Babu wanda rashin sa a Kalankuwar KILAF zai sa ta kassara – Abdulkareem Muhammad

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Bayan kammala taron kalankuwa tare da bajekolin finafinan Afirka na wannan shekara KILAF AWARD 2023, da aka gudanar daga 21 zuwa 26 na watan Nuwamba da ya gabata, wakilin mu ya ya yi tattaunawar musamman da Malam Abdulkareem Muhammad wanda shi ne shugaban shirya Kalankuwar Afirka da ake yi duk shekara a Kano wanda ake yi wa laqabi da ‘Kano Indigenous Languages Of Africa Film Market and Festival’ KILAF Award wadda kamar kowacce shekara a bana an shirya bikin kuma an yi an kammala lafiya. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Kamar yadda aka saba a wannan shekarar ma an yi taro kuma an kammala taron KILAF 2023. Ko ya ya taron wannan shekarar ya kasance?

MALAM ABDULKAREEM: Wato shi wannan taron kalankuwa da muke shiryawa a kowacce shekara kuma wanda muka yi karo na shida kenan aka kammala a ranar asabar 26 ga Nuwamba da biki da aka yi na bada kyaututtuka na gasa da aka yi na finafinan harsunan Afirka, mun yi shi ne na tsawon kwanaki biyar wanda ranar farko 21 ga Nuwamba muka buɗe taro da Kai wa Fadar Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ziyara tare kuma da shrya liyafar cin abinci ta maraba da baƙi da muka yi da daddare a Brritol Hotel.

To bisa gayyata da muka miqa wa gwamnan Jihar Kano ya kasance ya shugabancin wannan taron. Amma saboda an san yanayin da shi gwamna yake ciki kan taƙaddamar kotu, hakan ya sa bai samu damar halarta ba. Kuma mun gayyaci manyan mutane da suke Kano na cewa su halarci wannan liyafa ta cin abincin maraba da baqin namu kuma mun samu halartar mutane aƙalla 140 da suka halarta.

A rana ta biyu kuma muka buɗe bita da muke yi a kowacce shekara, wanda a wannan shekara mun yi wa bitar laƙabi da ‘Ya za a yi a warware katutu na mulkin mallaka da yake zukatan ‘yan Afirka’ kuma an gabatar da muƙaloli wajen guda 14 daga mutanen da suka fito daga ƙasashe wajen biyar. Kuma mun yi wannan bita ne da haɗin gwiwa da tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero, kuma a harabar wannan makaranta ne muka gudanar da taron wadda muka yi na kwana biyu.

Sannan a cikin waɗannan kwanakin sai aka fara wata horaswa da aka yi a kan yadda ake ilmintar da jarumai na yadda za su inganta harkar wasan kwaikwayon su. To nan mun gayyato masana da suka haɗa da Sani Mu’azu Galadiman Jos da sauran masu ilimi a harkar. Kuma mun samu halartar mutane daga wurare daban daban har daga gudan talbijin na ƙasa, wato NTA suka shiga wannan horaswa.

A lokacin da ake wannan horaswa kuma an yi bajekoli na kayayyakin al’adu na gargajiya namu, sannan an bajekolin abincin mu na gargajiya inda duk wani wanda ya zo taron ya yi rajista ake ba shi abincin domin ya ɗanɗana irin abincin da muke da shi a nan. Sannan kuma ban da abincin hatta su zobo da duk wata harka ta sha ko ci mun tabbatar da abincin mu ne na gargajiya muka bayar don haka muka samar da su zogale, rama, lansir, dambu duk irin waɗannan abubuwa saboda mu nuna musu cewa muna da abincin mu na gargajiya.

To bayan wannan kwanaki uku da aka yi ana waɗannan shirye-shirye na koyarwa, da bajekolin kayan gargajiya. An shirya wasan garaya da hawan bori wanda aka yi ranar Alhamis a Gidan Danhausa wanda shi ma wani ɓangare ne na al’adun Hausa da yake neman ya vace aka shirya domin nuna wa baƙin mu al’ada.

