15
Oct
Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan; Hajiya Halima (Dada) rasuwa a mahaifarsa dake garin Gashuwa, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade a jihar Yobe. Yayin da yake sanar da rasuwar, Malam Yahaya Mato, a madadin iyalai da 'yan uwa, ya bayyana cewa Allah ya yi wa Hajiya Dada; 'yar kimanin shekaru 90 a duniya rasuwa a Unguwar Katuzu dake cikin garin Gashuwa. Haka zalika, sanarwar ta bayyana cewa za a yi jana'izar marigayiyar ne gobe Lahadi, 15 ga watan Oktoban 2023, da misalin ƙarfe 11:00 na rana a masallacin ƙofar…
