An yi janazar mutane takwas da ‘yan bindiga suka hallaka a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wata dabar ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai sun bude wa ‘yan kasuwa takwas wuta, kusa da kauyen babangida bayan da suka dawo cin kasuwar Jibiya dake karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.

‘yan ta’addar sun kuma jikkata wasu karin mutane hudu a yayin da wasu biyu suka bata tun bayan harin da aka kai jiya Lahadi da dare.

Wadanda aka kashe din mazauna kauyen ‘Yan gayya ne a karamar hukumar ta Jibiya dake makota da Zurmi ta jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewar luguden wutar da sojin sama na Nijeriya ke yi wa ‘yan ta’addar ne ya tilasta masu barin dajin Zurmi dake jihar Zamfara.

Tuni aka yi janazar wadanda suka rasa rayukansu a yayin da wadannan suka jikkata ke ci gaba da karvar magani a asibiti.