Editor

9513 Posts
Cece-kuce ba zai canja hukunce-hukuncenmu ba – Alƙalai

Cece-kuce ba zai canja hukunce-hukuncenmu ba – Alƙalai

Daga BASHIR ISAH Babban Alƙalin Najeriya (CJN), Mai Shari'a Olukayode Ariwoola, ya jaddada cewa cece-kucen da ake yi a ƙasa ba zai canja hukunce-hukuncensu kan shari'un siyasa ba. Kawo yanzu, hukunce-hukuncen da Kotun Ƙoli ta yanke kan batutuwan zaɓe, wanda hakan ya yi sanadiyar soke nasarar wasu gwamnoni da 'yan majalisu, ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin 'yan ƙasa musamman 'yan siyasa. Da yake jawabi a wajen buɗe zama na musamman na fannin shari'a na 2023/2024 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyin Nijeriya su 58, Ariwoola ya buƙaci alƙalai da su yi tsayin daka game da ayyukansu. Ya…
Read More
Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin baiwa da ya siya (3)

Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin baiwa da ya siya (3)

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Anti Aysha Asas ina yini, ya lamura? Don Allah kar ki ambaci sunana, ko garin da nake. Wallahi na matsu ne, shi ya sa zan fallasa wannan sirrin don Ina son na samu mafita, saboda yanzu kaina ya yi zafi kan lamarin, ban san inda zan fuskata ba. Ina da shekara sha uku, uwata da kawuna da mai unguwarmu da wanda uwata take zaune gida nai, tana taya matansa aiki, suka shirya da ni, muka taho cikin garin………….da kayana da komai nau. Muka taho gidan wani babban mutum da yake da…
Read More
2024: Babu abin da zai dakatar da ni daga takarar Gwamnan Edo – Shaibu

2024: Babu abin da zai dakatar da ni daga takarar Gwamnan Edo – Shaibu

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Gwnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya bayyana aniyarsa ta neman shiga takarar gwamnan jihar ya zuwa 2024. Ya ce zai tsaya takarar ne a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, tare da cewa, babu abin da zai hana shi neman kujerar gwamnan jihar. Shaibu ya bayyana aniyyar tasa ce da safiyar ranar Litinin a cibiyar Biohop Kelly Centre da ke Benin City, babban jihar. Da yake yi wa dandazon masoyansa jawabi, Shaibu ya ce a matsayinsa na ɗan asalin jihar wanda kuma ya san ciwon al'ummar jihar, zai nemi shugabancin jihar ne don cigabanta da ma al'ummarta baki ɗaya.…
Read More
Shari’ar kotunan Nijeriya ta zama tufka da warwara – PDP

Shari’ar kotunan Nijeriya ta zama tufka da warwara – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Nijeriya, ta bayyana hukunce-hukuncen da kotunan ɗaukaka qara suka yi, inda suka ƙwace nasarar wasu gwamnoni a matsayin "karan-tsaye" ga dimokraɗiyya. Jam'iyyar adawar na zargin APC mai mulkin Nijeriya ne da "amfani da qarfin iko" wajen tanqwara hukuncin kotunan, zargin da APC ta musanta. "Shari'ar Nijeriya ta zama kamar rawar 'yan mata yanzu; idan an yi gaba, sai a koma baya," inji Mataimakin Sakataren PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi. Ya ce dalilan da mutanen nan ke gabatarwa suna kwace zaɓen nan, akasari batutuwan da suka shafi kafin zaɓe…
Read More
Muna maraba da kafa jam’iyyar haɗaka kamar yadda Atiku ya nema – NNPP

Muna maraba da kafa jam’iyyar haɗaka kamar yadda Atiku ya nema – NNPP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar adawa ta NNPP a Nijeriya ta nuna aniyarta ta shiga jam'iyyar haɗaka da sauran jam'iyyun adawa kamar yadda Atiku Abubakar ya nema a makon da ya gabata. Ɗan takarar na jam'iyyar PDP a zaven shugaban Nijeriya na 2023, Atiku ya zargi APC da yunƙurin mayar da Nijeriya bin tsarin jam'iyya ɗaya sannan ya yi kira ga jam'iyyun adawa da su dunqule don yin waje da jam'iyyar mai mulki. Shugaban Riƙo na NNPP na Ƙasa, Abba Kawu Ali, ya faɗa a yau Talata yayin wani taron manema labarai cewa kiran na Atiku abin a…
Read More
Mutanen Gaza ba su gaza ba bayan kashe dubbai

