Tinubu ga ‘yan Nijeriya, ku saurari samun walwala nan ba da daɗewa ba

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbaci kan su sa ran samun walwala nan ba da dadewa ba.

Tabbacin Shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwar da suke fuskanta wadda cire tallafin mai ya haifar.

Tinubu ya ba da tabbacin haka ne a sakon Kirsimetin da ya aike wa ‘yan kasa, musamman mabiya addinin Kirista, albarkacin bikin Kirsimetin da al’ummar Kirista ke gudanarwa a wannan Litinin a duk fadin duniya.

Shuagaban ya ce gwamnatinsa ta bada himma ainun wajen aiwatar da ingantattun matakan da za su taimaka wajen rage wa ‘yan kasa radadin rayuwar da suke fuskanta.