Editor

9513 Posts
Google ya bayar da gargaɗin mako uku ga masu amfani da Gmail

Google ya bayar da gargaɗin mako uku ga masu amfani da Gmail

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwanan nan Google ya ba da gargaɗi na makonni uku ga masu asusun Gmail, wanda ke nuna alamar share miliyoyin asusun a wata mai zuwa a matsayin wani ɓangare na sabunta dandamali. Wannan yunƙurin zai shafi duk asusun Google waɗanda ba a yi amfani da su ba aƙalla shekaru biyu, wanda ya haifar da cire imel na dindindin, takardu, maƙunsar bayanai, alƙawuran kalanda, hotuna, da bidiyoyi. Sabuwar manufar, wacce aka gabatar a farkon wannan shekarar, an tsara ta fara aiki a watan Disamba na 2023. Babban maƙasudin da ke bayan wannan yunqurin shi ne don haɓaka…
Read More
An buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da kuɗaɗen Abacha wajen cigaban matasa

An buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da kuɗaɗen Abacha wajen cigaban matasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Joseph Effiong, Shugaban Yaxa Labarai na UpdateAfrika Communications ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da dala miliyan 150 da tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya Sani Abacha ya wawashe inda wajen cigaban matasan Nijeriya, da zarar Faransa ta sake kuɗaɗen. Effiong ya ce, kamata ya yi gwamnati ta mutunta shawarar da Faransa ta bayar na tura kuɗaɗen zuwa ayyukan raya ƙasa, kuma kada ta bari ya tafi yadda ya tafi a baya. Da ta ke magana game da kuɗaɗen Abacha, Catherine Colonna, ministar Turai da harkokin wajen Faransa, ta ce mayar da kuɗaɗen zai biyo…
Read More
Gwamnan Binuwai ya kai bantensa a Kotun Ɗaukaka Ƙara

Gwamnan Binuwai ya kai bantensa a Kotun Ɗaukaka Ƙara

Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta yi watsi da ƙarar da Jam'iyyar PDP a Jihar Binuwai da ɗan takarar gwamnanta, Titus Uba suka shigar. Masu ƙarar na ƙalubalantar hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta yanke ne a ranar 23 ga Satumba inda ta kori ƙarar tasu kana ta tabbatar da nasarar Hyacinth Alia na Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. Alƙalan kotun sun ce ƙarar ba ta darajar da za a saurare ta. Kotun ta ce PDP da ɗan takarar nata sun gaza gabatar da ƙwararan hujjoji don kare zargin amfani da…
Read More
Bisa shirin saƙi da cin zarafin mata na “EU-UN Spotlight Initiative”, mun samu gagarumin cigaba – Uwargidan Gwamnan Legas

Bisa shirin saƙi da cin zarafin mata na “EU-UN Spotlight Initiative”, mun samu gagarumin cigaba – Uwargidan Gwamnan Legas

Daga WAKILINMU Uwargidan Gwamnan Jihar Legas, Dr. Ibijoke Sanwo-Olu, ta bayyana cewa, sakamakon goyon bayan da suka samu daga shirin Tarayyar Turai (EU) da Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) na yaki da cin zarafin mata, Jihar Legas ta samu gagarumin ci gaba wajen samar da al’ummar da kowace ‘ya mace za ta iya rayuwa ba tare da tashin hankali ko nuna mata wariya ba. "Ta hanyar haɗin gwiwar da muka yi, mun sami ci gaba sosai wajen samar da al'ummar da kowace mace za ta yi rayuwa ba tare da tashin hankali da wariya ba." Ta bayyana a wurin rufe shirin…
Read More
Darakta a Kannywood, Aminu S. Bono ya riga mu gidan gaskiya

