07
Jul
Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Esther Amisu, 'yar siyasa ce a jihar Gombe kuma ƙwararriya a ɓangaren sanin harkokin siyasa, ta ce ba shakka matan Gwamnonin Arewa ba su yi zaɓen tumun dare ba na zaɓar Hajiya Asma'u Muhammad Inuwa Yahaya, uwargidan gwamnan Gombe a matsayin jagora. Esther Amisu, ta ce zaɓar Asma'u Inuwa Yahaya da matan gwamnonin suka yi zai ƙara bai wa mata dama na shiga harkokin siyasa domin Asma'u mace ce da a kullum take ƙoƙarin mata sun samu kulawa ta musamman an kuma basu wani kaso mai tsoka a muqaman siyasa. Ta yi wannan batu…
