Kawar da ciwon hanta kafin 2030

A baya-bayan nan ne kasashen duniya suka gudanar da bikin ranar yaki da cutar ‘Hepatitis’ wanda ake kira da ciwon hanta a Hausance, domin kara wayar da kan jama’a game da wannan mummunar cuta da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta nau’in B da C a duniya. A yayin da ciwon hanta nau’in B kawai ke kashe rayuka 900,000 duk shekara.

Har ila yau, hukumar lafiyar ta ce, kaso 10 cikin 100 ne kawai na masu fama da cutar hanta nau’in B da kuma kaso 19 cikin 100 na masu fama da ciwon hanta nau’in C suka san suna dauke da cutar.

Wannan na nuni da miliyoyin mutane da ke fama da ciwon hantar amma basu sani ba, kuma hakan na faruwa ne saboda karancin zuwa asibiti domin gwajin ciwon hanta akai-akai.

Haka nan, kaso 42 cikin 100 ne kawai na yaran da ake haifa a fadin duniya suke iya samun allurar rigakafin ciwon hanta nau’in B bayan haihuwarsu. Saboda haka hukumar ke sake jaddada kira game da yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri cewa, ya kamata dukkan jarirai su sami rigakafin ciwon hanta nau’in B bayan haihuwarsu.

Sai dai kuma bincike ya nuna cewa Hepatitis A, Hepatitis B, da kuma Hepatitis C su ne suka fi wanzuwa tsakanin mutane.

Alamomin ciwon hanta sun hada da; Ciwon ciki, zafin jiki, amai, tashin zuciya, kasala, bakin fitsari, idanuwa su yi kalar dorawa da jiki, kaikayin jiki, bahaya kore.

Ga dan bayani akan cutar Hepatitis A,B,C,D,E a kasa:

Hepatitis A:

Ana kamuwa da kwayar cutar Hepatitis A ne ta hanyar gurvataccen abinci ko ruwan sha wanda ya gaurayu da kashin wani mai dauke da cutar, wanda kwari ke yadawa, sannan ya fi yaduwa ne a kasashen da tsaftar muhalli ke da karanci.

Hepatitis B:

Kwayar cutar hepatitis B cuta ce ke haddasa wannan rukuni na ciwon hanta, wanda ke yaduwa a cikin jinin mutumin da ya kamu da ita. Ana kamuwa da shi ne idan aka sanya wa mutum jinin mutumin da ke dauke da shi, yin amfani da allura ko reza, ko wasu karafa masu dauke da kwayar cutar. Haka zalika, ana dauka daga uwa zuwa danta, da kuma saduwa da wanda ke dauke da cutar.

Binciken lafiya ya nuna cewa cutar hanta wato Hepatitis B ta zamo cutar da ke kisa a boye.

Masana harkar lafiya sun ce cutar ta fi kisa fiye da cutar zazzabin cizon sauro a shekara. Binciken ya ce, kimanin mutane miliyan 257 ne ke fama da cutar samfurin ‘B’ a duniya, kuma Nijeriya na daga cikin kasashe biyar da ke da kashi 60% na masu fama da wannan cutar. An ware ranar 28 ga watan Yulin ko wace shekara a matsayin ranar ciwon hanta ta Hepatitis.

Hepatitis C:

Ana kamuwa da shi ne ta kwayar cutar Hepatitis C. Yana yaduwa ne ta hanyar sanya wa mutum jinin wanda ke dauke da ita.

Hepatitis D:

Ana kamuwa da shi ne ta kwayar cutar Hepatitis D. Yana shafar mutumin da ya riga ya kamu da cutar hepatitis B ne, domin yana bukatar kwayar cutar hepatitis B kafin ya iya tsira a jikin mutun. Yana yaduwa ta hanyar sanya wa mutum jinin mai dauke da ita da kuma saduwa da wanda ke dauke da cutar. Dadewar wannan cuta na iya sa mutum kamuwa da cutar dajin hanta.

Hepatitis E:

Ana kamuwa da shi ne ta kwayar cutar hepatitis E. Sannan akan kamu da shi ne ta hanyar cin danyen naman alade. Wannan baya dadewa a jikin mutum, sannan baya bukatar kowani magani, amma ya kan munana a cikin wasu mutane.

Wasu daga cikin matakan kariya sun hada da:

  • Tattaunawa da likita kan daukar alluran rigakafin ciwon hantar.
  • Kada a yi amfani da allura, reza ko burushin goge baki da wani ya ke amfani da su.
  • Ga masu juna biyu, tattauna da likita kan yadda za a kare yaduwar cutar zuwa jariri.
  • A yi amfani kadai da abubuwan yanka jiki (kamar askar aski ko askar tiyatar likita) da aka tsabtace su daga dukkan kwayoyin cuta.
  • A lizimci amfani da kwaroron roba (condom) ko da yaushe yayin saduwa da wanda ke dauke da cutar ko hadarin kamuwa da cutar.
  • Idan zai yiwu, a zaci shan kwayar magani maimakon yin allura.

A cewar Darektan Hukumar ta WHO a Nahiyar Afirka, Dakta Matshidiso Moeti, a wani sako na bikin ranar yaki da cutar Hepatitis ta duniya ta 2022, ya sanar da cewa, cutar hanta ita ce ke da alhakin mutuwar mutane kusan 125,000 a Afirka duk shekara, duk da samun magani. Ya yi kira ga dukkan gwamnatocin Afirka da su himmatu wajen karkatar da kulawa zuwa matakin kiwon lafiya na farko, ta yadda za a samu saukin jinya ga kowa, ba tare da la’akari da inda ya ke zaune ba.

Ya kuma bukace su da su sanya fifiko kan kudade don magance wannan barazanar lafiya da za a iya maganceta. Ya bukaci kasashen Afirka da su samar da hanyoyin da za su iya bi, tsarin kiwon lafiya don tantance gudummawar jini ga cutar hanta, da tabbatar da cewa an yi amfani da sirinji sau daya kawai kuma a zubar da shi a shara, domin wadannan su ne manyan abubuwan da ke taimakawa wajen yaduwar cutar hanta. Ya bukaci al’ummar Afirka da su je a yi gwajin cutar da kuma kula da su.

An bayyana Nijeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da ke da yawan masu dauke da kwayar cutar a cikin kasashe 47 na Afirka. Rahotanni daga kafafen yada labarai sun bayyana cewa, kimanin kashi 12 cikin 100 na al’ummar Nijeriya miliyan 200 da aka kiyasta suna fama da cutar hanta na kullum wato Hepatitis B, yayin da kashi biyu cikin 100 na fama da cutar hanta ta C.

Kuma yayin da bincike ya nuna cewa Nijeriya tana da tsarin kula da cutar hanta ta kasa da kuma wani shiri mai muhimmanci na cutar hanta, an ce yawan allurar rigakafin cutar hepatitis B ya kai sama da rabi, kashi 58 cikin 100 a kasar, inda har yanzu mutane da dama ba su san cutar ba saboda rashin kulawa da dalilai daban-daban kamar rashin bayar da rahoto.

Don haka wannan jarida ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara wayar da kan jama’a game da cutar, tare da karfafa gwiwar jama’a da su je a yi gwaje-gwaje, idan kuma ana so a yi musu magani. Ya kamata gwamnatin tarayya ta kuma samar da kayan aiki tare da raba hanyoyin tantance cutar hanta da kuma kula da cutar hanta daga asibitocin tsakiya zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta yadda zai iya isa ga kowa.