26
Nov
Daga MAHDI. MUHAMMAD Ƙungiyoyi 20 sun samu gurbin shiga gasar Euro 22024 kai tsaye, inda Jamus za ta karɓi baƙuncin wasannin a 2024. Ingila, wadda Gareth Southgate ke jan ragama tana cikin tawagogin da za su jira raba jadawali, bayan da ta ja ragamar rukuni na uku, itama Scotland ta samu gurbi. Dukkan wadda ta yi ta daya da ta biyu a kowanne rukuni, su ne suka samu tikiti kai tsaye a wasannin da za a fara daga Yuni zuwa Yulin 2024. Yanzu kenan saura gurbi uku ya rage, inda tawaga 12 za ta buga wasannin cike gurbin shiga Euro…
