Editor

9513 Posts
‘Yan bindiga sun kashe mutum tara tare da yin awon gaba da wasu da dama a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutum tara tare da yin awon gaba da wasu da dama a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu mahara ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun hallaka mutum tara, gami da yin garkuwa da wasu mutane da dama a ƙaramar hukumar Ɗan Musa da ke jihar Katsina. Wani mazaunin garin da aka sakaya sunansa, ya bayyana wa MANHAJA cewa maharan waɗanda ba zai iya ƙiyasta yawansu ba, sun afka wa garin cikin daren ranar Lahadi da misalin ƙarfe 8:00 na dare. A cikin mutane tara da suka rasa rayukansu sakamakon harin, har da ɗan sanda da kuma tsohon kantoma na ƙaramar hukumar, wato Hon. Dauda Lawal Mai…
Read More
Tarihin Gobir da yadda Gobirawa suka riski Ƙasar Hausa

Tarihin Gobir da yadda Gobirawa suka riski Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙasar Gobir na ɗaya daga cikin ƙasashen Hausa na ainii, an ce ita ɗin tsohuwar daula ce kuma wata babbar ƙasa ce da ta yi iyaka da Agades daga arewa, ta yi iyaka da Zamfara daga Kudu, ta yi iyaka da Mayali daga Gabas, sannan kuma daga yamma ta yi iyaka da Konni. Amma magana anan ita ce, asalinsu ba hausawa bane tunda wasu na cewa asali wai daga gabas ta tsakiya suka fito musamman ma Misira, inda ake da yaƙinin cewa Sarakuna ukku daga cikin sarakunan Misira gobirawa ne. Sarkin Gobir Mai Martaba Alhaji Abdulhamid…
Read More
Wazirin Fika ya riga mu gidan gaskiya

Wazirin Fika ya riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa Wazirin Fika kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Adamu Fika, rasuwa. Sanarwar rasuwar ta fito ne daga bakin Ɗanburan Fika, Alhaji Idris Adamu Kukuri, kamar yadda ya shaida wa majiyarmu ta waya. Ya ce za a sanar da yadda jana'izarsa za ta kasance bayan an tattauna da Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali. Majiya ta kusa da marigayin ta ce, marigayin ya rasu ne a cikin daren da ya gabata inda ya bar duniya yana da shekara 90. Wani na kusa da ahalin marigayin, Hassan Gimba Ahmed, ya ce, “Ya rasu ne a hanyar…
Read More
Kada ku ƙyamaci masu roƙon ku taimaka musu

Kada ku ƙyamaci masu roƙon ku taimaka musu

Tare da ABBA ABUBAKAR Halin ƙuncin rayuwa da yunwa da ake fama da shi a wannan lokaci na koma bayan tattalin arziki da talauci a ƙasa, ya jefa iyalai da magidanta da dama cikin wani mawuyacin rayuwa. Samun damar cin abinci sau uku ko sau biyu a wuni ya fara zama tarihi a wajen wasu. Magidanta da dama sun zama maroƙan ƙarfi da yaji, tun mutum na jin nauyin ya yi roqo, har ya fara zama masa jiki, don dai neman abin da zai ciyar da iyali, ko da kuwa shi zai haƙura ya kwana da yunwa. Muna sane da…
Read More
Gwamnati ta jaddada ƙudirinta na bai wa fannin tsaro cikakken goyon baya

Gwamnati ta jaddada ƙudirinta na bai wa fannin tsaro cikakken goyon baya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Nijeriya ta jaddada ƙudirinta na bai wa sojojin ƙasar cikakken goyon baya don ci gaba da kare ƙasa da 'yan ƙasa. Hakan ya fito ne daga bakin Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, sa'ilin da ya ziyarci Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, a Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja. Da yake jawabi yayin ziyarar, Ministan ya yaba wa sojojin Nijeriya dangane da nasarorin da suke samu a fagen yaƙi da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta. Ya ce, sojoji na yin bakin ƙoƙarinsu wajen kare ƙasa ba tare da bayyana irin nasarorin da suke samu ba. Abubakar…
Read More
’Yan sanda sun damƙe lauyan bogi da ya yi nasara a shari’o’i 26 a kotu

