Ku yi koyi da karantarwar Yesu, kiran Gwamna Sule ga al’ummar Kirista

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiya Abdullahi Sule, ya yi kira ga al’ummar Kirista na Jihar Nasarawa da kewaye da su yi koyi da karantarwar Yesu Kristi, yayin bukukuwan Kirsimeti na wannan shekara.

Bayanin haka na kunshe ne cikin sakon Kirsimetin da Gwamna Abdullahi Sule ya mika wa al’ummar jihar a birnin Lafia ta bakin hadiminsa kan sha’anin yada labarai da hulda da jama’a, Dr. Nawani Aboki.

Gwamna sule ya ce haihuwar Yesu Krist alama ce mai nuni da a so juna, yafiya, taimakeniya, hakuri da kyautata wa juna da sauransu.

Daga nan, ya bukaci al’ummar Kirista da su dabbaka kyawawan dabi’un Yesu ta hanyar wanzar da kauna a cikin al’umma, girmama shugabanni tare da yi musu addu’a domin samun damar maganace matsalolin da ake fuskanta a wannan lokaci.

Kazalika, ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar Nasarawa da a zauna lafiya da juna kana a guji aikata duk wani abin da zai tada zaune tsaye a cikin al’umma.

By Editor