Editor

9513 Posts
‘Yan bindiga sun sake kashe lauya a Zamfara

‘Yan bindiga sun sake kashe lauya a Zamfara

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun kashe wani lauya mai suna Barista Ahmad Muhammad Abubakar a Jihar Zamfara. Majiyarmu ta ce 'yan bindigar sun bi margayin ne har gidansa da ke garin Kwatarkwashi, cikin Ƙaramar Hukumar Bungudu suka hallaka shi. Kafin rasuwarsa, marigayi Muhammad shi ne sakataren walwala na Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya reshen Gusau. Kazalika, shi ne ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a mazaɓar Bunguɗu ta Yamma ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP a yayin babban zaɓen da ya gabata. Duk da dai Rundunar 'Yan Sandan Zamfara ba ta ce komai kan batun ba, sai dai majiya ta kusa da marigayin…
Read More
Zulum ya ƙaddamar da motoci 80 don jigilar manoma zuwa gona a Borno

Zulum ya ƙaddamar da motoci 80 don jigilar manoma zuwa gona a Borno

Daga BASHIR ISAH A matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ke yi don rage wa talakawansa raɗaɗin cire tallafin mai, Gwamnan ya saki manyan motocin bas-bas guda 80 haɗi da na ɗaukar kaya domin jigilar manona zuwa gona kyauta. A ranar Talata Zulum ya saki motocin don fara aiki kamar yadda aka tsara. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da mayaƙan Boko Haram suka kai hare-hare a yankin Wulari inda suka kashe manoma takwas, da kuma yankin Bulajimban tare yi wa manoma bakwai yankan rago. Yayin da yake duba lafiyar hanyar da…
Read More
APC ta nesanta kanta da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya

APC ta nesanta kanta da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nesanta jam'iyyar da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya kamar yadda shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai suka sanar a ranar Talata. Yayin taro da Kwamitin Gudanawar na Ƙasa na jam'iyyar da ƙungiyar gwamnonin APC a Abuja, Adamu ya ce Majalisar Tarayya ta saɓa ƙa'ida wajen sanar da manyan jami'an da aka naɗa ba tare da sanin jam'iyyar ba kamar yadda tashar AIT ta rawaito. A zaman da majalisun suka yi a ranar Talata aka jiyo Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar…
Read More
An yi naɗe-naɗen manyan muƙamai a Majalisar Tarayya

An yi naɗe-naɗen manyan muƙamai a Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, sun yi naɗe-naɗe na manyan muƙamai a majalisar tarayya. A yayin zaman majalisun a ranar Talata Akpabio da Abbas suka sanar da naɗe-naɗen sabbin manyan muƙaman da aka yi. A Majalisar Dattawa, Akpabio ya ambaci Opeyemi Bamidele a matsayin Shugaban Masu Rinjaye, David Umahi a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye; Mohammed Ali Ndume a matsayin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye, sai Lola Ashiru a matsayin Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu rinjaye. Yayin da a Majalisar Wakilai kuwa, Abbas ya ambaci Julius Ihonvbere daga Edo a…
Read More
An cafke kwamishinan Ganduje da wasu kan zargin rashawar N1bn a Kano

An cafke kwamishinan Ganduje da wasu kan zargin rashawar N1bn a Kano

Daga BASHIR ISAH Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, ta kama tare da tsare Kwamishinan Ayyuka da Samar da Ababen More Rayuwa na tsohuwar gwamnatin Ganduje, Idris Wada Saleh. Majiyarmu ta ce an tsare tsohon kwamishinan ne tare da wasu mutane biyar bisa zargin almundahanar Naira biliyan ɗaya. Majiyar ta ce Babban Sakataren Hukumar Kula da Harkokin Gwamnati, Mustapha Madaki Huguma da Daraktan Kuɗi da na Bincike da Tsare-tsare, na daga cikin waɗanda kamen ya shafa da yammacin Litinin. Ana zargin waɗanda lamarin ya shafa ne da yin kwanciyar kaza kan Naira…
Read More
Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH 'Yan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP da Peter Obi na Jam'iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya gabata, sun yi ca a kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na ƙin yarda da rahoton ƙarshe da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun da ya gabata. A ranar Talata, 27 ga Yuni, EU ta miƙa rahoton nata game da zaɓen a Abuja. Babban jami'in sanya ido, Barry Andrews, ya ce rahoton ya samo asali ne daga nazarin bin ƙa’idojin da Nijeriya ta ɗauka na…
Read More
BIDIYO: Shugabannin tsaro sun ziyarci Tinubu