’Yan sanda sun damƙe lauyan bogi da ya yi nasara a shari’o’i 26 a kotu

Brian Mwenda, lauyan bogi wanda ya yi nasara a shari’o’i 26 yayin da yake bayyana a matsayin Lauyan Babbar Kotun Kenya ya shiga hannun ’yan sanda. Ƙungiyar Lauyoyi ta Kenya, Nairobi Reshen Rapid Action Team (RAT) ta kama Mwenda kuma ta tsare shi bayan wani abin mamaki da ya fallasa shaidar sa na bogi. Mwenda, wanda da yaudara ya bayyana kansa a matsayin “Mai ba da shawara na Babban Kotun Kenya,” ya sami damar yin aiki da doka na tsawon lokaci, yana shiga cikin shari’o’i daban-daban a faɗin ƙasar. Ba a gano yadda ya yi bajinta ba har sai da…
Read More
Shugaban INEC ya gana da jam’iyyun siyasa gabanin zaɓen gwamnoni a jihohin Kogi, Bayelsa, Imo

Shugaban INEC ya gana da jam’iyyun siyasa gabanin zaɓen gwamnoni a jihohin Kogi, Bayelsa, Imo

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya gana da shugabannin jam'iyyun siyasa a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata. Taron ɓangare na shirye-shiryen da INEC ke yi don gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa da kuma Imo nan gaba kaɗan. Ana sa sa ran shugaban INEC ya yi wa jam'iyyun bayanin shirye-shiryen INEC kan zaɓuɓɓukan da kuma rawar da Jam'iyyun za su taka. Kazalika, taron wata dama ce ga jam'yyun da lamarin ya shafa su bayyana wa shugban INEC damuwarsu da sauran lamurran da suka yi la'akari da su gabanin zaɓen.
Read More
Ranar MƊD ta Duniya: Babban Jami’in MƊD a Nijeriya, Matthias Schmale ya yi wa ƙasar saƙo mai ratsa jiki

Ranar MƊD ta Duniya: Babban Jami’in MƊD a Nijeriya, Matthias Schmale ya yi wa ƙasar saƙo mai ratsa jiki

Babban Jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, ya gabatar da jawabi mai ratsa jiki domin bikin ranar Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ake gudanarwa kowace shekara don tunawa da muhimmiyar ranar da Yarjejeniyar Kafa Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara aiki a ranar 24 ga Oktoba,1945. A jawabin nasa, babban jami’in ya yi tsokaci a kan ƙa'idoji da ayyukan MƊD da kuma ƙalubalen da duniya ke fuskanta a yau. Mr. Schmale ya fara ne da taɓo batun yadda aka buɗe taron Yarjejeniyar Kafa MƊD, wanda ya jaddada cewa babban ƙudirin kafa hukumar shi ne "ceto al'ummar duniya daga bala'in…
Read More
Na jima Ina kallon harkar fim a matsayin sana’a mai kyau – Habiba Ɗorayi

Na jima Ina kallon harkar fim a matsayin sana’a mai kyau – Habiba Ɗorayi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Habiba Isa Dorayi da aka fi sani da Habiba Dorayi matashiya ce da ta taso a masanaantar fim ta Kannywood. A tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu, a Kano, za ku ji cikakken tarihinta da kuma yadda frodusoshi suke ribibin saka ta a fim, ku biyo mu: MANHAJ: Za mu so ki gabatar mana da kanki? HABIBA ƊORAYI: Sunana Habiba Isah, an fi sani na da Habiba Dorayi. Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinki? An haife ni a Rano. Da kakanina suka rasu sai muka dawo cikin garin Kano. Na yi Primary, na yi secondry,…
Read More
Wa ke da alhaki a auri-saki a ƙasar Hausa? (2)

Wa ke da alhaki a auri-saki a ƙasar Hausa? (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a filinku na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu zo muku da ci gaba a kan maganar ne da muka fara a makon da ya gabata, wato matsalar auri-saki a ƙasar Hausa. A makon da ya gabata mun ɗauko bayani a kan dalilan da suke sa auri-saki a ƙasar Hausa. Yanzu za mu igaba daga inda aka tsaya. Rashin dace/bauɗaɗɗen hali: Akwai wasu mazan masu bauɗaɗɗen hali waɗanda ba kowaccce mace ce za ta iya jure ta zauna da irin…
Read More