Ƙungiyar Gwamnoni ta maka tsohon Daraktanta a kotu kan zarginta da almundahana

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta musanta zargin karkatar da kudade da tsohon Daraktanta na Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Abdulrazaque Bello Barkindo, ya yi.

News Point Nigeria ta rawaito cewa, cikin wata wasikar sirri da ya aike wa Gwamna AbdulRasaq, Barkindo ya fallasa cewa a halin da ake ciki NGF ta fi bai wa hada-hadar kudi muhimmanci fiye da ayyukan cigaba.

Barkindo ya jaddada cewa, kungiyar ta zama wata kafa inda wasu tsiraru ke amfana da ita, don haka ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan yadda NGF ke tafiyar da kudadenta.

Sai dai, a wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun sashen kula da shari’a, kungiyar ta bayyana zargin mara tushe balle makama da kuma bata mata suna.

Kungiyar ta ce ta mika batun ga lauyoyinta don neman shawara kan batun da kuma bukatar wayar da kan al’umma kan badakalar Abdulrazaque Bello Barkindo, wanda ya ajiye aiki a kungiyar ran 7 ga Disamban 2023.

“Muna tabbatar wa jama’a da sauran abokan huldarmu cewa babu wata matsala da NGF ke fuskanta,” in ji Kungiyar

NGF ta ce tuni ‘yan sanda sun fara bincike kan bayanan zargin da aka yada wanda aka danganta da Barkindo, sannan an shigar da kara kan haka.

Ta kara da cewa, za su bai wa ‘yan sanda cikakken hadin kai game da binciken da suke gudanarwa, sannan za a tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan badakala.