Editor

9513 Posts
Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya: Sama da mutum biliyan ɗaya na fama da talauci – Sakataren MƊD

Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya: Sama da mutum biliyan ɗaya na fama da talauci – Sakataren MƊD

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, MƊD, Antonio Gutteres, a cikin jawabinsa na ranar kawar da talauci ta duniya, ya yi iƙirarin cewa, a wannan duniyar tamu mai cike da ɗimbin arziki, bai kamata Talauci ya yi ma ta katutu ba. Gutteres ya ce, duk da ɗimbin arzikin cikin duniyarmu amma kusan mutane miliyan 700 ke fama da ƙalubalen rayuwa, inda suke rayuwa a ƙasa da dala 2.15 daidai da naira N2,000 a duk rana. Sama da mutane biliyan ɗaya ne ke fama da matsananciyar rayuwa daga ƙarancin abinci, ruwa, lafiya da ilimi. Akwai biliyoyin mutane da ba su da tsaftataccen…
Read More
‘Yan Majalisar Wakilai sun mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da ake yi game da batun saya musu motocin alfarma

‘Yan Majalisar Wakilai sun mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da ake yi game da batun saya musu motocin alfarma

Majalisar Wakilai ta ƙasa ta mayar da martani a kan ce-ce-ku-cen da 'yan ƙasa ke yi game da batun saya wa mambobinta su 360 sabbin motocin alfarma. A cewar Majalisar, za a sayi motocin ne don aikin ofis, kuma kuɗin da ake cewa za a sayo motocin bai kai yadda ake zuzutawa ba. A hirarsu da BBC, Honorabul Kabiru Alasan Rurum mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya daga jihar Kano a Majalisar, ya ce: "Tun da mu ne karkatacciyar bishiya mai daɗin hawa kusan duk abubuwan a kanmu yake, ya kamata idan za a yi abu a…
Read More
Wa ke da alhaki a auri-saki a ƙasar Hausa?

Wa ke da alhaki a auri-saki a ƙasar Hausa?

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a filinku na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu yi magana ne game da auri-saki a ƙasar Hausa. Ko ba a gaya maka ba mai karatu za ka yi wa kanka alƙalanci cewa ƙasar Hausa tana neman zama shalkwatar mace-macen aure a Nijeriya. Domin idan ka dubi sauran ƙabilu, ba su fiye samun wannan matsala ta saurin mutuwar aure da sakewa ba kamar yadda muke yi a nan yankin. A 'yan kwanakin nan ma da aka yi ta zance game…
Read More
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon kayan karatu ga makarantun gwamnati

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon kayan karatu ga makarantun gwamnati

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano La’akari da buƙatar da ake da ita na samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa, Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf a Litinin da ta gabata, ya ƙaddamar da rabon littattafai da kayayyakin tallafin karatu ga makarantun firamare da sakandiren gwamnati a faɗin jihar a wani taron da aka gudanar a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnati. Da yake jawabi, Gwamna Abba Kabir ya ce samar da kayayyakin ya yi daidai da kishin gwamnatinsa na inganta harkar karatu a makarantun gwamnati da kuma cika buri na al’ummar jihar, inda ya tabbatar da…
Read More
Gwamna Sanwo-Olu ya sake buɗe kasuwar Mile 12 kwana biyu bayan rufe ta

Gwamna Sanwo-Olu ya sake buɗe kasuwar Mile 12 kwana biyu bayan rufe ta

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bada umarnin gaggawa kan sake buɗe fitacciyar kasuwar nan ta Mile 12 biyo bayan gamsuwa da matakan tsaftace muhalli da aka ɗauka a kasuwar. A ranar Juma'ar da ta gabata gwamnatin jihar ta rufe kasuwar Mile 12 tare da kasuwar Owode Onirin saboda dalilai masu nasaba da rashin tsaftace muhalli. Sanarwar da gwamnatin ta fitar a ranar Litinin ta bakin Kwamishinan Muhalli da Ruwa na jihar, Mr Tokunbo Wahab, ta ce an sake buɗe kasuwar ce bayan gamsuwa da matakan tsaftace muhallin da aka ɗauka a kasuwar Kwsmishinan ya ce gwamnatin jihar ba ta…
Read More
Tinubu ya sauya ranar taron Majalisar Zartarwa

