An buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da kuɗaɗen Abacha wajen cigaban matasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Joseph Effiong, Shugaban Yaxa Labarai na UpdateAfrika Communications ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da dala miliyan 150 da tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya Sani Abacha ya wawashe inda wajen cigaban matasan Nijeriya, da zarar Faransa ta sake kuɗaɗen.

Effiong ya ce, kamata ya yi gwamnati ta mutunta shawarar da Faransa ta bayar na tura kuɗaɗen zuwa ayyukan raya ƙasa, kuma kada ta bari ya tafi yadda ya tafi a baya.

Da ta ke magana game da kuɗaɗen Abacha, Catherine Colonna, ministar Turai da harkokin wajen Faransa, ta ce mayar da kuɗaɗen zai biyo bayan kammala matakan shari’a.

“Wannan tsari ne mai tsawo, amma mun yi farin ciki da an kammala shi. A wasu lokuta, adalci yana iya yin tafiyar hawainiya, amma wannan nasara ce mai kyau sosai,” inji ta.

Colonna ta yi nuni da cewa, za a fara tattaunawa tsakanin gwamnatocin Faransa da Nijeriya, domin ware kuɗaɗen ga ayyukan raya kasa da za su amfanar da al’umma, kamar yadda gwamnatin Nijeriya ta sa gaba.

Effiong, wanda kuma mai fafutukar kare haƙƙin matasa ne, ya buƙaci gwamnati da ta baiwa matasa fifiko a cikin shirinta na kashe kuɗi, duba da irin rawar da suke takawa wajen bunƙasar tattalin arziki da cigaban ƙasa.

Ya ci gaba da cewa, matasa, waɗanda suka zama kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar Nijeriya, su ne mafi girman kadarorin Nijeriya, kuma babu shakka, mafi girman jarin cigaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya, siyasa da fasaha.

Ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da dukiyar da aka samu wajen kafawa da inganta shirye-shiryen tsoma bakin matasa da ake da su a fannonin ilimi, kwarewa, ci gaba, ƙarfafawa, aikin yi, da fasaha da dai sauransu.

“Gaba ɗaya saka hannun jari a waɗannan fannoni ba matasan Nijeriya kaɗai zai amfana ba har ma da ɗaukacin al’ummar ƙasar, domin hakan zai samar da yanayi mai kyau na bunasar tattalin arziki da cigaban ƙasa,” inji shi.

Effiong ya kuma buqaci jama’a musamman ƙungiyoyin farar hula (CSO) da kafafen yaɗa labarai da su kasance cikin shiri don ganin gwamnatin da ta shuɗe ta yi wa gwamnati mai ci ta hanyar tabbatar da cewa an dawo da abin da aka wawure a cikin tattalin arzikin ƙasa.

A kwanakin baya, Catherine Colonna, ministar kula da harkokin Turai da harkokin wajen ƙasar Faransa, ta bayyana aniyar qasar na mayar da kuɗaɗen da aka sace a matsayin martani ga buqatar da ma’aikatar shari’a ta Nijeriya ta gabatar ga gwamnatin Faransa da sauransu, na ƙarfafa alaqar da ke tsakanin ƙasashen biyu. .

Sanarwar da Faransa ta bayar tun daga lokacin ta taso da martani daga jama’ar da ke neman gwamnati ta ɗauki mataki, gabanin fitar da asusun.