Mutanen Gaza ba su gaza ba bayan kashe dubbai

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Fiye da mako 6 kenan sojojin Isra'ila su na ruwan wuta kan Gaza inda Falasɗinawa fiye da miliyan 2 da ke zaune a garin musamman arewacin sa ke zama cikin yiwuwar afkuwar komai a kullum. In za a tuna Isra'ila ta buƙaci Falasɗinawan su kaura zuiwa kudancin Gaza don kare ran su daga boma-bomai. Duk da dai ba lalle ba ne can kuɗin ma tudun mun tsira ne amma ya fi yankin arewaci 'yar sararawar hare-hare, hakan bai sa dubban Falasɗinawa kauracewa gidajen su ba. Wannan akwai abun dubawa a nan don ga gidajen an…
Read More
Zuwa ga al’ummar Arewa

Zuwa ga al’ummar Arewa

Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri gare ku duka, ina kuma mai jajanta muka akan halin da muka tsincin kanmu a yau. Ina fatan wannan wasiƙar tawa ta same ku lafiya, cikin ƙoshin lafiya da walwala. Na rubutu wannan wasiƙar ne domin na isar muku da saƙona tare da fatana gare ku. Ina mai shaida muku cewa, ƙaunarku ce ta sa na rubutu wannan wasiƙar, domin masu iya magana kan ce 'Idan kunne ya ji…' Wannan wasiqar ita ce babbar gudunmawar da zan iya bayarwa a halin yanzu, bayan koyar da yara da nake a…
Read More
Alƙali ya gargaɗi jama’a da su daina jibge masa layu da kayan tsubbace-tsubbace a kotu

Alƙali ya gargaɗi jama’a da su daina jibge masa layu da kayan tsubbace-tsubbace a kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Shari’a Hakeem Oshodi na Babbar Kotun Ikeja, Legas ya gargaɗi jama’a cewa su daina lavavawa su na jibge masu layu, kambu, karhuna da gurayen tsibbace-tsibbace a cikin kotu. Oshodi ya bada wannan gargaɗin a ranar Litinin, yayin shari’ar wasu mutum biyar da ake tuhuma da kisan wani mai suna Ifeanyi Etunmuse. A ranar Litinin ɗin ce dai aka fara shari’ar, inda kuma a ranar ya yi wannan gargaɗin. “Kada wanda ya ƙara jibge min layu da karhunan tsibbace-tsibbace a kotu. Kada a kuskura a ƙara yi min haka. Domin an samu layu a…
Read More
APC zaɓe ko ƙwace?

APC zaɓe ko ƙwace?

Ga dukkan alamu jam'iyya mai mulki APC tana daf da kwace duk kujerun gwamnonin arewa. Jihar Kano ce ta farko wajen yiwuwar ta zamo ta APC amma idan Kotun Ƙoli ta tabbatar da hakan. Sai jihar zamfara wacce ga alamu sai an sake zaɓe a wasu yankuna a tsakani gwamnan PDP mai karagar mulki da kuma tsohon gwamna na APC wanda minista ne a yanzu. Jihar Filato ma a cen kotu ta kwace kujera ta gwamnan PDP ta mayar ga gwamnan APC wanda su kai takara. Amma mu kula da kyau? Dukkanin inda a ke ƙwace kujeru na gwamnoni ko…
Read More
Batun sake duba dawo da martabar noma a Nijeriya

Batun sake duba dawo da martabar noma a Nijeriya

Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa, akwai gayar muhimmanci ga gwamnati ta sake duba batun bunqasa harkokin noma a ƙasar nan, duba da rawar da ɓangaren ke takawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasa da samar da wadataccen abinci. Ayyukan noma su ne ginshiƙi kuma babbar hanyar da za ta iya jure kowace irin kwaramniya ga ci gaban ƙasa tare da al’ummarta baki ɗaya. Noma babbar abu ce a Nijeriya, ana ma kallon cewa ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwuwa ba. Haka zalika, kamar…
Read More