16
Oct
Ma'aikatan Hukumar Tura Saƙonni (NIPOST) a babban ofishin hukumar da ke Abuja, sun yi zanga-zanga tare da rufe ma'aikatar saboda rashin amincewa da naɗa Tola Odeyemi a matsayin sabon shugaban hukumar da Shugaba Bola Tinubu ya yi. A makon da ya gabata Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya bada sanarwar cewa Shugaba Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe a hukumomin sadarwa ciki har da hukumar NIPOST. Sai dai jim kaɗan bayan sanar da naɗin Odeyemi, rahotanni suka nuna an sake maida babban jami'in hukumar da aka tsige da fari. An ga Adepoju a cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa yana…
