Editor

9513 Posts
Tafiye-tafiye: Ban kashe miliyan N400 ba – Gwamna Dauda

Tafiye-tafiye: Ban kashe miliyan N400 ba – Gwamna Dauda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaryata labarin ƙarya da ake yaɗawa na cewa, ya kashe sama da Naira miliyan 400 a balaguro zuwa ƙasashen waje. Rahotanni sun nuna cewa, wata jarida ta yanar gizo ta yi kuskuren ruwaito Gwamna Dauda ya kashe Naira 170,276,294.31 wajen tafiye-tafiye na ƙasa da ƙasa, N221,567,094 kan tafiye-tafiyen cikin gida, N6,929,500.00 kan harkokin tsaro na sirri cikin watanni uku. Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce wasu vata gari ne suka ƙirƙiri labarin da gangan…
Read More
Duk minti ɗaya ana haifar yara 33 cikin yunwa a 2023 – SCI

Duk minti ɗaya ana haifar yara 33 cikin yunwa a 2023 – SCI

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kimanin yara miliyan 17.6 ne aka haifa cikin yunwa a shekara ta 2023, ko kuma kimanin yara 33 a cikin minti ɗaya, wato kashi 22 cikin 100. Binciken ya yi hasashen cewa Afirka da Asiya za su kai kashi 95 cikin 100 na jariran da ba su da isasshen abinci a shekarar 2023. Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin ƙasashen duniya da su faɗaɗa shirye-shirye masu rahusa don yin rigakafi da kuma magance matsalar rashin abinci mai gina jiki. Kimanin yara miliyan 17.6 ne aka haifa cikin yunwa a shekara ta 2023, ko kuma kimanin yara…
Read More
Tinubu ya nemi Jamus ta saka hannun jari a fannin makamashi da layin dogo

Tinubu ya nemi Jamus ta saka hannun jari a fannin makamashi da layin dogo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ƙasar Jamus da ta saka hannun jari a fannonin tattalin arzikin Nijeriya masu muhimmanci kamar wutar lantarki da sufurin jiragen ƙasa. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale, ya fitar, ta ce Mista Tinubu ya yi wannan kiran ne a wani taro da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, a taron G20 Compact with Africa Economic Conference, ranar Litinin a Berlin. Shugaban ya ce ana buƙatar zuba jarin Jamus a cikin muhimman masana'antu masu samar da ci gaba a fannin makamashi, sufuri, da samar…
Read More
Kamfanin Boska ya raba wa masu babura hular kwano 698 a Gombe

Kamfanin Boska ya raba wa masu babura hular kwano 698 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Don ganin an rage yawan mutuwa a sanadiyar hatsari, Kamfanin Dexa da suke yi maganin nan na Boska ya raba wa mahaya babura sama da 600 hular kwano kyauta a Gombe. Kamfanin na Boska ya yi haɗin gwiwa ne da hukumar kiyaye hatsura ta ƙasa FRSC reshen Jihar Gombe don ganin cewa suna da ruwa da tsaki wajen faɗakar da masu baburan muhimmancin sanya hular kwano ga duk mai hawa babur. Da ya ke jawabi a lokacin raba hular kwanon Kwamishinan Ma’aikatar tsaron cikin gida na jihar Gombe Laftanal Abdullahi Bello mai ritaya, ya…
Read More
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙalubalanci Obasanjo kan kalamansa ga dimukraɗiyyar Nijeriya

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙalubalanci Obasanjo kan kalamansa ga dimukraɗiyyar Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo kan halin da dimokraɗiyyar Nijeriya ke ciki a halin yanzu. Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Bayo Onanuga, mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, ya nuna cewa Obasanjo na da tasiri kai tsaye kan irin dimokuradiyyar da al’umma ke yi a yau. Ya ce tasirin Obasanjo ya kai wa’adi biyu a matsayin shugaban qasa, na farko a matsayin shugaban farar hula daga 1999 zuwa 2007 sannan a matsayin shugaban qasa na soja daga 1976 zuwa 1979.…
Read More
Liverpool tana shirin faɗaɗa Anfield kafin wasanta da Manchester United

