Editor

9513 Posts
Marubuta a dinga bincike kafin rubutu – Gimbiya Rahma

Marubuta a dinga bincike kafin rubutu – Gimbiya Rahma

"Tun Ina firamare na fara rubutu" Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Sanannen abu ne, rubutun adabi ya ta shi daga hannun masu buga littafai zuwa yanar gizo, wanda hakan ne ya ba wa matasa damar baje basirarsu ba tare da tunanin fara neman kuɗin buga littafi ba. Ta dalilin hakan ya sa ake samun marubuta da yawa masu rubutu kuma mai ma'ana, hakan ya tabbatar da cewa, matasan marubuta na matuƙar ƙoƙari wurin samar da labarai da za su ƙayatar da masu karatu. Duk da cewa, an yi ammana rubutun intanet ba karɓe wa marubuta kasuwa ya yi ba, samar…
Read More
Gwamnatin Tinubu za ta ba da fifiko wajen amfani da na’urorin zamani a gidajen rediyo da talabijin – Minista

Gwamnatin Tinubu za ta ba da fifiko wajen amfani da na’urorin zamani a gidajen rediyo da talabijin – Minista

Daga WAKILINMU Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa amfani da kayan aiki na zamani a gidajen rediyo da talbijin na da muhimmanci ga gwamnatin Bola Tinubu. Haka kuma ya jaddada alwashin gwamnati na bai wa harkokin bunƙasa kayan aikin rediyo, talbijin da shirya finafinai goyon baya saboda muhimmancin su ga bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Ya ce su na a sahun gaba wajen samun nasarar inganta tattalin arziki a ƙarƙashin ajandar Farfaɗo da Martabar Nijeriya ta 'Hope Agenda' da gwamnatin Tinubu ta himmatu a kai. Da ya ke jawabi wurin taron AFRICAST na 13…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa kotun ta neman kotu ta ba shi damar gabatar mata da sabuwar hujja a kan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu. Atiku ya buƙaci kotun da ta ba shi damar gabatar da bayanan da ya ce ya samo game da karatun da Tinubu ya ce ya yi a Jami'ar Jihar Chicago ta ƙasar Amurka. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar na ra'ayin cewa bayanan bogi ne Tinubu ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a…
Read More
Burina shi ne kada na yi tarayya da ƙanena wurin dogaro da iyayenmu – Aisha Tanabiu

Burina shi ne kada na yi tarayya da ƙanena wurin dogaro da iyayenmu – Aisha Tanabiu

"Ina da burin samun mijin da zai bar ni na nemi na kaina" Daga AISHA ASAS  Neman na kai bai zama lallai sai ga macen da ta yi aure har ta haifafa ba, kamar yadda a shekarun baya a Ƙasar Hausa an fi ba wa sana'ar matar aure mai 'ya'ya muhimmanci fiye da ta matashiya mai shirin yin auren. Wataƙila hakan bai rasa nasaba da cewar, ita mai auren ta fi mallakar hankalinta, kuma ita ce ke da 'ya'ya da za ta nema don su amfana. Yayin da wasu ke ganin macen da ba ta yi aure ba ba ta…
Read More
UNESCO ta yi bikin ‘Ranar Amfani Da Kafofin Watsa Labarai Da Yaɗa Bayanai Ta Duniya’ a Abuja

UNESCO ta yi bikin ‘Ranar Amfani Da Kafofin Watsa Labarai Da Yaɗa Bayanai Ta Duniya’ a Abuja

Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta ce a shekarar 2023, kashi 60% na al'ummar duniya mai jimlar mutane biliyan 4.75, sun rungumi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana abubuwan da suka shafe su da neman amsoshin tambayoyi da sauran mu’amala. Ms. Audrey, wanda Darakta na Hukumar UNESCO ta Nijeriya, Mista Diallo Abdourahamane, ya wakilta, ta bayyana hakan a yayin bikin Ranar Amfani da Kafofin Yada Labarai da Yaɗa Bayanai ta bana, ranar Laraba, a Abuja. Ta yi bayani a kan alfanun hanyoyin sadarwa na zamani da kuma ƙalubalen da suke…
Read More
Kotun Ƙoli: Gobe su Atiku za su san matsayinsu

Kotun Ƙoli: Gobe su Atiku za su san matsayinsu

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis ta wannan makon Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan ƙarar da 'yan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyyun PDP da LP, Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu wadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar masa da ita. Daraktan Yaɗa Labarai na Kotun Ƙoli, Dr Awemeri Festus Akande, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba. Ya ce an ɗauki matakan tsaron da suka kamata domin tabbatar da lumana a ciki da wajen kotun. Baya ga rashin gamsuwa da nasarar Tinubu, Atiku yana kuma neman…
Read More
Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin INEC na jihohi guda tara

Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin INEC na jihohi guda tara

Daga BASHIR ISAH Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin kwashinonin zaɓe na jihohi (RECs) guda tara ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na wa'adin shekara biyar. Tinubu ya naɗa kwamishinonin zaɓen ne kafin daga bisani Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nasu. Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce Tinubu ya yi naɗin ne bisa damar da Sashe na 154 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima, da Sashe na 6 na Dokar Zaɓe ta 2022…
Read More
Mun fita daga hannun ‘yan sari, mun faɗa hannun ‘yan sane

Mun fita daga hannun ‘yan sari, mun faɗa hannun ‘yan sane

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA  A kwanakin baya ne dai shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaɗa ƙararrawa a cibiyar kasuwar NASDAQ, wato kasuwar zuba hannun jari "Stockbroking" ma fi girma a duniya. Bola Tinubu shi ne shugaban ƙasa na Afrika na biyu  da ya sake samun wannan dama da buga ƙararrawar NASDAQ. Ita wannan kasuwar tana birnin New York a ƙasar Amurka, masu hada-hadar kuɗi da cinikayya da kasuwanci suna dogaro da ita a kullum wajen lissafe-lissafe na tattalin arziki a faɗin ƙasashen duniya. Na saurari jawaban Bola Tinubu a gurin buga ƙararrawar, sai na ji shi yana bayanin  an…
Read More
Shafi-mu-lera: Ya abin yake a kimiyyance?

Shafi-mu-lera: Ya abin yake a kimiyyance?

Daga ABDULAZIZ TIJJANI BAƘO (MBBS, MPH, PhD) An shafe shekaru ana azabtar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba bisa zargin cewa sun sace wa wani 'ya'yan maraina ko al'aurar wani namiji ta hanyar siddabaru ko tsafi. A kan irin wannan zargi maras tushe an kashe mutane masu yawa, an kuma jikkata mutane da dama. Tarihi ya nuna cewa, wannan dabi'ar an fara ta ne a Nijeriya a shekarun 1970s sannan ta yaɗu a kusan dukkanin sassan ƙasashen Afirka. A garuruwan Asiya akwai kwatankwacin irin wannan ɗabi'ar wacce su ke kira 'Koro,' duk da cewa lokaci…
Read More