Darakta a Kannywood, Aminu S. Bono ya riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH Allah ya yi wa darakta a Kannywood, Aminu Surajo Bono, rasuwa a yammacin Litinin, 20 ga Nuwamba, 2023, bayan da ya yanke jiki ya faɗi. Da safiyar Talata, 21 ga Nuwamba, ake sa ran za a yi jana’izar marigayin a Kano. Wannan rashi ya kaɗa ‘yan fim su da sauran jama'a ainun, musamman ganin yadda rasuwar tasa ta yi ba-zata, ba ciwo ba ko hatsari. Marigayi Aminu yana daga cikin daraktocin da tauraronsu ke haskawa, musamman a ɓangaren bada umarnin shirya waƙa. Ya yi firamare da sakandire a Kano, sannan ya fara fim a shekarar 1999.
Read More
Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Rahotanni daga Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) sun nuna cewa, aƙalla gurɓata muhalli na sanadiyyar salwantar rayukan kusan mutum miliyan goma a duniya a kowace shekara. Wani babban abin tashin hankalin shi ne Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirika da wannan matsala ta yi ƙamari a cikinta, kuma ita ce ta huɗu a cikin jerin ƙasashen duniya da ake fama da wannan matsala ta gurɓata muhalli. Domin kuwa ƙididdiga ta nuna cewa, duk cikin ’yan Nijeriya dubu ɗari, akwai mutum ɗari da hamsin da ke mutuwa sakamakon shaƙar gurɓatacciyar iska a kowace shekara. A ƙasar Afganistan mutum 406,…
Read More
PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi a Taraba

PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi a Taraba

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar PDP a Jihar Taraba ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar kwanan nan. A ranar Lahadin da ta gabata Hukumar Zaɓe ta Jihar Taraba, TSIEC, ta bayyana cewa PDP ce ta lashe zaɓen ciyamomi a ilahirin ƙananan hukumomi 16 da jihar ke da su, kana ta samu kansiloli guda 168. Shugaban hukumar zaɓen jihar, Dr. Philip Duwe, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen a Jalingo, babban birnin jihar, inda ya ce shida daga cikin jam'iyyu 19 da aka yi wa rijista ne suka shiga zaɓen. Dr Duwe ya yaba wa 'yan jarida bisa…
Read More
Manufar Gidauniyar Hausa da Haɗa kan Hausawan Duniya shi ne martaba kimar Bahaushe – Dr Saidu

Manufar Gidauniyar Hausa da Haɗa kan Hausawan Duniya shi ne martaba kimar Bahaushe – Dr Saidu

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban Gidauniyar haɗa kan Hausa da Hausawan Duniya, Dakta Sa'idu Muhammad Ghana ya bayyana cewa kusan shekaru huɗu da kafata tana cigaba da samun karɓuwa sosai a tsakanin Hausawa a faɗin duniya. Ya bayyana haka ne da yake zantawa da 'yan jarida a Kano ya ce sun assasa gidauniyar ne da kyakkyawan manufa ta haɗa kan al'ummar Hausawa a duniya duk inda Bahaushe ya samu kansa ya zama ana taimakawa juna da ƙulla dangantaka da kyautata rayuwa. Ya ce "akwai sosa rai matuqa idan ka je wasu ƙasashen sai ka ga yara ƙanana masu jin…
Read More
Matasa ku guji faɗa wa harkar zinace-zinace

Matasa ku guji faɗa wa harkar zinace-zinace

Assalam alaikum. Babban abin da ke addabar matasa maza da mata shi ne, sha’awa. Kusan kullum matasa na faɗawa cikin bala’in fasiƙanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kaucewa haka. Idan mutum ya yi duba na tsanaki tare da la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani da muke ciki zai ga cewar da yawa wasu na faɗawa cikin aikata fasiƙanci ba cikin son ransu ba, sai don abin ya fi ƙarfinsu. Sau da yawa za ka ga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron Allah, ya san illar zina, ya san girman zunubinta, amma saboda fitinar sha’awa ya ka sa…
Read More
Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin yaranku

Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin yaranku

Assalamu alaikum, Manhaja. Barkan ku da aiki, muna muku fatan Allah ya ƙara muku ƙwazo, Ameen. Ina kuma muku addu’a Allah ya ƙara muku hikima da basirar aiki da kuma bunƙasa wannan jarida mai farin jini baki ɗaya. A Arewa ne za ka samu gidan Almajirai da yara ba adadi, a Arewa ne za ka samu iyaye sun sake yaran su ana kwashewa ana sauya musu addini, a Arewa ne za ka samu gidan kangararru inda ake tara ɗaruruwan yara wai da sunan sun gagari iyayensu. Kwanaki kaɗan da suka wuce wata baiwar Allah ta saka wani bidiyo a shafin…
Read More