Editor

9513 Posts
An ɗauki tubabbun ’yan daba aikin ɗan sanda a Kano

An ɗauki tubabbun ’yan daba aikin ɗan sanda a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, reshen Jihar Kano ta ƙaddamar da tubabbun 'yan daba 50 waɗanda ta ɗauka aikin ɗan sanda a jihar bayan kammala horo na wata biyu. Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Abdullahi Kiyawa, ta ce an zaɓo mutanen ne daga ƙananan hukumomin Municipal, da Dala, da Ungoggo, da Gwale, da Fagge, inda aka ɗauki mutum 10 kowaccensu. Da yake jawabi ranar Litinin a birnin Kano, Kwamishinan 'Yan Sanda Mohammed Usaini Gumel ya ce 'yan daba 222 ne suka tuba tare da miƙa makamansu a birnin. Birnin Kano ya fuskanci hauhawar faɗan daba da kuma…
Read More

INEC za ta haɗa gwiwa da gidajen jarida don daƙile labaran bogi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi kira da a kara haɗa kai da manema labarai a ƙoƙarin da ake na yaƙi da labaran bogi. Hukumar zaɓen ta bayyana hakan ne a ranar Talata a Akwanga, jihar Nasarawa, cewa haɗin gwiwar zai kuma rage yaɗuwar munanan bayanai da kuma yadda ake gudanar da zaɓe. INEC ta yi wannan kiran ne ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban Hukumar, MRotimi Oyekanmi, a wajen wani taron ƙarawa juna sani na kwanaki biyu ga Hukumar Yaɗa Labarai ta INEC. Taron ya mayar da hankali ne…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya tsige manyan daraktocin NOA, NBC, FRCN da wasu

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya tsige manyan daraktocin NOA, NBC, FRCN da wasu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsige shugabanni wasu hukumomin gwamnati ƙarƙashin Ma'aikatar Yaɗa Labarai. Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta nuna tsigewar ta shafi shugabannin hukumomin NOA da FRCN da NBC da dai sauransu. Haka sanarwar, ta ce Tinubu ya baɗa sabbin shugabanni da za su maye huraben waɗanda aka tsige. Ga sabbin naɗe-naɗen kamar haka: 1) Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) — Mr. Lanre Issa-Onilu (2) Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA) — Mr. Salihu Abdulhamid Dembos (3) Tashar Rediyo ta…
Read More
An zo wajen: An samu manhaja mai tuve mutum tsirara!

An zo wajen: An samu manhaja mai tuve mutum tsirara!

TIJJANI MUSA MUHAMMAD WAllaahi mun faɗa wajen shekaru goma sha uku baya (2010) cewa, matan Musulmi, 'yan Arewa musamman Hausawa su kiyayi ɗora hotunansu a shafukan sada zumunta tun wancan lokacin a Fesbuk. Ba don komai ba sai don gudun wasu waɗanda ba Musulmi ba za su iya sauke su a cikin wayoyinsu ko na'urorinsu su dinga kallon su suna sha'awarsu ko su yi wasu abubuwan da ba shikenan ba da hotunan. Aka samu wasu a cikinmu da ba sai na ambaci suna ba mazansu da mata suka ƙalubalanci wannan jan hankali da kashedi da muka yi suna cewa muna…
Read More
Kusan duk wani fim da ake saka wa Arewa24 na ɗora murya akwai ni a ciki – Maryam Hotoro

Kusan duk wani fim da ake saka wa Arewa24 na ɗora murya akwai ni a ciki – Maryam Hotoro

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Maryam Ibrahim Hotoro da aka fi sani da Maryam Hotoro, jaruma ce a masana'antar fim ta Kannywood kana ma'aikaciya ce a tashar Arewa24, ƙwararriya a wajen fassara da kuma ɗora murya. A tattaunawar ta da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma yadda ta zama mawaƙiya inda har ta buɗe kamfanin waƙoƙin bikin aure. Ku biyu mu: MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki? MARYAM HOTORO: Sunana Maryam Ibrahim Hotoro, amma anfi kirana da Maryam Hotoro. Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihinki? An haife ni a…
Read More
Na fi gane na buga littafi maimakon na saka a onlayin – R.A. Adam

