Editor

9513 Posts
Mahimmancin rubuta bayanan kasuwanci

Mahimmancin rubuta bayanan kasuwanci

Daga ZAUREN TASKAR NASABA Bayanan Kasuwanci (Record keeping) 'yan kasuwa masu yawa suna buƙatar ƙara sanin taskacewa ko rubuta bayanan kasuwanci abu ne mai matuƙar mahimmanci da kawo cigaban kasuwancin. Sai dai wasu cikin 'yan kasuwa basu ɗauki rubutun bayanan kasuwanci a matsayin abu mai amfani ba, don haka ba ruwansu da shi. Misali za ka samu ɗan kasuwa ya sayo atamfa a Kano a kan kuɗi N 9,000 ya ɗauke ta zuwa Adamawa ya sayar a kan Naira 9,500 yana tunanin ya ci ribar N500 wanda a zahiri haka ne, ya samu ribar N500. Amma ɗan kasuwa wanda yake…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta bankaɗo hujjoji kan yadda Matawalle ya kwashi kuɗin jihar da sunan aikin tashar jirgin sama

Gwamnatin Zamfara ta bankaɗo hujjoji kan yadda Matawalle ya kwashi kuɗin jihar da sunan aikin tashar jirgin sama

Gwamnatin Jihar Zamfara ta fito da sabbin hujjoji na yadda tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi sama da faɗi da kuɗin aikin tashar jirgin sama. A Juma’ar da ta gabata ne Matawalle ya musanta zargin sace biliyoyin kuɗi da sunan aikin jirgin saman. A wata takardar manema labarai, wacce mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, babban birnin jihar, ta ce musanta wannan batu ba komi ba ne face rashin kunya da kuma kira wa kai fallasa. Ya ƙara da cewa, idan ma dai ban da Matawalle na ƙoƙarin wawitar da mutane, ya manta…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ba da wa’adin shekaru biyar ga shigo da alkama Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta ba da wa’adin shekaru biyar ga shigo da alkama Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Ministan harkar noma da kiwo na Nijeriya, Abubakar Kyari, ya ba da wa'adin shekaru biyar ga Nijeriya ta daina shigo da alkama daga ƙasar waje. A cewarsa, hakan yana lamushe tanadin kuɗin wajen da Nijeriya ta yi. Kyari ya yi wannan bayani ne ga 'yan jaridu jim kaɗan bayan ya duba ingancin irin shukar alkama a Kano ranar Juma'ar da ta gabata. A cewar sa, ya gamsu da cewa, samar da abu a cikin ƙasa shi ne ƙashin bayan noma. Kuma a cewar sa, gwamnati tana ta ƙoƙari wajen ganin an daina shigo da tsabar alkama…
Read More
Nijeriya ta zama ƙasa ta 4 a jerin ƙasashe 10 mafiya amsar bashi a Bankin Duniya

Nijeriya ta zama ƙasa ta 4 a jerin ƙasashe 10 mafiya amsar bashi a Bankin Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai ƙasar Nijeriya ta taka matsayi na 4 na ƙasashen da suka fi kowa cin bashi a jerin sunayen ƙasashe na IDA na Bankin Duniya (ƙasashe masu yin rance a bankin). A yanzu haka ana bin ƙasar bashin Dalar Amurka biliyan 14.3. Nijeriya ta daɗe a wannan matsayi nata na huɗu a jerin ƙasashe da ke ƙungiyar (IDA) masu rancen. Tun bayan da ta baro matsayi na 5 a Yunin shekarar 2022. Duk da Nijeriya ta kasance mai matsayi na 4, ta tara wa kanta bashin Dalar Amurka biliyan 1.3 a cikin shekara…
Read More
Falasɗinu: Jinin mata da yara na kwarara!

Falasɗinu: Jinin mata da yara na kwarara!

