ya gabata mun fara kwararomuku bayanai, sai muka tsaya saboda sarari ya cika. Yanzu sai ku gyara tabaronku don cigaba da karanta bayanai daga makon da ya gabata.…
Read More