Sannan kuma ranar Juma’a aka shirya taron cin abinci da bayyana finafinan da suka fito a matakin shiga gasar wanda aka yi da daddare a otal ɗin Tahir, kuma manyan mutane da dama sun halarta.

Sai kuma ranar Asabar da rana aka ɗauke baƙin mu aka zagaya da su wuraren tarihi da yawon shaƙatawa da suke cikin birnin Kano. In da kuma bayan an gama aka tafi gidan shugaban ƙungiyar ACF reshen Jihar Kano Dakta Gwani Umar Faruk wanda ya haxa mana liyafar cin abincin rana a gidansa wanda shi ma na gargajiya ne aka ci.

Sai kuma bayan nan da daddare aka shiga wajen taro na otal ɗin Broslal in da aka gudanar da bikin bada kyautuka ga waɗanda suka ci gasa daban-daban. Sannan muka naɗa Dakta Gwani Umar Faruk ya kasance shi ne Garkuwan wannan KILAF 2023.

To waɗannan su ne abubuwan da muka gudanar a taron mu na wannan shekarar.

Taron da aka yi na ƙarshe na karrama waɗanda suka ci gasar shi ne mafi girma saboda shi ne wanda ya ɗauki mutane da yawa da suka zo daga wurare da dama. Ko ya ya ka kalli wannan taro?

To wannan ya yi armashi sosai, saboda mun samu shigowar finafinai wajen 56 daga ƙasashe 21 na duniya, sannan kuma mun bayar da lamba ta yabo ga finafinai ta fannoni 16 na harkar shirya fim. Sannan kuma mun ware guda uku da muka bai wa fitattu na wannan nahiya tamu ta Afirka da suka bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban musamman ma a harkar.

Wannan taron da aka yi shi ne karo na shida da aka yi ana yi. Idan ka duba tsawon sheakaru shida da aka yi ko waɗanne irin nasarori aka samu?

Nasara ta farko dai ita ce da ya zama wannan taron ya fara karvuwa har ya zama na Nahiyar Afirka, tun da har ta kai ƙasashe 21 sun shiga wannan taron. To ka ga nasara ta farko kenen. Sannan kuma shigo da finafinan, abin da nake gani ya ƙara wa mutane ƙarfin gwiwar inganta aikin su ta yadda za su shigo da finafinai masu kyau gasar ta yadda sai ka na ganin abin da ka yi mai kyau ne sannan za ka shiga wannan gasar.

Saboda haka mun saka wa masu wannan harka ɗan ba na cewar su rinƙa yin abu mai inganci saboda su shigo gasar don su samu nasara. Sannan kawo mutane, don ina ganin bita da muka yi a Jami’ar Bayero, ina ganin babu wani taro da ake yi na harkar fim da yake kawo masu harkar fim da kuma waɗanda suke koyar da harkar fim na jami’o’in mu waje guda a ce sun samu fahimtar juna.

Saboda mun samu halartar farsoshoshi da kuma daktoci da suke koyar da harkar kuma sun zo sun koyar da muƙaloli. Kuma a cikin waɗanda suka koyar muke fitar da wasu takardu mu buga su mu wallafa su zuwa littafi. Wannan ba ƙaramin abu ba ne, saboda zai inganta harka don mu ɗin nan Nahiyar Afirka akwai Malaman da suke koya mana na da suka yi jawabi kuma za mu karanta mu samu biyan buƙatar da muke nema, maimakon mu yi ta kawo littattafai daga ƙasashen Turai wanda suke nuna mana abubuwan da su suke yi, sai ya zama a yanzu mu muke wallafa littattafan da suke koya mana yadda ake yin harkar nan da duk wani abu da muke buƙata, don haka wannan ba ƙaramin abu ba ne a cikin nasarar da muka samu.