Na fi gane na buga littafi maimakon na saka a onlayin – R.A. Adam

"Masu hali ba sa ƙarfafa gwiwar marubuta" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Rufa'i Abubakar Adam, wanda aka fi sani da R.A. Adamu, wani matashin marubuci ne da ya taso cikin sha'awar karance-karance da rubuce-rubuce har kafin Allah ya sa ya zama mai aikin ɗab'i da zane-zane a na'urar kwamfuta. Yana daga cikin matasan marubutan da suka kafa ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Gombe (GAMJIG), domin haɗa kan marubutan Gombe da samar da wasu hanyoyi na bunƙasa cigaban adabi da harshen Hausa. Gwagwarmayar da ya sha a baya a yayin ƙoƙarinsa na ganin ya zama marubuci ya silar kawo sauyi a Jihar Gombe,…
Read More
Nijeriya @63: Ranar ‘yancin kai ko ranar bautar da kai?

Nijeriya @63: Ranar ‘yancin kai ko ranar bautar da kai?

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI Tun bayan da aka ba wa Nijeria 'yancin kai na shekaru 63, har yanzu Nijeriya ba ta samu wata guda ba cir ba tare da an ɗauke wutar Lantarki ba a duk sassan faɗin ƙasar. Wannan shi ne 'yancin kai?! Na tava hira da wani matashi a ƙasar waje zai kai shekaru 25 a wancan Lokacin. Ya ce, ya ɗauka wutar lantarki halitta ce kamar rana da wata da taurari. Har sai da ya ƙara wayo sannan ya gane cewa fasaha ce. A Nijeriya yaro ɗan shekara biyu ya san Idan aka ce NEPA! Ana nufin…
Read More
Yakamata iyaye da sarakuna ku daina kashe kes na cin zarafi a tsakaninku – Rabi Salisu

Yakamata iyaye da sarakuna ku daina kashe kes na cin zarafi a tsakaninku – Rabi Salisu

“Za mu tabbatar da ƙwatar wa marasa ƙarfi ’yancinsu” Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamishinar Jinƙai da Walwalar Al'umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim (Garkuwar Marayun Zazzau), wata jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi, da son taimaka wa al'umma. Tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafa wa waɗanda aka zalunta, zawarawa da marayu ne ya sa ta kafa Gidauniyar Arrida, wacce a dalilin ta mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana, kuma rayuwarsu ta inganta, wanda kuma a dalilin hakan ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya naɗa ta a…
Read More
Mutum uku ne suka ɗora Tinubu

Mutum uku ne suka ɗora Tinubu

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA Ranar 25 ga watan Fabrairu 2023, jama'ar ƙasar nan suka fita filin zaɓe domin su zaɓi wanda zai mulke su tsawon shekara huɗu. Mutum huɗu ne suka fi samun tagomashi. Na ɗaya, ɗan takarar jam'iyyar APC wadda ke kan mulki, Jagaban Borgu, Bola Ahmed Tinubu. Na biyu Wazirin Adamawa Atiku Abubakar na PDP, na uku Peter Obi, na LP, sai na hudu Injiniya Rabiu Kwankwaso na NNPP. Hukumar zaɓe ta ƙasa ta bai wa mutane miliyan 93 katin zaɓe. Amma da aka zo hakikanin zaven, kashi 27 ne suka fito. Da quri'ar Tinubu da Atiku da…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Olukoyede a matsayin shugaban EFCC

Da Ɗumi-ɗumi: Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Olukoyede a matsayin shugaban EFCC

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Ola Olukoyede a matsayin sabon Shugaban Hukumar EFCC a yayin zaman da ta yi a ranar Laraba. Haka nan, Majalisar ta tabbatar da naɗin Muhammad Hammajoda a matsayin Sakataren hukumar ta EFCC. Naɗin nasu ya biyo bayan kammala tantance su da majalisar ta yi. Idan za a iya tunawa a ranar 12 ga Oktoban 2023 Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar, sannan Hammajoda a matsayin sakatare.
Read More