Editor

9513 Posts
Boko Haram sun kashe jami’in Kwastam a Yobe

Boko Haram sun kashe jami’in Kwastam a Yobe

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari a rukunin gidajen Hukumar Kwastam da ke garin Geidam cikin Ƙaramar Hukumar Geidam, Jihar Yobe, inda suka kashe wani jami'in hukumar, Usman Gombe. Majiyarmu ta kalato cewar maharan sun yi dirar mikiya a kusa da hanyar Maine Soroa da motocinsu da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Asabar sannan suka shiga harbi da bindiga. A cewar majiyar, “Sun kai harin ne bayan da suka tabbatar da jami'an sun dawo gida daga wurin aiki. Jin yadda maharan ke ta ruwan alburusai ya sa jami'an neman mafaka, yayin da wasunsu…
Read More
Zamfara: Dauda ya ƙara yi wa Matawalle fallasa

Zamfara: Dauda ya ƙara yi wa Matawalle fallasa

*Gwamna ya zargi ministan da wawure biliyoyin kuɗi na aikin filin jirgi*Za a gurfanar da masu hannu ciki a gaban kuliya Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu zazzafar adawar siyasar dake tsakanin Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da wanda ya gaje shi kuma Ƙaramin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle, na ƙara yin tsamari a tsakaninsu, inda a baya-bayan nan gwamnan ya zargi ministan da wawure biliyoyin Dala na aikin gina filin jiragen sama na jihar ta Zamfara. Lawal ya ce, gwamnatin da ta shuɗe ta Bello Matawalle ta wawure biliyoyin Naira a filin jirgin sama na Zamfara, wanda daga…
Read More
Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a Nijeriya

Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An yanke wa wasu 'yan Nijeriya su biyar ɗaurin shekara 12 a gidan yari bayan kama su da laifin tono ƙoƙon kan wani mutum domin yin asirin yin arziƙi. Mutanen sun tono ƙoƙon kan ne domin kai wa wani boka, wanda ya ce ana buƙata domin yi musu asirin zama masu kuɗi. Mutanen waɗanda aka kama su da ƙoƙon kan a cikin wani buhu, sun amsa laifinsu a kotu. Mai gabatar da qara ya shaida wa kotu a jihar Neja da ke arewacin Nijeriya cewa mutanen sun zaƙulo gawar ce a wata maƙabarta bayan…
Read More
Tinubu ya naɗa Adewale Adeniyi shugabancin Hukumar Kwastam

Tinubu ya naɗa Adewale Adeniyi shugabancin Hukumar Kwastam

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Adewale Adeniyi a matsayin sabon shugaban Hukumar Yaƙi da Fasaƙwauri ta Nijeriya (NCS). Sanarwar da ta fito ta bakin Daraktantan yaɗa labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ta ce naɗin ya soma aiki ne daga ranar 19 ga Otoban 2023. Idan za a iya tunawa, a watan Yulin da ya shige Shugaba Tinubu ya naɗa Adeniyi riƙon ƙwaryar shugabancin hukumar ta Kwastam kana ya yi wa wasu jiga-jigan hukumar ritaya. Kazalika, naɗin ya shafi wasu jami'an hukumar da aka ɗaga matsayinsu zuwa mataimakan Kwantrola Janar. Jami'an da naɗin ya shafa sun…
Read More
Matasa sun gudanar da zanga-zanga kan rashin wutar lantarki A Kebbi 

Matasa sun gudanar da zanga-zanga kan rashin wutar lantarki A Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Ranar Litinin ɗin da ta gabata wata ƙungiya mai rajin kare mutuncin al'ummar yankin Kamba da kewaye mai suna Concerned Citizen a garin Kamba dake jihar Kebbi ta gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna ƙin jinin hukumar samar da wutar lantarki ta KAEDCO kan saɓa yarjejeniya da suka yi. Malam Musa Kamba ya bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja da cewa zanga-zangar ta lumana ta biyo bayan saɓa yarjejeniya da suka yi tsakaninsu da ofishin Hukumar samar da wutar lantarki ta KAEDCO da ke kulawa da wannan yankin na cewa a kullum za su ba garin…
Read More
Gombe a shekara 27: Tarihi ba zai manta da shugabannin jihar ba – Zannan Gombe