Sannan shigowar kamar ‘Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation’ da take Kaduna, sun shigo wannan lamari suna ganin cewa tun da harkar fim matasa ne suke yin ta. Kuma su suna da sha’awar inda za su inganta rayuwa ta matasa, sai suka ga ta ya yaya za su shigo a yi wannan tafiya da su. Kuma mun nuna musu cewa ya kamata a ce duk wani horo da za a yi a cikin wannan dandamali a ce sun shiga ciki sun bai wa matasan mu gurbin yadda za su ce sun ɗauki ɗawainiyar su su zo su koyi wani abu.

Ita ma haka ƙungiyar Tuntuba ta Arewa sun buɗe mana ƙofa kuma sun nuna mana sha’awar su na cewa in dai har za a sake yi nan gaba za su iya duba in da za su kawo mutane waɗanda suke ‘yan Arewa su ba su dama a koyar da su a irin wannan dandamali da muke samarwa a cikin wannan tafiya ta KILAF. To ka ga waɗannan abubuwa ne manya.

Sannan alal misali kamfanoni na Bankin Manoma sun shigo wannan harkar mun nuna musu cewa muna son mu yaɗa harkokin cin abinci kamar irin cin abincin da muke yi wanda shi ne suka ba mu gudunmawa. Ka ga wannan ba ƙaramin abu ba ne ba. Sannan akwai wani kamfani su ma da suke harkar noma da suka shigo wannan waje suka bayar da abinci kyauta, ka ga wannan ma ci gaba ne saboda zai inganta harkar su sannan kuma zai bai wa mutane damar su ɗanɗana kayan su. Ka ga sun samu kasuwa.

Akwai kuma bankin masana’antu da suka nuna sha’awa sun zo sun duba yadda muke abin kuma sun gamsu da cewa abin da muka yi yana da fa’ida, suna da zummar su ma su shigo su ga yadda za su tallafa wa harkar. To ina ganin waɗannan gudunmawa idan aka same su daga waɗannan vangarorin zai ma inganta abin fiye da yadda ma muke yi.

Duk shekara daga lokacin da aka gama taron ake fara shirin na gaba. Ko wannan ma haka ne?

Gaskiya wannan haka abin yake ko a yanzu ma haka ne, saboda in ka lura da abubuwan da muka tsara babu yadda za a ce ba a shirya masa ba a samu a yi wannan taron. Domin abubuwan da muka yi ba ƙaramin abu ba ne ba. Don gabatar da abu tsawon kwana biyar ana wannan ana wancan idan har ba a shirya masa ba ai babu yadda za a yi ya yiwu. Saboda haka a yanzu mun saka dan ba na yin taro na gaba na KILAF2024 in sha Allahu.

Kuma ina son mutane su gane musamman waɗanda muke yin harkar fim a nan Ƙasar Hausa, kamar har yanzu ba su farga da cewa KILAF ko mutum ya so ko bai so ba, KILAF wallahi wakiltar sa take yi. Saboda idan harshen Hausa ya zama shi ne yake karɓar baƙuncin harsuna na Afirka a ce ka na cin abinci a harkar fim, amma a ce an yi babu kai, wallahi to kash ɗin ka, don rashin sanin ciwon kai ne.

Saboda haka ina kira ga waɗanda suke yin wannan harkar ta fim idan mutum yana ganin cewar wannan KILAF kassara tafiiyar ta zai yi don bai shigo ta ba, wallahi ƙarya yake yi. Don ta fi ƙarfin mutum. Abin da za mu yi dole mu yi la’akari da cewa wannan abu namu ne ko mun ƙi ko mun so, saboda zummar cewa harshen Hausa zai shugabanci harsunan Afirka a yi wannan Kalankuwa. To idan babu Bahaushe a ciki wannan shi ya so.

To madalla mun gode.

To ni ma na gode sosai.