22
Nov
Daga AISHA ASAS A daidai lokacin da shahararren jarumi a masana'antar fim ta Kudu, wato Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu ke kwance gadon jinya tare da alhinin iftila'in da ya saukar masa, its kuwa maiɗakinsa mai suna Stella Maris, da kuma 'yarsa ta riqo Jasmine Okafor, suka fara nuna wa juna yatsa danganen da kuɗaɗen da abokanen sana'arsa da masoyansa na faɗin duniya suka yi tururuwar tura masa, sa'ilin da aka nemi taimakon jama'a don sama masa lafiya. Kamar yadda sanannen shafi a kafar sada zumunta ta Instagram, Gistlover, ya wallafa hoton firar 'yar ta…
