Editor

9513 Posts
Dalilin Gwamnati na ƙaddamar da shirin ‘cash transfer’ – Minista

Dalilin Gwamnati na ƙaddamar da shirin ‘cash transfer’ – Minista

A ranar Talatar da ta gabata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin bada tallafi ga 'yan ƙasa na 'Renewed Hope Conditional Cash Transfer', shirin da ake sa ran magidanta miliyan 15 za su amfana da shi. An ƙaddamar da shirin ne a Fadar Villa da ke Abuja albarkacin Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya ta bana. Yayin ƙaddamar da shirin, Shugaba Tinubu ya miƙa cekin N25,000 ga wasu daga cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin: Larai Suleiman, Shuaibu Hassana, Sariki Bala Gamu, Okor Jonah da kuma Hameed Kosemani Isiaka. Wakilin Tinubu a wajen taron kuma Sakataren Gwamnatin…
Read More
Yadda rikicin Isra’ila da Falastinawa ya samu asali a tarihi

Yadda rikicin Isra’ila da Falastinawa ya samu asali a tarihi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rikici tsakanin Isra'ila da Falastinu ya na da dogon tarihi, amma za mu ɗauko shi daga ƙarni na 19 a lokacin da Yahudawa bisa jagoranci wani ɗan jarida Bayahude ɗan asalin ƙasar Sweeden mai suna Theodore Herzl, suka shirya wani muhimman taron a birnin Bale na ƙasar Sweezerland, wanda sakamakon shi suka ƙirƙiro abinda suka kira 'Sionisme', wato ƙungiyar ƙwatar 'yanci Yahudawa da kuma komawarsu a tsaunin Sion, wanda suka ce nan ne ƙasar ta asali. Sun ƙaddamar da wannan shiri dalili da azabar da kuma wariyar da Yahudawan su ka ce su na fama da…
Read More
Adamu Aliyu ya zama sabon Shugaban ICPC

Adamu Aliyu ya zama sabon Shugaban ICPC

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dr. Musa Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC gabanin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin. Kazalika, Tinubu ya Mr. Clifford Okwudiri Oparaodu a matsayin sakataren hukumar. Bayanin naɗin na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata. A cewar sanarwar, an naɗa Adamu Aliyu shugabancin ICPC ne domin maye gurbin tsohon shugaban hukumar wanda wa'adin shugabancinsa ya zo gab da ƙarshe. Ta ƙara da cewa Dr. Musa Adamu Aliyu babban lauya ne wanda ya riƙe muƙamai da dama, ciki…
Read More
Kotu ta tsige ɗan Majalisar Wakilai daga Adamawa

Kotu ta tsige ɗan Majalisar Wakilai daga Adamawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta tsige ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Adamawa, wato Hon. Jingi Rufai, na jam'iyyar PDP. Kafin wannan lokaci, Jingi Rufai shi ne mai wakiltar Mubi ta Arewa, Mubi ta Kadu da Maiha a Majalisar Wakilai ta Ƙasa. Kotun ta yanke hukuncin haka ne a zaman da ta yi a ranar Talata, inda ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Hon. Jaafar Magaji, a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Kotun ta kuma bai wa hukumar zaɓe IMEC umarni a kan ta miƙa wa Magaji shahadar lashe zaɓen ba tare da wani jinkiri ba. Wannan na…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe jama’a da dama, sun yi awon gaba da wasu a Kano

‘Yan bindiga sun kashe jama’a da dama, sun yi awon gaba da wasu a Kano

'Yan bindiga a Jihar Kano sun yi garkuwa da mutanen da ba a tantance yawansu ba kana sun kashe wasu a hare-haren da suka kai a yankunan Ƙaraye da Rogo a jihar. Wani mazaunin yankin Ƙaraye da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa majiyarmu cewa, 'yan bindigar sun kai hari yankin ne tsakanin Asabar da Lahadin da suka gabata kuma a lokuta daban-daban. “An sanar da cewar a ranar farko da aka kai harin, kimanin mutum huɗu aka kwashe sannan mutum biyu sun mutu, yayin da a rana ta biyu aka sace mutum biyu tare da kashe wasu…
Read More
Alamomin da mata ke ji da ke tabbatar da suna ɗauke da cutar sanyi

