‘Yan bindiga sun kashe gomman mutane a Filato

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga jihar Filato sun ce, akalla mutum 145 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da ‘yan bashin daji suka kai a kan kauyuka 23 a sassan jihar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan bindigar sun kashe mutum 113 a kauyuka 20 a yankin Karamar Hukumar Bokkos, sannan mutum 32 a wasu kauyuka uku da ke yankin Karamar Hukumar Barkin Ladi a jihar.

Bayanai sun ce an kai hare-haren ne cikin daren Asabar zuwa safiyar Litinin da ta gabata, inda aka kashe gomman jama’a tare da jikkata wasu da dama da kuma lalata dimbin dukiya.

Ya zuwa hada wannan labari, kokarin da aka yi don jin ta bakin hukumar ‘yan sandan yankin, ya ci tura.

Shugaban kwamitin riko na Karamar Hukumar Bokkos, Monday Kassah, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

By Editor