Editor

9513 Posts
Addinina ya koyar da ni yin adalci ga kowa -Tinubu

Addinina ya koyar da ni yin adalci ga kowa -Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed ya jaddada aniyarsa ta yi wa kowa adalci a mulkinsa tare da tabbatar da ya haɗa kan 'yan Nijeriya da samar da walwala ga ƙasar da 'ya'yanta. Da yake jawabi bayan kammala sallar Juma'a a babban masallacin Ansar-Ud-Deen da ke Suruleren, Jihar Legas, a ranar Juma’a, Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta ɓullo da su na da nufin samar da tsayayyen tushe da 'ya'ya da jikokin 'yan Nijeriya za su mora. Shugaba Tinubu, wanda ya bi sahun al’ummar Musulmi wajen gudanar da addu'o'in bikin cikar ƙungiyar Musulmi ta Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria shekara…
Read More
Gwamna Dauda ya gabatar da kasafin 2024 

Gwamna Dauda ya gabatar da kasafin 2024 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 na Naira biliyan 423,523,730,000.00 ga majalisar dokokin jihar. Taken kasafin kuɗin jihar Zamfara na 2024 shi ne “Kasafin Ceto” kuma an gabatar da shi ne a ranar Alhamis a zauren majalisar dokokin jihar da ke Gusau. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce kasafin kuɗin da aka gabatar ya haɗa da Naira 118,134,730,000.00 na kashe kuɗaɗe na yau da kullum da kuma N305,389,000,000.00 na kashe kuɗaɗe. A cewarsa, gwamnatin jihar Zamfara na shirin…
Read More
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta bai wa ɗaliban da aka ceto tallafin karatu

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta bai wa ɗaliban da aka ceto tallafin karatu

Daga UMAR GARBA a Katsina Uwargidan Shugaban Ƙasa Sanata Oluremi Tinubu ta tallafa wa ɗaliban jami'ar gwamnatin tarayya ta Dutsinma da aka kuɓutar daga hannun 'yan ta'adda. Oluremi Tinubu ta bayar da tallafin ne lokacin da ta karɓi baƙuncin huɗu daga cikin ɗalibai biyar na jami’ar. Babbar mai taimaka wa uwargidan shugaban ƙasar ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Busola Kukoyi, ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta saka wa hannu. Kowace yarinya ta samu tallafin karatu Naira milyan ɗaya  da sabuwar kwamfutar tafi da gidanka. Tun farko Shugaba Tinubu ya bayyana cewar  gwamnatin tarayya za ta bai wa…
Read More
Hukumar Abuja za ta rusa gidaje 200 don gina filin saukar jirgin shugaban ƙasa

Hukumar Abuja za ta rusa gidaje 200 don gina filin saukar jirgin shugaban ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya umurci daraktan sashen kula da cigaban ƙasa da ya tabbatar da cewa al'ummar Nuwalege da ke kan titin filin jirgin sama sun ba da fili don gina filin saukar jirgin shugaban ƙasa. Umarnin ya biyo bayan buqatar da rundunar sojin saman Nijeriya ta gabatar. Da ya ke magana ta bakin Daraktan, Mukhtar Galadima yayin wani taron al’umma da ’yan ƙasa a ranar Talata a Abuja, Ministan ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi al’umma su ba da damar cigaba. A cewarsa, “Kimanin wata guda da ya gabata ne…
Read More
Al’ummar Ebira mazauna Kebbi sun karrama Gwamna Nasir 

Al’ummar Ebira mazauna Kebbi sun karrama Gwamna Nasir 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Ƙungiyar mutanen Ebira a jihar Kebbi ta bai wa Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi lambar yabo. bikin bajekolin al'adu da karramawar jama'a wanda ya gudana a jiya a ɗakin taro na Saffar da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi. Da yake jawabi a wajen taron da ya halarta, shugaban ƙungiyar Malam Suberu Asuku Iliyasu ya bayyana karramawar ga Maigirma Gwamnan ya samu kyakykyawan sakamako bisa la'akari da ci gaba da haɗin kai da ya kawo jihar Kebbi tun bayan hawansa karagar mulki watanni bakwai da suka wuce. Ya ƙara da cewa an…
Read More
Na yi ritaya daga siyasa, cewar Abdullahi Adamu

