Editor

9513 Posts
Ta yaya rashin tsafta ke iya haifar wa mace ciwon sanyi?

Ta yaya rashin tsafta ke iya haifar wa mace ciwon sanyi?

Daga AISHA ASAS Tun a farkon darasin idan ba a manta ba, mun kawo a ɗaya daga cikin ma'anonin da ake yi wa ciwon sanyi da cewa, ciwo ne da ke samuwa sakamakon rashin tsaftace al'aura. A wannan satin da yardar mai dukka, za mu yi sharhin waccan ma'ana, wato hanyoyin da rashin tsafta za ta iya haifar da cutar sanyi ga mata. Kusan kodayaushe a na huɗuba ga mata, akan yi kira gare su da su kula da farjinsu, su tsaftace shi, kuma kada su bar wurin da duk wani abu da zai gayyato masu ƙwayoyin cuta. Na san…
Read More
Zan ƙara wa VON ƙaimi – Ndace

Zan ƙara wa VON ƙaimi – Ndace

Sabon Babban Daraktan Muryar Nijeriya (VON), Jubrin Ndace, ya sha alwashin ƙara wa hukumar ƙaimi domin tabbatar da yaɗa sahihan labarai game da Nijeriya da Afirka da ma duniya baki ɗaya. Ndace ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya kama aiki a sabon ofishinsa da ke VON Broadcasting House, Abuja, a ranar Litinin. Sabon Shugaban VON ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa mai barin gado, Mr. Osita Okechukwu da sauran jami'an hukumar. Ndace ya ce a shirye yake ya ɗaga cigaban hukumar fiye da yadda take a yanzu. Da yake jawabi, Ndace ya ce: “Ina miƙa godiyata ga…
Read More
Zuwa ga iyaye: Abubuwan da ke kawo lalacewar ’ya’ya mata a wannan zamani

Zuwa ga iyaye: Abubuwan da ke kawo lalacewar ’ya’ya mata a wannan zamani

Jama'a, Assalamu Alaikum, barkanmu da wannan lokaci. A cikin wasiƙata ta yau zan zayyana wasu abubuwa guda uku da ke kawo sanadiyyar lalacewar tarbiyyar ’ya’yanmu, musamman ma ’yan mata a wannan zamani. Idan ka ji ko ki ka ji kina aikata ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, kina ko kana amfani da ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, sai ka yi ƙoƙari ka gyara ta hanyar rabuwa da wannan munanan abubuwa. Domin yin hakan shi zai sa ka tsira ko ki tsira daga fazawa halaka, idan kuma ’yarka ko ɗanka yana ko tana amfani da irin waɗannan abubuwa to a yi ƙoƙari…
Read More
Allah Ya yi wa jikar Aminu Ɗantata, Batulu rasuwa a Kano

Allah Ya yi wa jikar Aminu Ɗantata, Batulu rasuwa a Kano

Allah Ya yi wa Batulu Alhassan Baba Ahmad Dantata rasuwa tana da shekara 40. Marigayiyar ɗaya ce daga cikin jikokin hamshaƙin ɗan kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Dantata. Majiya daga ahalin ta ce, Batulu ta rasu ne a Kano bayan fama da rashin lafiya. Marigayiyar ta rasu ta bar mahaifiya, Hajiya Ummul Khair Aminu Dantata, wadda ta kasance 'yar fari Alhaji Aminu Dantata, sai kuma mahaifinta, Alhaji Baba Alhassan Ahmad Dantata. Ana sa ran za a yi mata Jana’iza da misalin ƙarfe 10 na safe a babban masallacin Koki da ke Kano a wannan Talatar.
Read More
Taron Afirika KILAF Award 2023: shirye-shirye sun kankama

Taron Afirika KILAF Award 2023: shirye-shirye sun kankama

DAGA MUKHTAR YAKUBU A daidai lokacin da a ke ci gaba da shirye shiryen bikin Bajekolin finafinai na Afirka 'African Indigenous Language Filims'. Mai taken 'Kano Indigenous Languages Of Africa Film Market & Festival' KILAF AWARD, da aka saba shiryawa duk shekara a garin Kano. A yanzu haka dai an kai ga matakin tantance finafinan da suka shiga gasar domin fitar da waɗanda za su kai matakin matakin cancanta da kuma wadanda ba su kai ba. Alƙalan gasar dai su bakwai ne da suka haɗa da Victor Okhoir, Emmanuel Emascalu, Charlas Okwuowulu, Falakemi Ogungbe, Izu Ojukwu, Charity Torut, da Alwine…
Read More
’Yancin ’yan jarida a gwamnatin Tinubu

