Tarihin Gobir da yadda Gobirawa suka riski Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙasar Gobir na ɗaya daga cikin ƙasashen Hausa na ainii, an ce ita ɗin tsohuwar daula ce kuma wata babbar ƙasa ce da ta yi iyaka da Agades daga arewa, ta yi iyaka da Zamfara daga Kudu, ta yi iyaka da Mayali daga Gabas, sannan kuma daga yamma ta yi iyaka da Konni.

Amma magana anan ita ce, asalinsu ba hausawa bane tunda wasu na cewa asali wai daga gabas ta tsakiya suka fito musamman ma Misira, inda ake da yaƙinin cewa Sarakuna ukku daga cikin sarakunan Misira gobirawa ne.

Sarkin Gobir Mai Martaba Alhaji Abdulhamid Balarabe Salihu ya tava faɗar asalinsu a wata fira da jaridar ‘Daily Trust’ ta yi dashi, inda yake cewa, gobirawa sun zo ne daga Misira (egypt). Har ya ce, su jikokin Annabi Nuhu (A.S) ne kuma sun bar misira saboda wahalar mulki na sarakunan lokacin ne. Shine suka sauka a wani wuri mai suna Gubur. Gaga nan ne suka samo sunan Gobir.

Ya ci gaba da cewa, daga baya sun isa Yemen, sun yi yaƙi sosai a ƙasar saboda su suna da jinin yaƙi da jarumta. Daga nan kuma sai suka isa ƙasar libya, a haka suna matsawa har suka zo wani gari mai suna Azbin inda yanzu mutanen Taureg suka mamaye.

Da suka bar Azbin sai suka shiga sahara, har suka kafa wani gari mai suna Magali, daga baya sai suka bar garin izuwa wani mai suna Surukul, inda dukkansu yanzu suna jamhuriyar Nijar ne. A hankali suka riski birnin lalle da gwararramu a ƙarni na 15 zuwa na 16. A lokacin kuwa, Sarkin zamfara Abarshi ke mulki wanda yake da zama a Katanga, kuma an samu har ya auri ɗiyar sarkin Gobir mai suna Fara, wacce ta haifi Sarkin gobir Ibrahim Babari.

Kafin Babari ya zamo sarki, sai da ya yi faɗa da Sarkin Zamfara na lokacin kuma ya ci ƙarfinsa. Akan haka sarkin Zamfara ya ƙuduri niyyar halaka shi, amma sai yayarsa ta maido dashi ƙasar mahaifiyarsu watau Gobir, a haka kuma har ya zama sarki, Watau ya yi gado ta wajen Uwa.

Babari ya roƙi Sarkin gobir ya bashi wuri a yankin Zamfara inda zai zauna, amma sai aka gargaɗi sarkin Zamfara da cewa kul ya baiwa Babari gurin zama domin nan gaba zai iya mamaye zamfara dukkan ta, ai kuwa daga bisani hakan ne ya faru, da yaƙi ya varke a wajajen qarni na 16 zuwa na 17, sai da Gobirawa suka cinye har Alkalawa da yaƙi, abinda ke nufin inda suke zaune a yau asali ƙasar zamfara ce.

Sarkin Gobir Abdulhamid ya qara da cewa, “a lokacin Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo (Ƙarni na 17), an ce an ruwaito cewa, Ko zakaru basa cara saboda qarfin tsafinsa, kuma aduk yaƙe-yaƙen da suke yi, gobirawa basu tava miqa wuya ba. Ance sunfi gwammacewa a kashe su akan su miƙa wuya, shi yasa ake musu kirari da ‘Gobir gidan faɗa’.”

Sarkin ya ce, “Bawa jan Gwarzo bai tava yaƙi da Shehu Usmanu ba a zamanin jihadi, maganar gaskiya ma ita ce shehu ya koyar da ‘ya’yan Bawa, ciki harda Yunfa, Atiku, Bello da Mayaki. An ce ma saida shehu ya yi musu nasiha da kada su bari a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin su.”

Sarkin ya ce, “Mutanen da ke kusa da Bawa sune suka haɗa ƙiyayya a tsakanin su, wanda ya yi silar shehu yabar Alkalawa, daga baya kuma ya ci gaba da jihadi a sassan sokoto.

Don gane da tsagun Gobirawa, Sarkin ya ce, asali ba su da tsagu a fuska, amma saboda da yaƙe-yaƙe ne ya sa suka rinƙa tashi daga nan zuwa can, don haka suka ɓullo da tsagu domin su rinƙa shaida junansu.