Na yi ritaya daga siyasa, cewar Abdullahi Adamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ya yanke shawarar barin harkokin siyasa, inda ya ce ya lura cewa siyasa ta fita daga ran sa. Adamu ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da wani littafi mai suna ‘Progressive Governance, Showcasing The Achievements of Governor Abdullahi Sule of Nasarawa State 2019–2023’ wanda Abdullahi Tanimu ya wallafa. Tsohon shugaban jam’iyyar APC ɗin, wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a jihar, kuma ya yi mulki a tsakanin 1999 zuwa 2007, yayin da yake magana kan littafin mai shafuka 230, ya…
Read More
Mai tsaron raga da mataimakin kocin Algeria sun mutu a haɗarin mota

Mai tsaron raga da mataimakin kocin Algeria sun mutu a haɗarin mota

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani haɗarin mota da ya faru a Algeria ya halaka nai tsaron raga da kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Mouloudia Club El Bayadh lamarin da ya tilastawa hukumar ƙwallon ƙafar aasar ɗage dukkan wasannin da aka tsara bugawa. Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar ya ce, mai tsaron ragar ƙungiyar Zakaria Bouziani mai shekara 27 da mataimakin koci, Khalid Muftah sun mutu sanadin haɗarin. ’Yan wasan na hanyar zuwa Tizi Ouzou domin buga wasa da JS Kabylie ranar Juma'a lokacin da motar ɗauke da tawagar ’yan wasan ta yi haɗari kusa da birnin Tiaret da ke Arewa…
Read More
Kasafin 2024: Ba a ware wa ƙidayar 2024 ko sisi ba, inji Majalisar Dattawa

Kasafin 2024: Ba a ware wa ƙidayar 2024 ko sisi ba, inji Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ’Yan kwamitin Majalisar Dattawa kan kasafin kuɗi sun kaɗu a ranar Talata bayan da aka sanar da su cewa babu wani tanadi da aka tsara na ƙidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2024 a cikin ƙudirin kasafin kuɗin hukumar ƙidaya ta ƙasa. Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da yawan al’umma ta ƙasa Sanata Abdul Ningi (PDP Bauchi ta tsakiya) ne ya sanar da ’yan majalisar halin da ake ciki a lokacin da yake gabatar da rahoton kasafin kuɗin NPC na 2024 ga kwamitin tattara bayanai. Ya shaida wa kwamitin cewa idan ba a samar…
Read More
Kotu ta haramta wa tsohuwar minista riƙe muƙami

Kotu ta haramta wa tsohuwar minista riƙe muƙami

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata babbar kotu a Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar Litinin, ta yanke hukuncin haramta wa tsohuwar ministar harkokin mata, Dame Tallen riƙe duk wani muƙamin gwamnati a cikin ƙara mai lamba CV/816/2016. Don haka, Kotun ta bayyana cewa furucin Tallen ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki, rashin ɗa'a ne, rashin kunya, kiraye-kirayen ƙin bin hukuncin kotun, don haka ta raina babbar kotun tarayya ta Nijeriya. Kotun ta kuma bayar da umarnin da ke hana tsohuwar ministar riƙe duk wani muƙami a Nijeriya, sai dai idan ta wanke kanta daga halin da ake ciki ta hanyar…
Read More
Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukunci kan zaɓen Gwamnan Kano

Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukunci kan zaɓen Gwamnan Kano

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukuncin zaɓen gwamnan Kano zuwa wani lokaci da ba ta ambata ba. Zaman da Kotun ta yi mai alƙalai biyar a ranar Alhamis, ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Inyang Okoro. A ranar 17 ga Nuwamban 2023 Gwamnan Kano, Abba Yusuf da Jam'iyyarsa ta NNPP suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli inda suke ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke nasarar da Gwamna Abba ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ran 19 ga Maris. Kazalika, jam'iyyar ta nusar da Kotun Ƙolin dambarwar da ta auku a hukuncin…
Read More