Ya kamata gwamnatin tarayya ta haramta shigowa da tsofaffin motoci Nijeriya – (NADDC)

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar tsarawa da kera motoci ta Nijeriya ta yi kira ga gwamnatin Tarayya a kan ta haramta shigo da tsofaffin motoci da aka yi amfani da su daga shekarar 2000 zuwa 2007 cikin Nijeriya.

Jaridar Persecondnews ta rawaito cewa, bayanan da aka samu a binciken Hukumar kasuwancin Kasa da kasa a Amurka ta samar, ya bayyana cewa, bukatar ababen hawa/motoci a Nijeriya na kowacce shekara ta tasam ma guda 720,000 yayin da masana’antu na cikin gida suke iya samar da guda 14,000 kacal a kowacce shekara. Don haka ake shigo da ƙari wasu motocin don a cike givi.

Darakta Janar na Hukumar tsarawa da kera motoci (NADDC), Mista Joseph Osanipin, ya ba da shawarar a haramta shigo da motocin da aka yi amfani da su daga shekarun 2000 zuwa 2007 cikin kasar nan.

A cewar sa, wannan shawarar za ta matukar taimaka wa kamfanonin kera motocin wajen gudanar da ayyukansu ba tare da tangarda ba. Sannan za ta kare kasar daga zama bolar tsofaffin motoci.

Osanipin, ya bayar da wannan shawarar ne a yayin kaddamar da tsarin NADDC na (NAIDP 2023 zuwa 2033) a Abuja.

Ya qara da cewa, NADDC za ta hada kai da wasu kamfanoni da hukumomin da suka dace don shimfida iyakar shekarun tsofaffin motocin da za a shigo da su kada su wuce shekaru 20.

Ya kara da cewa, dole su zauna tare da abokan aikinsu musamman wadanda suke a hukumar Kwastam don su fara sa takunkumin shekaru a kan motocin da aka yi amfani da su. “Kuma ba za mu kyale Nijeriya ta zama bolar tsofaffin motoci ba”, inji shi.

A cewar sa ba zai yiwu a dinga shigowa da motocin da aka yi amfani da su a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2007 zuwa Nijeriya ba. Don haka za a yi mai yiwuwa don ganin bayan matsalar. Sannan bayan haka za a fara duba daraja da lafiyar mota kafin a shigo da ita.