25
Dec
Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tsarawa da kera motoci ta Nijeriya ta yi kira ga gwamnatin Tarayya a kan ta haramta shigo da tsofaffin motoci da aka yi amfani da su daga shekarar 2000 zuwa 2007 cikin Nijeriya. Jaridar Persecondnews ta rawaito cewa, bayanan da aka samu a binciken Hukumar kasuwancin Kasa da kasa a Amurka ta samar, ya bayyana cewa, bukatar ababen hawa/motoci a Nijeriya na kowacce shekara ta tasam ma guda 720,000 yayin da masana'antu na cikin gida suke iya samar da guda 14,000 kacal a kowacce shekara. Don haka ake shigo da ƙari wasu motocin don a…
