Daga SADIQ TUKUR GWARZO
Cikakken sunan sa shi ne Muhammadu Rumfa ɗan Yaƙubi, sunan mahaifiyarsa Faɗimatu, ance ita mutuniyar ƙasar Rano ce.
Muhammadu Rumfa nagartaccen mutum ne, adali, malami, wanda ba za a samu wani tamkarsa ba a cikin sha’anin mulkin Kano.
Akwai zantuka game da yadda aka sanya masa suna RUMFA.
Zance na farko na cewa saboda a saman Rumfa ake ajiye masa abinci sa’ar da ya zama sarki wai saboda dabbobi na zagayawa su lalata kafin ya baro fada.
Na biyu kuma mafi inganci shine bisa kasancewarsa Rumfa majinginar ‘yanuwansa da sauran al’umma, watau mai taimako da shiga lamuran al’ummarsa.
Ya mulki Kano daga wuraren 1463 zuwa 1499, watau a ƙarni na goma sha biyar.
A cikin zamaninsa sharifai suka zo Kano, watau su Muhammad Abdulkarim Al Maghili ko Abdurrahmani tare da jama’arsu.
An ce shi Shehu Al Maghili, Annabi Muhammad S.A.W ne yazo masa a cikin barci, ya ce masa “Tashi ka tafi wajan yamma ka ƙarfafa Musulunci”. Da ya tashi daga bacci sai ya ɗebi ƙurar Madina ya zuba a sanho ya zo da ita ƙasar Hausa. Kowane gari ya shiga sai ya ɗebi ƙurarsa ya gauraya ta da ta Madina, sai ya ga ba su haɗu ba, sai ya wuce. Haka ya rinƙa yi har yazo kano, ya ɗebi ƙurarta ya gaurayata, sai yaga ta zamo abu ɗaya, sai yace “Wannan gari shine na gani cikin barcina”
Al Maghili ya zauna a wani gari da ake kira Panisau, wanda yake daf da kano, sannan ya aikewa sarkin Kano Muhammadu Rumfa buƙatarsa ta shiga birni.
Sarki Rumfa ya tafi izuwa gareshi tare da jama’arsa irinsu Hantari, da Gemun dodo, da Gadangami, da Alfagi, da sauransu, ya taho dashi cikin birnin kano.
Al-Maghili ya zauna a kano ya ƙarfafa Musulunci cikin wannan gari. Shine yazo da littattafai masu yawa ya umarci Rumfa ya gina masallacin jumua, ya sare itaciyar da ake bautawa a wancan lokacin tare da gina hasumiya a wajen. Da addini ya zauna daram a Kano, sai ya wallafa wani littafi mai suna ‘Taj al-din fi ma yajib ‘ala I-muluk’ wanda zai taimakawa Sarki Rumfa gudanar da sha’anin mulki bisa tafarkin Islama daga nan ya yi ƙaura zuwa Misira tare da barin Na’ibinsa mai suna Sidi Fari a Kano yana cigaba da karatar da mutane addini.
An ce Sarkin Kano Rumfa ya nemi malamai sunyi masa adduoi guda tara waɗanda ana ganin har yau suna da tasiri a Kano.
Daga cikin adduoin; an roƙa masa cewa duk wanda yazo Kano har kuma ya samu arziki a Kano, to ya zauna a Kano ba tare da ya koma garinsu ba
Sannan an roƙa masa cewa duk cikar da garin Kano zai yi kada a sami yunwa.
Wata addu’ar da aka yi masa itace duk wanda ya zo Kano dare ko rana to ya sami abincin da zai ci. Sarkin Kano Rumfa shi ne ya fara abu goma sha biyu a ƙasar Kano.
Shi ne ya gina gidan sarautar kano da har yau ake kiransa da suna GIDAN RUMFA.
Da shekara ta zagayo kuma ya faɗaɗa ganuwar birni tun daga ƙofar dagaci zuwa ƙofar Mata, zuwa ƙofar gyarta-wasa, zuwa ƙofar ƙawaye, zuwa ƙofar Na’isa, zuwa ƙofar kansakali.
Da wata shekarar ta sake zagayowa sai ya tare a sabon gidansa.
Haka kuma shine ya kafa kasuwar kurmi,
Shine ya fara dawakin zage domin yaƙi da Latsina.
Shine ya fara kame, ya sa Darman ya shiga gidajen Indabawa ya kamo kowace budurwa da ya iske. Shine sarki na farko wanda ya mallaki mataye dubu a Kano. Shine ya fara kulle. Shi ne ya fara Tara-Ta-Kano da kakaki da figini da takalmin jimina. Shine farkon wanda yayinsallaar idi a shada-koko
Shine wanda ya fara baiwa Babanni sarauta; na farkinsu Ɗan kusubi, da Ɗan jigawa, da Ɗan turbuna, da sarkin Gabas da sarkin Tudu da sarkun Ruwa da Maaji da sarkin Bai da sarkin ƙofa.
Har gobe ana ambatar duk wanda za a naɗa sarkin kano da suna ‘Magajin Rumfa’.
A zamaninsa ƙasar kano ta yi yaqi da ƙasar Katsina, wanda sai da aka shekara goma sha ɗaya ana fafatawa a tsakaninsu ba tare da ɗaya ta rinjayi ɗaya ba.
Sarki Muhammadu Rumfa ya sarauci Kano tsawon shekaru talatin da bakwai.
Ana masa kirari da ‘Balaraben sarki ya gyara ƙasa!’