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A gaskiya a ƙa’idar tsarin yaƙi bai dace a tava rayuwar mata da yara da ma tsoffi ba. Hakanan duk wanda ba hari ya kawo ko ya na riƙe da makami da a ke gwabzawa da shi ba, to ƙyale shi a ke yi a yanayin yaƙi. Duniya ko ba ta adalci; amma akwai dokokin da ta ke bi ko ta ke kan su. In da Majalisar Ɗinkin Duniya na iya tsawatawa a ji, to haƙiƙa da wasu rayukan da ba su da hannu a faɗa ba su tavu ba. Ya kamata a duba yadda…
Read More
Ƙaruwar cutar mantuwa a Nijeriya

Ƙaruwar cutar mantuwa a Nijeriya

Wani bincike na masana ya nuna cewa ’yan Nijeriya na cikin waɗanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya. Ciwon mantuwa da ake kira ‘dementia’ na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil’adama. Ƙungiyar da ta gudanar da binciken mai suna Alzheimer’s Disease International ta ce, sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba. Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma waɗannan alƙaluma sun fi yawa a ƙasashen Nijeriya da Indiya da kashi 90 cikin…
Read More
Gwamna Abba Yusuf ya taya Sanata Kwankwaso murnar cika shekaru 67

Gwamna Abba Yusuf ya taya Sanata Kwankwaso murnar cika shekaru 67

Daga WAKILINMU Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya taya tsohon Gwamnan Kano, jagoran Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, murnar cikar sa shekaru 67 a duniya. Cikin wata sanarwar mai taken: "Taya Madugu Uban Tafiya Murnar Cika Shekara Sittin da Bakwai", wadda Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a safiyar Asabar, 21 ga Oktoba, Gwamna Abba ya jinjina wa Kwankwaso bisa kishin al'umma, jagoranci nagari da aiki tuƙurun da ya yi fice a kai. "A madadin al'ummar Jihar Kano, Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf…
Read More
Gwamnan Kano ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur’ani a gidan Kwankwaso

Gwamnan Kano ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur’ani a gidan Kwankwaso

Daga WAKILINMU A wani shiri daga cikin shirye-shiryen taya tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso murnar cikar sa shekaru 67, Gwamna Abba Yusuf ya buɗe ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur'ani, wadda aka raɗa wa suna Majidaɗi Institute for Qur'anic Research and Advancement (MIQRA). An sadaukar da cibiyar ne ga mahaifin Kwankwaso, Musa Sale Kwankwaso. Kuma an gina cibiyar a gidan Kwankwaso da ke kan titin Miller Road, Kano. Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar, ya ce, "da ya ke jawabi a wurin buɗe cibiyar, Gwamna Abba ya yaba wa Sanata Rabi'u Kwankwaso dangane…
Read More
Shirin Bunƙasa Ilimi a Kano: Yadda Gwamnatin Abba Gida-gida ta bi gida-gida ta kwashi ɗalibai 1001 zuwa karatu ƙasashen waje

Shirin Bunƙasa Ilimi a Kano: Yadda Gwamnatin Abba Gida-gida ta bi gida-gida ta kwashi ɗalibai 1001 zuwa karatu ƙasashen waje

Daga WAKILINMU A ƙoƙarin ta ta ɗabbaƙa darajar ilmi, Gwamnatin Jihar Kano ta zaɓi ɗalibai 1001 da ta fara ɗaukar nauyin karatun na digiri na biyu a ƙasashen waje. Premium Times Hausa ta ruwaito cewa, yayin da wasu za su yi na su karatun a Indiya, wasu kuma a Uganda za su yi na su kwasa-kwasan daban-daban. Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya rage kuɗin rajistar shiga jami'a da na zangon karatu da kashi 50 bisa 100 a kwanan baya, ya ƙaddamar da Shirin Bada Tallafin Karatu Ƙasashen Waje, wanda aka fara ranar Alhamis da jigilar ɗalibai 550 daga Kano.…
Read More
An cafke wasu shugabannin makaranta kan zargin  kashe ɗalibi ta hanyar lakaɗa masa duka a Kaduna

An cafke wasu shugabannin makaranta kan zargin kashe ɗalibi ta hanyar lakaɗa masa duka a Kaduna

Hukuma ta tsare shugaban makaranta da mataimakinsa na makarantar Al-Azhar da ke Zaria a Jihar Kaduna bisa zargin kashe wani ɗalibin makarantar mai suna Marwanu Nuhu Sambo ta hanyar lakaɗa masa duka. Ana zargin su biyun da hannu a horo mai tsanani da aka ce sun bai wa ɗalibin ɗan ajin JSS3 wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa a ranar Juma'a, 20 ga Oktoban, 2023. Bayanai sun ce marigayin Sambo ya ci duka a hannun shugabannin makarantar da ma wasu shugabannin ɗaliban makarantar saboda rashin zuwa aji. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da…
Read More