Gombe a shekara 27: Tarihi ba zai manta da shugabannin jihar ba – Zannan Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Maigirma Zannan Gombe, Alhaji Baba Gana Goni, ya yi imani da cewa, duk shugabannin da suka mulki Jihar Gombe tun da ta samu ‘yancin kanta daga Jihar Bauchi ranar ɗaya ga watan Oktoba, 1996, wato shekara 27 kenan, mutane ne masu kishi da kuma hangen nesa. Zannan ya yi wannan iƙirarin ne yayin tattaunawa da manema labarai a ofishinsa a garin Gombe cikin makon jiya, a kan cikan shekara 27 da jihar ta yi, inda ya yi nuni da cewa, ci gaban da jihar ta samu cikin wannan tafiya (shekara 27), abin alfahari ne ga…
Read More
Abinda ya sa ba zan binciki gwamnatin Masari ba – Raɗɗa

Abinda ya sa ba zan binciki gwamnatin Masari ba – Raɗɗa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya ce, ba zai binciki gwamnatin tsohon gwamnan jihar da ya gada, Alhaji Aminu Masari, ba, saboda shi ma yana cikin gwamnati tasa. Malam Raɗɗa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC ranar Alhamis. Ya ce: “Babu wani shiri na bincikar wanda ya gabace ni. Kuma ina da dalilai guda biyu na faɗar haka. “Na farko ina cikin waɗanda suka kafa gwamnatin Aminu Bello Masari. Don haka ba ku tsammanin zan binciki gwamnati, wacce nake cikinta. “Kuma ko da ma…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ƙanin Sarkin Zazzau, Mansur Nuhu Bamalli ya kwanta dama

Da Ɗumi-ɗumi: Ƙanin Sarkin Zazzau, Mansur Nuhu Bamalli ya kwanta dama

Sanarwar da mai magana da yawun Masarautar Zazzau ya fitar ta ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Legas a hanyarsa ta zuwa ƙasar Moroko. “Za a sanar da lokacin da za a yi jana'izarsa nan gaba kaɗan," in ji sanarwar. Ya rasu yana da shekara 52, sannan ya bar mata guda da 'ya'ya biyu. Kafin rasuwarsa, Mansur Nuhu Bamalli shi ne jakadan Nijeriya a Ƙasar Moroko. Haka nan, shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ɗan uwa gs Mai Martaba Sarkin Zazzau.
Read More
Malamin Musulunci ya kwaɗaitar da attajirai falalar taimaka wa marayu

Malamin Musulunci ya kwaɗaitar da attajirai falalar taimaka wa marayu

Daga MOH'D BELLO HABIB a Zariya Wani malamin addinin Islama dake Zariya, Malam Umar Magaji ya buƙaci attajirai da 'yan siyasa da su taimaka wa marayu da zawarawa da miskinai da faƙara'u da masu buƙata ta musamman da abinda za su ci. Malamin ya yi wannan kiran ne lokacin da yake zantawa da wakilin Manhaja a Zariya kan halin ƙunci da mutanen ƙasar nan musamman masu ƙaramin ƙarfi suke ciki. Ya ce tabbas talakawa na cikin ƙuncin rayuwa saboda tsadar kayan abinci da dukkan kayan masarufi da kuma matsin tattalin arziki.  Malam Umar ya ce yakamata attajirai da 'yan siyasa…
Read More
Majalisar Ɗinkin Duniya za ta samar da sabon tsarin zaman lafiya a Kaduna da Katsina

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta samar da sabon tsarin zaman lafiya a Kaduna da Katsina

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Gutteres ya ɗauki nauyin samar da wani tsari mai suna "Ƙarfafa Zaman Lafiya a Kananan Hukumomi da Jihohin Katsina da Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya". Yankin Arewa maso Yamma, musamman Jihohin Kaduna da Katsina, na fama da matsalolin da suka shafi rikicin manoma da makiyaya da rikicin ƙabilanci da ta’addanci da sauransu. Domin samun nasarar tsarin, an gudanar da wani taro na musamman a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja, ranar Alhamis, don neman goyon baya da tabbatar da zaman lafiya da yaki da ‘yan bindiga musamman a Jihohin Kaduna…
Read More