Editor

9513 Posts
Fiye da mutum 50,000 ke zaman jiran shari’a a gidajen kurkukun Nijeriya – Jami’i

Fiye da mutum 50,000 ke zaman jiran shari’a a gidajen kurkukun Nijeriya – Jami’i

 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana cewa akwai sama da mutum 50,000 tsare a kurkuku daban-daban cikin kasar nan, wadanda ke zaman tsammanin jiran a yanke masu hukunci a kotuna daban-daban. Wani jami’i ne ya tabbatar da haka, inda ya ce kashi 69 bisa 100 na wadanda ke tsare a gidajen kurkuku, duk jiran a yanke masu hukunci suke yi. Hukumar Kula da Gidajen Kurkukun Nijeriya (NCoS), ta ce akwai mutum 53,836 tsare a gidajen kurkuku daban-daban, wadanda ke zaman jiran a yanke masu hukunci a gidajen kurkuku 253 da ke cikin kasar nan. Wannan kididdiga dai za…
Read More
An dakatar da kansila a Kebbi bisa zargin rashin taɓuka aiki

An dakatar da kansila a Kebbi bisa zargin rashin taɓuka aiki

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Kansiloli bakwai daga cikin 11 da ke akwai a Karamar Hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi sun tsige Hon Samaila Muhammad Felande, kansila mai wakiltar Mazabar Felande daga mukaminsa na Shugaban Kansiloli, wato Council Leader, bisa ga zargin rashin tabuka wani abin a-zo-a-gani wajen jagoranacin kansilolin. Kansila mai wakiltar mazabar Tungar Zazzagawa, Hon. Buhari Usman, ne ya bayyana haka jiya a garin Argungu bayan wani zama da suka yi. Ya bayyana cewa, daga cikin korafe-korafensu akwai shirya wani gangamin taro a gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar, Tafidan Kabi, da ke garin…
Read More
Yadda Kotun Ƙoli ta ji ba’asin shari’ar zaɓen gwamnan Kano

Yadda Kotun Ƙoli ta ji ba’asin shari’ar zaɓen gwamnan Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne Kotun Koli ta jingine ranar yanke hukunci kan qarar da Jam’iyyar NNPP ta shigar ta na neman ta tabbatar da dan nasarar dan takararta, Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan Jihar Kano. A watan Satumba ne dai kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Kano ta kori Yusuf a matsayin gwamnan jihar. Daga bisani, NNPP da dan takararta suka kalubalanci hukuncin a Kotun Daukaka Kara. A ranar 17 ga Nuwamba, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Kotun Kararrakin Zabe, sannan ta kara da cewa Yusuf ba dan Jam’iyyar NNPP ba…
Read More
An kashe wata mata saboda mafarki a Kano

An kashe wata mata saboda mafarki a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An gurfanar da wasu maza su biyar kan zarginsu da yin taron dangi wajen kashe wata mata saboda mafarkin da wata ta ba su labari a Jihar Kano. Kotun Jihar Kano mai lamba 14 da ke zamanta a titin Miller ta gurfanar da su ne kan zargin haɗa baki da kashe matar saboda zarginta da maita. Mai gabatar da ƙara, lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soronɗinki ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargin su biyar suka haɗu suka kashe wata mata mai suna Ɗahara Abubakar. Barista Lamido Abba Soronɗinki ya ce a garin…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan kasafin 2024

Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan kasafin 2024

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya sanya hannu a kasafin kuɗi na shekara 2024. Sai da majalisar dokoki ta jihar ta shafe kwanaki talatin da uku tana ta tafka muhawara akai tare da gayyato kwamishinoni da shugabannin ma'aikatu kafin su amince da zartas da kasafin kuɗin. Gwamnan da ya sanya hannu a kasafi kuɗin a gaban babban joji na jiha mai shari'a Musa Danladi da Alƙalin Alƙalai Dr kabir Abubakar. Sauran sun haɗa da 'yan majalisar dokoki na jiha da 'yan majalisar zartaswa ta jiha da kuma manyan jami'an gwamnatin jihar. Gwamna Dikko…
Read More
Yadda sunayen manoman bogi suka mamaye shirin bunƙasa noman alkama a Yobe

