13
Oct
Daga AISHA ASAS Shahararriya kuma ƙwararriyar mai bayar da shawarwari kan zamantakewar aure da kuma rayuwa bakiɗaya, Khadija Ibrahim, marubuciya da ta jima tana gyara al'umma da alƙalaminta, ta shirya tsaf don bayar da ƙarin gudunmawa ga masu shirin yin aure, wato littafin da zai amsa tambayoyi ɗari har da ɗori da mata da maza suke buƙatar sani kafin su shige daga ciki. Littafin mai suna tambayoyi ɗari da ɗori kafin aure, wanda zai kasance a turance, wato '100+ questions before Nikkah' zai amsa kusan dukkan tambayoyin da ake buƙatar sani game da aure, waɗanda za su fitar da samari…
