Zan ƙara wa VON ƙaimi – Ndace

Sabon Babban Daraktan Muryar Nijeriya (VON), Jubrin Ndace, ya sha alwashin ƙara wa hukumar ƙaimi domin tabbatar da yaɗa sahihan labarai game da Nijeriya da Afirka da ma duniya baki ɗaya.

Ndace ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya kama aiki a sabon ofishinsa da ke VON Broadcasting House, Abuja, a ranar Litinin.

Sabon Shugaban VON ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa mai barin gado, Mr. Osita Okechukwu da sauran jami’an hukumar.

Ndace ya ce a shirye yake ya ɗaga cigaban hukumar fiye da yadda take a yanzu.

Da yake jawabi, Ndace ya ce: “Ina miƙa godiyata ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Ministan Labarai, Mohammed Idris bisa cancantata da suka gani na riƙe wannan muƙami.

“Ina matuƙar godiya, kuma na yi alƙawarin ƙwarin gwiwar da suke da shi a kaina ba zai tafi a banza ba.”

Ya ƙara da cewa, ya zo VON ne don yin aiki tukuru domin cimma ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu.

Kazalika, ya sha alwashin kyautata haƙƙin ma’aikatan hukumar domin cimma manufar gwamnati.

Daga bisani, shugaban hukumar mai barin gado, Mr Osita Okechukwu, ya miƙa wa Ndace ragamar aiki a matsayin sabon shugaban hukumar.

Ndace ya zagaya sassan VON bisa rakiyar jami’ai da abokan arziki don gane wa idanunsa sassan da VON ta ƙunsa.

Daga cikin ayyukan VON kamar yadda dokarta ta nuna, sun haɗa da yaɗa labarai har wajen Nijeriya, da yaɗa shirye-shirye don kare martaba da mutuncin Nijeriya da ‘ya’yanta da dsuransu.

VON na da sahalewar yaɗa shirye-shiryenta cikin manyan harsuna da suka haɗa da Hausa da Igbo da Yarabanci da Fulfulde da Ingilishi da Larabci da Farasanci da kuma Kiswahili.