Editor

9513 Posts
Gwamnatin ramuwa?

Gwamnatin ramuwa?

Daga ALIYU ƊAHIRU ALIYU Bakiɗayan mulkin Abdullahi Umar Ganduje daga 2019 zuwa 2023 na ramuwar gayya ya yi. Kuma shi a kan mutanen Kano ma bakiɗaya ya yi shi saboda ya san ba su zaɓe shi ba aka yi masa fashin zaɓe. Don haka, duk wanda ya ce a tsaya a ba wa wanda ya ci zaɓe zaɓensa, sai da ya yi masa rashin mutunci. Da Sanusi Lamiɗo Sunusi da Mallam Abduljabbar duka abin da suka faɗa kenan amma Ganduje ya ɗaure ɗaya da sharri ya kuma yi wa ɗayan korar wulakanci ta yadda 'yancinsa ma na yawo sai a…
Read More
Rusa badalar Kano da sake gina ta

Rusa badalar Kano da sake gina ta

Daga SAIFULLAHI YUSUF INDABAWA Shekara 39 aka yi ana gina Badalar Kano daga 1095 zuwa 1134 domin samar da tsaro daga mahara. Badalar tana da tsawon ƙafa hamsin (50), da faɗin ƙafa arba'in (40) da zagayen (nisa) ƙafa dubu arba'in da biyar da ɗari tara da talatin da biyu (45932). Idan ka lissafa tana Ariya Mai girman miliyan arba'in da biyu da dubu ɗari shida da ashirin da huɗu da ɗari takwas da tamanin da shida (42,624,896). Badalar tana da ƙofofi guda goma sha biyar (15) kamar Ƙofar Nassarawa, Sabuwar Ƙofa, Ƙofar Ɗan'agundi, Ƙofar Na'isa, Ƙofar Gadon Ƙaya, Ƙofar Famfo,…
Read More
Su waye mayaudaran maza?

Su waye mayaudaran maza?

Daga AMINA YUSUF ALI Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinku na zamantakewa a jaridarmu mai farin jini ta Manhaja. Fatan an yi shagulgulan babbar sallah lafiya. Allah ya maimaita mana. Kamar yadda kuka gani a take, kira ne ga 'yammata da zawarawa a kan su guje wa wasu nau'in samari da ake kira da samarin shaho. Na san mai karatu zai shiga kogin tunani a kan su waye samarin shaho kuma? Samarin shaho ba wasu ne ba face samarin da za su zo wajen budurwa ba da niyyar aurenta ba sai don su rage lokaci,…
Read More
Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa

Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa

Daga SADIQ TUKUR GWARZO Cikakken sunan sa shi ne Muhammadu Rumfa ɗan Yaƙubi, sunan mahaifiyarsa Faɗimatu, ance ita mutuniyar ƙasar Rano ce. Muhammadu Rumfa nagartaccen mutum ne, adali, malami, wanda ba za a samu wani tamkarsa ba a cikin sha'anin mulkin Kano. Akwai zantuka game da yadda aka sanya masa suna RUMFA. Zance na farko na cewa saboda a saman Rumfa ake ajiye masa abinci sa'ar da ya zama sarki wai saboda dabbobi na zagayawa su lalata kafin ya baro fada. Na biyu kuma mafi inganci shine bisa kasancewarsa Rumfa majinginar 'yanuwansa da sauran al'umma, watau mai taimako da shiga…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda huɗu a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda huɗu a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu ‘yan bindiga sun yi wa ‘yan sanda huɗu kwanton-ɓauna a hanyar Gusau zuwa Bunguɗu a Jihar Zamfara. ‘Yan sandan na aiki ne a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a lokacin da aka kai musu hari a daren ranar Litinin a jihar. Wani shaida a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, an kashe huɗu daga cikin ‘yan sandan yayin harin “’Yan bindiga da ke da yawan gaske sun kashe ‘yan sanda huɗu a Bunguɗu a daren jiya; sun yi wa ‘yan sandan kwanton-ɓauna ne a hanyar Gusau Bungudu kusa da…
Read More
Gwamnan Kano ya naɗa Sheikh Daurawa a matsayin Shugaban Hisba

