Zamfara: Dauda ya ƙara yi wa Matawalle fallasa

*Gwamna ya zargi ministan da wawure biliyoyin kuɗi na aikin filin jirgi
*Za a gurfanar da masu hannu ciki a gaban kuliya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Daga dukkan alamu zazzafar adawar siyasar dake tsakanin Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da wanda ya gaje shi kuma Ƙaramin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle, na ƙara yin tsamari a tsakaninsu, inda a baya-bayan nan gwamnan ya zargi ministan da wawure biliyoyin Dala na aikin gina filin jiragen sama na jihar ta Zamfara.

Lawal ya ce, gwamnatin da ta shuɗe ta Bello Matawalle ta wawure biliyoyin Naira a filin jirgin sama na Zamfara, wanda daga baya aka yi watsi da su.

Sabuwar gwamnatin ta zargi gwamnatin da ta shuɗe da yin almubazzaranci na Naira 6,775,949,561.50 na aikin filin jirgin dakon kaya da aka yi watsi da su a babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis da ta gabata a Gusau, Kakakin Gwamnan Jihar, Malam Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta kaɗu matuƙa da gano yadda gwamnatin da ta gabata ta wawure maƙudan kuɗaɗe na aikin filin jirgin saman dakon kaya na Zamfara da aka yi watsi da shi.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin Gwamna Lawal za ta gurfanar da waɗanda ke da hannu a wawure kuɗaɗe a gaban kuliya.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya an samu turka-turka tsakanin ɓangarorin biyu bisa zargin tattaunawar sirri da ’yan bindiga, inda har Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Tarayya ta tsoma baki a cikin batun.

Gwamna Dauda dai shine ya kayar da Bello Matawalle a zaɓen kujerar gwamnan jihar da ta gabata a yayin manyan zaɓuka Nijeriya na 2023, duk da cewa, Matawalle yana kan kujerar mulki a lokacin.

Daga bisani Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan, wanda ya fito faga jihar dake fama da mtsalolin tsaro, a matsayin ƙaramin Ministan Tsaro na Tarayyar Nijeriya.

Sai dai kuma Matawalle yana cigaba da ƙalubalantar Dauda a gaban kotu kan lashe zaven da ya yi, amma Kotun Zaɓe ta tabbatarwa Dauda da sahihancin zaɓensa.

A yanzu haka Matawalle ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara yana neman a jingine hukuncin ƙaramar kotun.