Yadda sunayen manoman bogi suka mamaye shirin bunƙasa noman alkama a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Gwamnatin Tarayya ta sha ɓullo da muhimman shirye-shirye da tsare-tsaren farfaɗo da harkokin noma, don inganta tattalin arziki, ayyukan yi tare da samar da isasshen abinci ga al'ummar ƙasa baki ɗaya. Wanda a zahiri, waɗannan muhimman shirye-shirye; idan an aiwatar da tsarin da yake a rubuce a takardun bayanai, hakan zai taimaka wajen kawo mafita ga wasu daga cikin wahalhalun da yan Nijeriya suke fuskanta na ƙarancin abinci da hauhawar farashinsa. Shirye-shiryen tallafa wa ayyukan da za su farfaɗo da aikin noma tare da manoma sun haɗa da amfani da ƙungiyoyin manoma na ƙasa, waɗanda…
Read More
Makamashi: Taron CO-28 ya zo da bazata

Makamashi: Taron CO-28 ya zo da bazata

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Babban labari a duk kafofin labarai na duniya a wannan makon shine duniya ta amince da ta daina amfani da duk wani makamashi da ke da haɗari wajan kawo ɗumamar yanayi, inda aka lissafa man fetur da gas da sauran dangogin su tare kwal. Amma abin mamaki ƙasashe sama da ɗari biyu (200) su suka sanya hannu bayan jefa ƙuri’ar amincewa. Taron ɗaya gudana a ƙasar haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a birnin Dubai ya zo da bazata domin kuwa an kwashe sama da shekaru 30 majalisar ɗinkin duniya tana fafutukar jawo hankalin duniya haɗarin da yake…
Read More
Ma’aikatar lafiya za ta soma ziyarar bazata a asibitocin Kebbi

Ma’aikatar lafiya za ta soma ziyarar bazata a asibitocin Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Ma'aikatar lafiya ta Jihar Kebbi ta sha alwashin ɗaukar matakin kai ziyarar bazata a manyan asibitocin da ke faɗin jihar. Kwamishinan Lafiya na jihar Honarabul Yunusa Musa Isma'il ne bayyana haka a wata ziyara da ya kai a asibitin garin Kamba a ƙaramar hukumar mulki ta Dandi. Kwamishinan ya ce yin haka zai zaburar da ma'aikatan wajen mayar da hankali ga ayyukansu musamman waɗanda ke wasa ko kuma rashin zuwa wajen aiki, bayan wannan kuma don su je su gane wa idonsu abubuwan da ke faruwa a asibitoci don ɗaukar matakin da ya dace.…
Read More
CAF ta amince da sunayen ‘yan wasa da Nijeriya ta gabatar na gasar AFCON

CAF ta amince da sunayen ‘yan wasa da Nijeriya ta gabatar na gasar AFCON

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafar Afrika (CAF) ta amince da sunayen tawagar ’yan wasan wucin gadi na Super Eagles ta Nijeriya da za su taka leda a gasar kofin Afrika ta 2023 kamar yadda kocin ƙungiyar, Jose Peseiro ya miƙa mata. CAF ta tabbatar da jerin sunayen kamar yadda aka bayyana a shafin yanar gizonta a ranar Laraba. Ana sa ran Peseiro ya gabatar da cikakkiyar tawagarsa ta ƙarshe ga hukumar ta CAF kafin wa'adin da aka ɗiba ya ƙare a ranar 3 ga watan Janairu. A cikin jerin sunayen akwai ’yan wasa uku da ke…
Read More
Gwamna Lawal ya ƙaddamar da aikin gyaran Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Zamfara

Gwamna Lawal ya ƙaddamar da aikin gyaran Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Zamfara

Daga BASHIRI ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da aikin gyaran College of Health Sciences and Technology da ke tsafe. Ƙaddamarwar wadda ta gudana a ranar Juma'a na mazaunin ɓangare ne na ƙudurin inganta fannin ilimin jihar da Gwamnan ke da shi. Aikin gyaran kwalejin ɓangare ne na shirin NG-CARES na Bankin Duniya wanda aka assasa don kyautata rayuwar 'yan karkara ta hanyar gyara musu abubuwan more rayuwa da ke yankunansu. Kakakin Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, aikin gyaran College of Health shi ne na farko a jerin…
Read More