12
Oct
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada aniyarsa ta tallafa wa makarantun sojoji da ke faɗun jihar. Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban makarantar sojoji ta Nigerian Army Education Corps (NAEC), Manjo Janar Bello Alhaji Tsoho, a Gusau, babban birnin jihar. Sanarwar da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce Shugaban makarantar ya kai ziyarar ne domin ƙarfafa alaƙa tsakanin makarantar da Gwamnatin Zamfara. Idris ya ƙara da cewa, Kwamandan ya nemi goyon bayan gwamnatin jihar kan ci gaba da kafa makarantun sosjoji a jihar. A cewarsa, “Gwamna Lawal…