Liverpool tana shirin faɗaɗa Anfield kafin wasanta da Manchester United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Liverpool na shirin buɗe saman filin wasanta na Anfield lokacin da za ta fafata da Manchester united a ranar 17 ga watan Disamba. Wannan dai na cikin wani shiri na faɗaɗa filin da ta ke yi daga mai ɗaukar mutum 7,000 zuwa 61,000, wanda zai ci maau kallo miliyan 80. Ana cewa aikin zai samu tsaiko zuwa 2024, bayan ƙungiyar ta sauya kwataragi da kamfanin da za su yi aikin. Amma Liverpool ta ce shirin buɗe filin wasan gabanin wasanta da Manchester na ƙila-wa-ƙala, domin sai masana sun yi nazari kai, saboda kare rayuwar 'yan kallo.…
Read More
Shakira ta amince da biyan Ƙasar Sifaniya tarar fam miliyan 6.5

Shakira ta amince da biyan Ƙasar Sifaniya tarar fam miliyan 6.5

Daga AISHA ASAS  Daga ƙarshe dai fitacciyar mawakiyar Colombia, Shakira ta cimma yarjejeniya da masu shigar da ƙara na Ƙasar Sifaniya kan sasantawa dangane da tuhumar almundahanar biyan haraji da ke kanta. Yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin fara zaman kotu da ita. Mawakiyar ta biya tarar Yuro miliyan 7.5m, duk da cewa, a buƙatar masu gabatar da ƙara a yanzu sun so a ɗaure ta tsawon shekara takwas, sannan a ci ta tarar Yuro miliyan 23.8, idan aka same ta da laifi.  Kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito maku a 'yan watannin baya, mawaƙiyar ta…
Read More
An sallami wata jaruma daga fim bisa wallafa goyon bayan Falasɗinawa

An sallami wata jaruma daga fim bisa wallafa goyon bayan Falasɗinawa

Daga AISHA ASAS  Wata jaruma da ta ke aikin ɗaukar wani fim mai suna 'Scream' ta zama korarriya dalilin wallafa saƙon nuna goyon bayanta ga Ƙasar Falasɗinu, tare da barranta kanta daga irin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza. Jarumar ta nuna matuƙar damuwa da halin da mutane ke ciki a Gaza, inda akai-akai ta ke wallafawa a shafukanta na sada zumunta ababen da ke wakana dangane da yaƙin Isra'ila a Gaza. A cikin irin rubutun nata, jarumar mai suna Melissa Barrera, ta zargi Isra’ila da aikata 'kisan ƙare dangi' wanda ke da ƙudurin shafe wata al'umma daga…
Read More
Masallacin Adogba: Sarkin Musulmi da Makinde sun kafa turbar kawar da ƙabilanci da bambancin addini

Masallacin Adogba: Sarkin Musulmi da Makinde sun kafa turbar kawar da ƙabilanci da bambancin addini

Daga AISHA ASAS A kwanaki ne aka ƙaddamar da babban masallacin Juma’a na unguwar Adogba da ke garin Ibadan wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya jagorancin buɗewa, Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gina, bayan da a ka rusa tsohon masallacin a shekara ta 2019, don sabunta ta don samar da qarin fahimtar juna da kuma kawar da bambancin ƙabilanci da na addini. A lokacin da gwmanatin jihar Oyo ta rusa masallacin Adogba wanda ake kuma kira da ‘Organisation of Tadhamunul Muslimeen Mosque’, da ke Adogba, a kan hanyar Iwo a cikin garin…
Read More
Hare-haren Isra’ila kan Falasɗinawa: Ban taɓa ganin irin wannan rashin imani ba – Abu Shawesh

Hare-haren Isra’ila kan Falasɗinawa: Ban taɓa ganin irin wannan rashin imani ba – Abu Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jakadan Falasɗinawa a Nijeriya, Abu Shawesh ya bayyana cewa, bai tava ganin irin wannan rashin tausayi da tsantsan rashin ba kamar yadda Isra'ila ke ta varin wuta kan fararen hula a Ƙasar Falastɗinu. Ya ce, Martin Griffiths, a cikin hirarsa ta tashar CNN, ya ce, "bai tava ganin wani abu makamancin haka a baya ba, kisan gilla na rashin imani tsantsa." Ya ƙara da cewa, sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama, da harbin bindiga, harbin sari-ka-noƙe, har zuwa saukar da bama-bamai ta sama, adadin waɗanda suka mutu a tsakanin Falasɗinawa ya zarce dubu goma…
Read More