’Yancin ’yan jarida a gwamnatin Tinubu

Duk da dai an samu wata ’yar taƙaddama a tsakanin sabuwar gwamnatin Alhaji Asiwaju Chif Bola Ahmed Tinubu a gefe guda yadda tun a karon farko a ka zaɓo fitacce kuma zaƙaƙuri ta fuskar masaniya da aikin kafafen yada labarai. Kuma a kai mai muƙami na minista. Alh Idris Muhammed Malagi zamowar sa minista a ɓangare na labarai da wayar da kan al'umma hakan wata gata ce ga aikin jarida a dukkanin Arewa da ma dukkanin ƙasar mu Nijeriya. Sai dai duk da haka a kula ita gwamnati uwa ga ’yan kasa ta yadda idan mutum ya bi doka ya…
Read More
Da ma yaudarar gwamnati kamfanonin shinkafa suke yi?

Da ma yaudarar gwamnati kamfanonin shinkafa suke yi?

Shekara bakwai kamfanonin shinkafar Abuja su na wahala da mutane kawai a barsu su goga da ’yan kasuwa a samo abinci daga waje farashi ya sauka mayaudara su ji kunya. Baza su iya ciyar da Nijeriya ba a farashi Mai sauki. Duk sune ke raba kuɗi suke saye abinci tun yana gona alhali sun karɓi manyan filaye da sunan za su yi noma sun kasa sun bar mutane a cikin azaba. Ka ɗauki misalin idan Saudiyya suka ce ba za su sayo abinci daga waje ba me zai faru. Dole su wahala to haka muma da gangan suka yi. Idan…
Read More
Janairun baɗi za a fara bai wa ɗalibai bashi a Nijeriya – Tinubu

Janairun baɗi za a fara bai wa ɗalibai bashi a Nijeriya – Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, ya zuwa watan Janairun 2024 shirinsa na bai wa ɗalibai bashi zai kankama. Ya bayyana haka ne sa'ilin da yake jawabi a wajen taron tattalin arziki na ƙasa na 2023 ranar Litinin a Abuja. “Ya zuwa Janairun 2024, sabon shirin bai wa ɗalibai bashi zai fara aiki. Don haka muke cewa babu sauran tafiya yajin aiki a rayuwar 'ya'yanmu kuma ɗalibai a nan gaba," in ji Tinubu. A ranar bikin "June 12" Shugaba Tinubu ya sanya wa ƙudirin bai wa ɗalibai bashi hannu ya zama doka, alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin…
Read More
Jaruma Tonto Dikeh ta sauya sheƙa zuwa APC

Jaruma Tonto Dikeh ta sauya sheƙa zuwa APC

Jaruma a masana'antar Nollywood wadda ta tsunduma harkar siyasa, Tonto Dikeh, ta sauya sheƙa ta koma Jam'iyya mai mulki ta APC. Jarumar ta koma APC ne bayan da ta fice daga Jam'iyyar hamayya ta African Democratic Congress (ADC). Jarumar ta yi takarar mataimakin gwamna ƙarƙashin ADC yayin zaɓen 2023 a Jihar Ribas. A wannan Litinin ɗin ake sa ran Shugabar Matan APC ta Ƙasa, Dr Mary Alile, za ta karɓi Tonto Dikeh a Sakatariyar APC da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na rana. A shekarun baya-bayan nan, an ga yadda jaruman fina-finai na Arewaci da Kudancin Nijeriya suka ba…
Read More
Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar APM kan ƙalubalantar nasarar Tinubu

Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar APM kan ƙalubalantar nasarar Tinubu

Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da Jam'iyyar Allied People’s Movement (APM) ta shigar inda take ƙalubalantar nasarar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen 2023. A ranar Litinin Kotun ta yi watsi da ƙarar bayan da mai ƙarar ta janye ƙarar da ta ɗaukaka. APM ta ɗaukaka ƙarar ne don ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Tun da fari, Jam'iyyar ta AMP ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke wanda hakan ya…
Read More