29
Nov
Daga IBRAHIM GARBA NAYAYA Nguru gururun duniya! Wannan yana daga cikin kirarin da muka taso muka ji ana yi wa wannan gari namu ma’abocin ɗaukaka da daraja! Gari, wanda ya samar da manyan mutane, shin malamai ne ko ‘yan kasuwa ne, ko wasu manyan ma’aikatan gwamnati! Gari, wanda ya yi shuhura da zaman lafiya da son addini da son masu addini! Gari, wanda mazaunansa suka taso suke ganin kowa ɗan’uwan juna ne! Gari, wanda a baya za ka iske mazaunansa na bibiyar matsalolin juna domin su magance musu ba don su yayata ba! Gari, wanda mutum guda zai ɗauki nauyin…