Gwamnan Kano ya naɗa Sheikh Daurawa a matsayin Shugaban Hisba

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan muƙamin shugabancin hukumar Hisbah ta jihar Kano. Tuni aka miƙa wa Malam Daurawa takardar kama aiki a hukumar ofishin Sakataren Gwamnatin jihar. A watan Mayun 2019 ne Sheikh Daurawa, tare da wasu jami'an hukumar ta Hisba a wancan lokaci suka ajiye muƙamansu. Duk da dai babu cikakken bayani kan dalilin ajiye aikin nasa a wancan lokaci, an yi amannar cewa hakan ya faru ne sanadiyyar rashin jituwa da ke tsakaninsa da tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje. Sheikh Daurawa ya…
Read More
Cutar mashaƙo ta kashe yara da dama a Yobe

Cutar mashaƙo ta kashe yara da dama a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Wasu majiyoyi a Potiskum ta jihar Yobe sun bayyana cewa ana kyautata zaton ɓullar sabuwar cutar mashaƙo a garin inda a halin yanzu an samu mutuwar yara da dama yayin da aka kwantar da wasu a cibiyoyin killace majinyata a sibitin garin. Dr. Umar Chiroma, shi ne muƙaddashin babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Yobe, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Lokacin da muka samu rahoton ɓullar cutar a garin Potiskum a ƙarshen mako, nan take muka haɗa tawaga zuwa wuraren da abin ya shafa don wayar da kan jama'a tare da…
Read More
Fitattun mawaƙan Nijeriya da suka taɓa zaman gidan kaso

Fitattun mawaƙan Nijeriya da suka taɓa zaman gidan kaso

Daga AISHA ASAS Sau da dama shahara kan ruɗi wasu daga cikin masu tare da ita, har su fara tunanin za su aikata kowanne irin laifi su sha. Sukan ruɗu da cewa, ƙasarsu cike ta ke da masoyansu wanda za su iya samun alfarma ta kowanne ɓangare. Da wannan ne suke ganin taka doka bai zama wani babban lamari a wurin su ba. Wasu kuwa ba wannan tunanin ne ke aika su ƙa saɓa wa doka ba, giyar ɗaukaka ce da suka ɗirka ta bugar da su, ta hana su tunanin makomarsu yayin da suka hasala hukuma. Don haka sai…
Read More
Akpabio ya naɗa Wadada da Adeola shugabancin kwamitocin majalisa

Akpabio ya naɗa Wadada da Adeola shugabancin kwamitocin majalisa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da kafa wasu kwamitoci a majalisar don gudanar da harkokin gwamnati. Kwamitocin sun haɗa da na Kwamitin Kasafi, Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati da Kwamitin Ɗa'a da Ƙorafe-ƙorafe. Da yake jawabi yayin zaman majalisar a ranar Talata, Akpabio ya bayyana Sanata Solomon Adeola a matsayin Shugaban Kwamitin Kasafi, yayin da Sanata Ahmed Wadada zai jagoranci Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati. A hannu guda, Shugaban Majalisar ya karanto wa zauren wasiƙar da Shugaba Bola Tinubu ya tura wa majalisar ta neman tabbatar da shugabannin tsaron da ya naɗa kwannan nan. Apkabio…
Read More
Zan ƙara ƙoƙarin kawo cigaban kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas – Turakin Ƙofa

Zan ƙara ƙoƙarin kawo cigaban kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas – Turakin Ƙofa

Daga DAUDA USMAN a Legas Babban Shugaban kulawa da cigaban kasuwancin ɓangaren citta da tafarnuwa a kasuwar Mile12 da ke cikin birnin Jihar Legas, Alhaji Yusif Daud Ƙofa kuma Turakin Ƙofa ta Jihar Kano ya bayyana cewa, zai ƙara ƙoƙari wajen kawo cigaban kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas da kewayanta gaba ɗaya. Turakin Ƙofa ya yi wannan tsokaci ne jim kaɗan bayan kammala taron ƙaddamar da su a matsayin shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta mile12 waɗanda za su cigaba da jagorantar ɓangarorin kasuwancin kasuwar ta mile12 a makon da ya gabata. Shuwagabannin ɓangarorin da kasuwar ta ƙaddamar akwai shi kansa…
Read More