Tinubu ya sauya ranar taron Majalisar Zartarwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya ranar da Majalisara Zartarwa (FEC) ta saba zama daga Laraba zuwa Litinin. Ministan Labarai, Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kamma taron majalisar a ranar Litinin. Taron wanda ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, wannan shi ne karo na biyu da Shugaban ke jagorantar taron tun bayan rantsar da shi a watan Mayun da ya gabata. Idris ya ce mai yiwuwa taron majalisar ba zai riƙa gudana a-kai-a-kai ba musammam idan babu wani muhimmin abu da za a tattauna. Kafin wannan…
Read More
Hanyoyin da za ki samar wa miji hutu da nutsuwa idan ya dawo gida

Hanyoyin da za ki samar wa miji hutu da nutsuwa idan ya dawo gida

Daga MUKHTAR YAKUBU  Gyara muhallin zama da kwanciyar sa ( palour da ɗaki)  Shirya masa abinci da abun sha a kan lokaci Tanadar masa da ruwan wanka  Tsara lokacin baccin yaranku Kimtsa jikin ki da amfani da turaren dare masu sanyi da kwantar da hankali ( dan Allah a kiyaye amfani da turare mai ƙarfi kamar na 'yan bori lokacin bacci, ana buƙatar abunda zai sa ma zuciya da ƙwaƙwalwa nutsuwa ne ba abunda zai hargitsa shi ya yi activating brain ɗin mutum ba)  In yana da gajiya a masa matsa/tausa mai sauke gajiya (a sa hankali a ƙeya, wuya,…
Read More
Kotu ta tsige sanatan Adamawa daga kujerarsa

Kotu ta tsige sanatan Adamawa daga kujerarsa

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja, ta tsige Sanata Ishaku Abbo mai wakiltar Adamawa ta Arewa daga kujerarsa. Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar ne a ranar Litinin inda ta karɓe kujerar Sanatan Adamawa ta Arewa daga hannu Abbo tare da bayyana ɗan takarar jam'iyyar PDP, Amos Yohanna a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Da yake ysokaci jim kaɗan bayan hukuncin da kotun ta yanke, Abbo ya yi alƙawarin zai yi sanarwa a shafinsa na facebook. Daga nan ya ui kira ga jama'ar mazaɓarsa kan cewa kowa ya kwantar da hankalinsa.
Read More
Tinubu ya rantsar da ƙarin ministoci uku

Tinubu ya rantsar da ƙarin ministoci uku

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da ƙarin ministoci guda uku a cikin majalisarsa. Minitocin da rantsawar ta shafa sun haɗa da Jamila Bio Ibrahim da Ayodele Olawande da kuma Balarabe Lawal. An rantsar da su ne a zauren Majalisar Zartarwa gabanin zaman majalisar wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin. Sabbin ministocin sun sha rantsuwar kama aiki ne makonni biyu bayan da Majalisar Dattawa ta tantance su. Tuni dai Shugaban Ƙasa ya miƙa wa kowannensu ma'aikatar da zai riƙe: Jamila Bio-Ibrahim – Babbar Minista Matasa, Ayodele Olawande - Ƙaramin Ministan Matasa, sannan Balarabe Lawal – Ministan Muhalli.
Read More
Ba da jimawa ba za a fara shiga daji da ni – Gwamna Raɗɗa

Ba da jimawa ba za a fara shiga daji da ni – Gwamna Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewar, da zarar an kammala duk shirye-shiryen da suka dace za a fara shiga daji da shi don farautar 'yan fashin daji. Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da BBC. "Nan ba da jimawa ba idan an kammala duk shirye-shiryen da suka dace za'a fara shiga daji da ni," inji Shi. Gwamnan ya ci gaba da cewa, zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kawo ƙarshen matsalar 'yan bindigar da suka addabi jihar. Don haka ne ya ƙuduri aniyar ganin bayan ‘yan bindigar…
Read More