23
Nov
Daga WAKILINMU Jakadan ƙasar Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh, ya ce mamayar da ƙasar Isra’ila ta yi a Gaza ba komai bane illa ta yi shi da nufin aiwatra da kisan kiyashi. Shawesh ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a ofishin jakadancin ƙasar na Nijeriya dake Abuja. Kazalika ya koka kan yadda ake kai hare-haren kan fararen hula babu ƙaƙƙautawa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, da sunan ana yaƙar dakarun Hamas wanda duniya ta san ba haka ba ne. da yake buga misali kan irin rashin imanin da Isra’ila…
