09
Jul
Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'Yan Sanda a Jihar Katsina, ta bayyana cewa ta kama mutane takwas da take zargi bisa ƙona motar jami'anta masu kula da zirga-zirgar ababen hawa a titunan jihar. Lamarin dai ya faru ne a titin Ƙofar Guga ɗaya daga cikin manyan hanyoyi a babban birnin jihar da aka fi samun cinkoson ababen hawa. Rahotanni sun bayyana cewa rikici ya ɓarke tsakanin jami'an rundunar (MTD) da kuma masu ababen hawa dake amfani da hanyar. 'Yan sandan sun yi ƙoƙarin kama wani mai babur da ya karya dokar tuƙi, sai dai wasu mutane dake kan titin…
