Kasafin 2024: Gwamna Lawal ya ware N1.3b don zamanatar da kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnati

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ware Naira biliyan 1.3 a kasafinta na 2024 don zamananta kafafen yada labarai mallakar jihar.

Kwamishinan Yada Labarai da Raya Al’adu na Jihar, Mannir Haidara, shi ne ya bayyana haka ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar, jim kadan bayan gabatar da kasafin ma’aikatarsa ga Kwamitin Kudi na Majalisar Dokokin jihar.

Kwamishinan ya jaddada cewa zamanantar da kafofin yada labarai mallakar jihar ya yi daidai da kudurin Gwamna Lawal na farfado da masana’antar yada labarai ta jihar.

Ya kara da cewa, Kamar yadda aka sani, ma’aikatar ke da alhakin yada labarai a fadin jihar. Mun kaddamar da ayyuka da dama domin bunkasa wannan masana’antar daidai da muradin gwamnatin Gwamna Lawal.”

Haka nan, ya ce zamanantar da masana’antar zai amfani sauran hukumomi da suka hada da Hukumar Tace Finafinai ta Zamfara da sauransu.

A ranar Alhamis da ta gabata Gwamna Dauda Lawal ya gabatar da kasafin 2024 na Naira biliyan 423.5 ga Majalisar Jihar.