BIDIYO: Shugabannin tsaro sun ziyarci Tinubu

Daga BASHIR ISAH Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya jagoranci sabbin shugabannin fannin tsaro haɗa da muƙaddashin Sufeto Janar na 'Yan Sanda (IGP), zuwa tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Villa da ke Abuja a ranar Litinin. Mahalarta tattaunawar sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Christopher Musa; Shugaban Rundumar Sojin Ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja; Shugaban Rundumar Mayaƙa Ruwa Rear Admiral Emmanuel Ogalla da sauransu. Idan dai ba a manta ba, makonni biyu da suka gabata ne Shugaba Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin tsaron. Ga wani ɓangare na bidiyon ziyarar:
Read More
Mai yiwuwa tsadar kayayyaki a Nijeriya ya ƙaru da kashi 25 a ƙarshen 2023 – Bankin Duniya

Mai yiwuwa tsadar kayayyaki a Nijeriya ya ƙaru da kashi 25 a ƙarshen 2023 – Bankin Duniya

Daga BASHIR ISAH Bankin Duniya ya yi hasashen cewa bayan cire tallafin mai da aka yi a Nijeriya, mai yiwuwa hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 ya zuwa ƙarshen 2023. A cikin rahoton da ya haɗa game da ci gaban da Nijeriya ta samu na watan Yuni 2023, Bankin ya ce galibi hauhawar farashin zai shafi kayan abinci ne sakamon tsadar kuɗin mota da ake fuskanta tun bayan cire tallafin mai. Bankin ya ce yanzu hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya kai kashi 22.41 wanda hakan ya jefa Nijeriya cikin jerin ƙasashen da suka…
Read More
Tinubu ya yi watsi da rahoton Tarayyar Turai kan zaɓen 2023

Tinubu ya yi watsi da rahoton Tarayyar Turai kan zaɓen 2023

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta yi watsi da rahoton da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan babban zaɓen 2023 da ya bai wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na Jam'iyyar APC damar zama Shugaban Nijeriya. Cikin Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Sahwara Kan Ayyuka na Musamman, Sadarwa da Tsare-tsare, Mr Dele Alake, ya fitar a ranar Lahadi, Fadar ta ce babu gamsassun hujjoji da ƙungiyar ko danginta suka bayar da za su iya ƙalubalantar sahihancin sakamakon babban zaɓen na 2023. A cewar Alake, rahoton Ƙungiyar Tarayyar Turan rahoto ne mara inganci wanda aka shirya shi…
Read More
Hajjin 2023: Nijeriya ta yi rashin alhazai 13 a Saudiyya – NAHCON

Hajjin 2023: Nijeriya ta yi rashin alhazai 13 a Saudiyya – NAHCON

Daga BASHIR ISAH Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya, NAHCON, ta bayyana cewa, aƙalla mutum 13 daga cikin mahajjatan Nijeriya 95,000 da suka halarci Hajjin bana ne suka riga mu gidan gaskiya yayin Hajjin 2023 a Saudiyya. NAHCON ta ce da fari mutum bakwai sun rasu kafin Arfa sannan shida a Arfa. Da yake jawabi a wajen taron bayan kammala Arfa da aka shirya ranar Lahadi a Makka, shugaban tawagar likitocin NAHCON, Dr. Usman Galadima, ya ce mahajjata huɗu suka kwanta dama a Arfa, biyu a Mina, wanda hakan ya sa jimillar alhazan Nijeriya da suka rasu yayin aikin Hajjin ya…
Read More