08
Jul
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Sanata Rufa'i Sani Hanga ya bayyana cewa masu hamayya akan kujerarsa ta Sanatan Kano ta Tsakiya "in ba su yi hamayya ba, ba su yi halasci ba domin dama abinda ita siyasa ta gada kenan abinda rayuwa ta gada kenan." Ya bayyana haka ne da yake zantawa da 'yan jarida a Kano, inda ya ce ba yadda za ka yi da ɗan hamayya mutum dole ko waye kai dole ka samu maƙiya da masoya, sai dai kullum fata shine masoya su fi maƙiya yawa. Ya ce shi baya jin ciwon hamayya ko abinda ake faɗa…
