Abubuwa 3 masu dakatar da nasarar mai sana’a – Likitan Sana’a

Daga AMINA YUSUF ALI

Ga wasu shawarwari da Badamasi Aliyu Abdullahi ya bayar ga masu sana’a don samun cigaba. Kamar yadda muka sani, kowacce cuta da maganinta. Don haka wasu abubuwa uku da Likitan sana’a ya rawaito cewa idan an guje su za a samu nasara a sana’ar da ake yi.

Na farko, jiran tallafin gwamnati wanda ba ka san ranar zuwan sa ba: Masu sana’a da yawa suna tafka wannan kuskuren. Wasu kafin fara sana’arsu. Wasu bayan sun fara. Ga duk mai sana’a, babban strategy ɗin da za ka dauka da zai taimake ka shi ne, kar ka tsara cigaban sana’arka a kan tsammanin tallafin gwamnati.

Wannan shi ke cutar mutane da dama. Abin da za ka yi shi ne, duk lokacin da gwamnati ta yi alƙawarin taimakawa masu kanana da matsakaitan sana’o’i, ka nema. Ba a kin nema. Abinda ba ka nema ba, ba za ka taba samu ba. Inda gizo ya ke sakar shi ne, in ka nema, ka dauka cewa in ta yi ruwa, rijiya. In ba ta yi ba, masai. Kar ka taba dora cigaban sana’arka a kan tallafin gwamnati. In ka yi haka ka gama yawo.

Na biyu, yawan korafi a kan lalacewar al’amuran kasuwanci: Kowa ya san cewa akwai matsala a kan harkokin kasuwanci a Nijeriya. Haka ma duniya. Amma ga mai sana’a da ke da tsari da manufa, ba ya tsayawa vata wa kansa lokaci wajen yawaita korafi a kan matsaloli. Bincike ya nuna kaso 80% na tunanin ka mara kyau ne.

Hakan na janyo ma damuwa, firgici da munana zato ga al’amuran rayuwa da na kasuwanci. Wannan ya sa hatta yawan korafi na neman ya fi yawan addu’a da mu ke yi wanda hakan kuskure ne. Idan kana sana’a, ka sani cewa korafi ba magani ba ne.
Na uku, yawan ba da uzuri a kan dalilan da suka sa ba ka yi nasara ba. Masu burin fara sana’a da yawa sun fi tallata uzurin da ya hana su fara kasuwanci a kan haja.

Da yawa su ma daga cikin wadanda suke kasuwanci kuma sun fi sana’anta uzurorin da su ka hana su cigaba fiye da hajar da za ta kai su inda su ke so su je a tafiya ta kasuwanci. Yawan ba da uzuri na nuna sarewa da kuma gazawa wajen shawo kan matsalolinka. Kasuwanci ya gaji kalubale.

Hakazalika, ma’anar kasuwanci gabadaya ita ce warware matsala, da ta ka da ta jama’a. Idan har ba korafin zama kudi ba ne, to ya kamata dan kasuwa ya yi amfani da lokacin ba da uzuri wajen yin tunanin shawo kan kalubalen da yake fuskanta.