Ta yaya rashin tsafta ke iya haifar wa mace ciwon sanyi?

Daga AISHA ASAS

Tun a farkon darasin idan ba a manta ba, mun kawo a ɗaya daga cikin ma’anonin da ake yi wa ciwon sanyi da cewa, ciwo ne da ke samuwa sakamakon rashin tsaftace al’aura. A wannan satin da yardar mai dukka, za mu yi sharhin waccan ma’ana, wato hanyoyin da rashin tsafta za ta iya haifar da cutar sanyi ga mata.

Kusan kodayaushe a na huɗuba ga mata, akan yi kira gare su da su kula da farjinsu, su tsaftace shi, kuma kada su bar wurin da duk wani abu da zai gayyato masu ƙwayoyin cuta. Na san wasu mata na tambayar dalilin da ya sa aka cika damunsu da wannan nasihar. To ɗaya daga cikin dalilin dai shi ne, kuɓucewa kamuwa da ciwon sanyi.

Abin tambaya a nan, ta yaya za a iya yin ƙazantar da za ta haifar da ciwon sanyi?

Zama da zane mai sanyi: idan ya kasance zanenki ko siket da makamantansu sun jiƙe, kuma sai ki ka bar su a jiki, ki na zama ki na tashi, wannan danshi zai iya isa ga farjinki ya haifar da ciwon sanyi.

Amfani na kamfai ɗaya tsayin lokaci: a darussa da dama mun sha jawo hankalin mata kan amfanin sauya kamfai akai-akai musamman ma idan aka yi gumi, ko ruwan tsarki suka jiƙa wandon. Haka kuma zama da kamfai ɗaya ba a iya haifar da ƙwayoyin cuta da za ta haifi ciwon sanyi ba, ƙazanta ce da za ta zama sanadin warin wurin.

Rashin kula da yadda ake yin tsarki: sau da yawa ka ke ganin mata da suka mallaki hankalin kansu, amma ba su san kyakkyawar hanyar da ake yin tsarki ba. Da yawa ba sa bambance gaba da baya yayin da suke yin tsarki, ma’ana, ba su san illar da ke tattare da wanke baya kafin wanke gaba. Ko ba su damu da ganin yayin da suke wanke baya ruwan ba sa gangarowa su dawo gaba ba, wanda hakan kawai zai iya haifar da ciwon sanyi.

Rashin kula a lokaci al’ada: jinin al’ada jini ne da ke wanke tarkace a jikin mace, sai dai a rashin kula yakan iya zama silar samuwar ciwon sanyi. Ta yaha? A lokacin da ki ke yin jinin, ba lokacin da ki ka fi buƙatar tsafta kamar lokacin, ba wai don kawai gudun ƙarni ba, har da kare kai daga kamuwa da cutar sanyi. Hakan zai iya yiwa ne, yayin da ki ke barin ƙyalen ba tsafta ko ki ke barin kaɗa ko ƙyale ya jima ba ki sauya ba.