Editor

9513 Posts
Kisan Jos: Ɗan Majalisa ya yi kira ga jama’a da su tashi su kare kansu

Kisan Jos: Ɗan Majalisa ya yi kira ga jama’a da su tashi su kare kansu

Ya ce kare kai halas ne a doka Daga BASHIR ISAH Wakilin Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a Majalisar Wakil ta Ƙasa, Hon. Dachung Musa Bagos, ya yi kira ga jama'ar yankinsa da su tashi su kare kansu daga kashe-kashe da haren-haren da ake kai musu. Ɗan majalisar ya ce kare kai abu ne da doka ta yarda da shi. Bagos ya nuna baƙin cikinsa kan sabbin hare-haren da aka kai a yankunan Mangu da Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata, inda aka kashe sama da mutane 20. Daga nan, ɗan siyasar ya…
Read More
A nisanta yara daga hotuna da bidiyon batsa

A nisanta yara daga hotuna da bidiyon batsa

Na san wannan take na yau zai tayar da hankalin wasun mu da dama, musamman malamai, alarammomi da ɗaliban ilimi, da ma uwa uba iyaye. Ba na zavi in yi wannan faɗakarwa kan almajirai ne kaɗai ba, har ma da sauran yaran mu da ke rayuwa a gaban iyayensu. Na san ba ni kaɗai ne wannan al'amari ke damuna ba, lura da yadda ake cigaba da samun taɓarɓarewar tarbiyyar yara ƙanana da ke samun kansu a cikin wata irin gurvatacciyar rayuwa marar tsafta, saboda rashin kulawar iyaye, sa ido daga manya masu kula da tarbiyya, har ma da malamai da…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shekara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarrashe ni, idan na ƙiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi. To da iyaye suka fara zancen ba mu haihu ba, mu…
Read More
Shin motsa jiki na taimako ga matsalar damuwa?

Shin motsa jiki na taimako ga matsalar damuwa?

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al’umma, Manhaja, da fatan ba ku ƙosa da wannan darasi na atisaye ba. A yau da yardar mai dukka za mu taɓo wani ɓangare da kusan zan iya cewa ya fi adabbar mutane, amma rashin sani kan sa ayi masa wata fassarar da ta saɓa wa sananniyar ma’anar sa. Da yawa daga cikin wasu matsaloli da suka dangance ciwo da muke cewa matsala ce ta mutanen ɓoye, ko sammu da jifa, zuwa duk wata damuwa da ta shafi rikeɗewar tunani, takan samu ne ta sanadiyyar damuwa.…
Read More
Ma’aikaciyar Jaridar Blueprint ta lashe lambar yabo ta ‘ReportHer Award’

Ma’aikaciyar Jaridar Blueprint ta lashe lambar yabo ta ‘ReportHer Award’

Daga BASHIR ISAH An karrama ma'aikaciyar Jaridar Blueprint, Ene Oshaba da lambar yabo ta 'ReportHer Award' bayan da ta yi zarra a tsakanin takwarorinta mata 'yan jarida su sama da 100. An karrama Ene ne a matsayin 'yar jaridar da ta yi rubuce-rubucen da mata suka fi amfana da su Tashar Radio 91.7 tare da haɗin gwiwar United Women for ECOWS da cibiyar aikin jarida na bincike ta Wole Soyinka (WSCI) tare da Gwamnatin Kanada ne suka ɗauki nauyin shirin. Shugabar tashar Women Radio, 91.7, Toun Okewale Sonaiya, ta ce an ƙirƙiro shirin ne don amfanin mata da kuma rajin…
Read More
Dimulukiyya: Za a ga sabbin fuskoki a gwamnatin Tinubu?

Dimulukiyya: Za a ga sabbin fuskoki a gwamnatin Tinubu?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Me ma za a ce ne kan dimokraɗiyyar Nijeriya musamman daga dawowa mulkin farar hula a 1999 kan wani canji na masu damawa a sha ko a na so ko ba a so. Kusan canjin a can sama ba yawa sosai don bayan mulkin PDP a 2015 da ta samu shekaru 16 an samu sabon shugaba da bai yi PDP wato Muhammadu Buhari amma sauran muƙarrabansa za ka taras akwai da yawa waɗanda jihohin PDP ne su ka kauro zuwa APC. In sharri PDP ta yi irin waɗannan mutanen na da kason su. Mu ma duba…
Read More
‘Yan wasan Kano Pillars sun fara hutun mako guda bayan nasarar dawowa NPFL

‘Yan wasan Kano Pillars sun fara hutun mako guda bayan nasarar dawowa NPFL

Daga BASHIR ISAH Hukumar kula da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta bai wa 'yan wasan ƙungiyar hutun mako guda bayan da ƙungiyar ta samu nasarar zuwa Gasar Firimiyar Nijeriya. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar, Babangida Umar, ya fitar jim kaɗan bayan kammala wasan ƙarshe na ƙungiyoyi takwas da ake kira da 'super 8' na Gasar Firimiyar Nijeriya wanda ya gudana a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba, Jihar Delta. Umar ya ce shugabannin ƙungiyar ba za su tafi hutu ba har sai sun miƙa rahotonsu na wannan kaka. Shuganan kulob ɗin ya…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta ɗauki malaman S-Power 7,000 aiki

Gwamnatin Katsina za ta ɗauki malaman S-Power 7,000 aiki

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana shirinta na ɗaukar ƙarin malaman makaranta 7,000 a faɗin jihar. Mai magana da yawun Gwamnan Dikko Umar Raɗɗa, Malam Ibrahim Kaula ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar. Ya ce, mataimakin gwamnan jihar, Hon. Faruq Lawal Jove ya sanar da hakan a lokacin da yake ƙaddamar da mambobin kwamitin da za su tantance waɗanda za a ɗauka ɗin a ofishinsa. Mataimakin gwamnan ya ce za a ɗauki malaman makaranta 5,000 dake da shaidar malanta ta ƙasa NCE/Diploma da za su koyar a makarantun firamare da kuma…
Read More
An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

An zaɓi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS). Wannan ya faru ne yayin taron ƙungiyar karo na 63 wanda ya gudana a Guinea Bissau a ranar Lahadi. Wannan ne karo na farko da Tinubu ya halarci taron na ECOWAS tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023. A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya karɓi bakuncin Shugaba Embalo a birnin Legas, inda ya ce sun ci abinci tare kuma “mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu.” A wancan lokacin, Tinubu ya ce…
Read More
Tinubu ya naɗa AbdulAziz AbdulAziz hadiminsa na ɓangaren jaridu

Tinubu ya naɗa AbdulAziz AbdulAziz hadiminsa na ɓangaren jaridu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shahararren ɗan jaridar nan, AbdulAziz AbdulAziz, a matsayin Babban Hadimi na Musamman a ɓangaren jaridu. Abdulaziz ɗan jarida ne da ya ƙware a binciken ƙwa-ƙwaf wanda kuma ya yi shura a soshiyal midiya. Kafin naɗin nasa, shi ne Hadimi na Musamman Kan Sha'anin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Tinubu. A baya, Abdulaziz ya yi aiki tare da kamfanin Media Trust inda ya riƙe muƙamin Mataimakin Babban Edita. Haka nan, ya kasance mai gabatar da shiri a Trust TV mallakar Media Trust.…
Read More