Alamomin da mata ke ji da ke tabbatar da suna ɗauke da cutar sanyi

Daga AISHA ASAS Mai karatu barka da yau, barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja. Har wa yau dai muna kan darasin ciwon sanyi, wanda idan ba a shafa'a ba, mun faro ne daga bayani kan ma'anonin da ake yi wa ciwon sanyi, zuwa bayyana adadi da karkasuwar ciwon. A wannan satin da yardar mai dukka, shafin Kwalliya zai yi duba kan alamomin da mace za ta ji da za su iya tabbatar mata tana ɗauke da ɗaya daga cikin nau'ukan ciwon sanyi na mata. Hakan kuwa wata dama ce da za ta iya taimaka wa wurin…
Read More
Falasɗinawa 500 sun mutu sakamakon harin Isra’ila a Gaza

Falasɗinawa 500 sun mutu sakamakon harin Isra’ila a Gaza

Rahotanni daga Falasɗin sun ce, ɗaruwan mutane ne suka rasa rayukansu a wannan Talatar sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan yankin Gaza na Falasɗinu ta sama. Bayanai sun ce mafi yawan hare-haren an kai su ne a kan wani asibiti da ke kula da waɗanda suka samu raunuka a wannan yaki. Majiyoyin kiwon lafiya a Gaza, sun ce adadin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon farmakin da Isra’ila ta kai a ranar Talata kawai ya kama daga 300 zuwa 500 ne. An dai kai waɗannan hare-hare ta sama ne a kan asibitin al-Ahli da ke Gaza, inda dubban fararen hula…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya tsige shugaban NAHCON ya maye gurbinsa da Jalal Arabi

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya tsige shugaban NAHCON ya maye gurbinsa da Jalal Arabi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Alhaji Ahmad Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) inda zai yi shekara huɗu a wa'adin farko. Bayanin naɗin na ƙunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Laraba. "Sabon Shugaban na NAHCON, Alhaji Jalal Ahmad Arabi, zai shiga ofis ne a matsayin muƙaddashi a ranar 18 ga Oktoba, daga bisani ya zama cikakken shugaba na hukumar na wa'adin shekara huɗu farawa daga ranar 17 ga Janairu," in ji sanarwar. Ahmad Arabi ya gaji wannan kujerar…
Read More
Dalilin Sanata Ndume na ficewa daga zauren Majalisa a fusace

Dalilin Sanata Ndume na ficewa daga zauren Majalisa a fusace

Da alama dai abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata wa Majalisar Dattawan Nijeriya musamman ganin yadda shugabanin majalisar suka shiga ganawar sirri mintoci ƙalilan da fara zaman majalisar a ranar Talata. Yayin zaman Majalisar a ranar Talata an ga Mai Tsawatarwa na Majalisar, Sanata Ali Ndume (APC Borno ta Kudu), ya yi ƙoƙarin nusar da Majalisar dangane da kurakuran da ake zargi Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya tafka ba tare da an yi gyara ba. Kuskuren da Ndume ke nufi shi ne kan batun ƙudirin da Sanata Summaila Kawu (NNPP Kano ta Kudu) ya gabatar a majalisa kan buƙatar…
Read More
Yaƙin Isra’ila da Hamas: Tura ta kai bango

Yaƙin Isra’ila da Hamas: Tura ta kai bango

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani hoton bidiyo da na gani ya nuna wasu ƙananan yara mata suna la'antar wasu sojojin Isra'ila da ke cikin shirin yaƙi a wani yanki na ƙasar Falasɗinu da ke ƙarƙashin mamayar yahudawan Isra'ila, yayin da sojojin ke korar yaran su tafi gida. A gefe guda kuma ’yan jarida ne ke ɗaukar hotunan abubuwan da ke faruwa. Babu mamaki hakan ya sa sojojin kasa ɗaukar wani mataki a kan yaran. Amma abin da na lura da shi shi ne yadda yaran ke magana cikin fushi yana qara nuna yadda al'ummar Falasɗinu ke cike da fushi…
Read More