Editor

9513 Posts
Buhari bai hana Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba – Garba Shehu

Buhari bai hana Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba – Garba Shehu

Daga UMAR GARBA a Katsina Kakakin tsohon Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, bai hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba. Malam Shehu ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya kuma musanta cewa tsohon Shugaban Ƙasar yana katsalandan a binciken da sabuwar gwamnati ke son yi kan jami’an gwamnatin da ta gabata. “Idan za a yarda da abin da aka ce a soshiyal midiya, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yana buƙatar mutumin da ya gaje shi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu kada ya…
Read More
Hajjin 2023: Nijeriya ta buƙaci kamfani ya maido da kuɗin da aka biya shi saboda rashin ingancin aiki

Hajjin 2023: Nijeriya ta buƙaci kamfani ya maido da kuɗin da aka biya shi saboda rashin ingancin aiki

Daga BASHIR ISAH Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya, NAHCON, ta buƙaci kamfanin da ya yi wa mahajjatan Afirka daga ƙasashen da ba Larabawa ba hidima yayin Hajjin bana a Saudiyya, da ya maido da kuɗaɗen da aka biya shi. NAHCON ta buƙaci hakan daga Kamfanin Mutawifs for Pilgrims from Africa Non-Arab Countries ne saboda gazawar kamfanin wajen yi wa alhazan Nijeriya hidima yadda ya kamata a Mina yayin aikin Hajjin 2023. Shugaban NAHCON na ƙasa, Zaikrullah Kunle Hassan, tare da wakilan hukumomin alhazai na jihohi da kamfanonin yawon buɗe ido su ne suka buƙaci hakan bayan da suka nuna rashin…
Read More
Batun farashin fetur zai ƙaru zuwa N700 ba gaskiya ba ne – IPMAN

Batun farashin fetur zai ƙaru zuwa N700 ba gaskiya ba ne – IPMAN

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Dillalan Fetur Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (IPMAN) da ta masu dakon mai, wato ADITOP a taƙaice, sun ƙaryata batun cewa akwai shirin cilla kuɗin fetur zuwa Naira 700 kan lita guda. Sun ƙaryata batun ne a wata zantawa da aka yi da su ranar Asabar a Abuja. Ƙungiyoyin sun ce babu ƙamshin gaskiya cikin rahotannin da aka yaɗa a kan batun ƙarin farashin man. A cewarsu, yanayin kasuwa ke tilasta ƙarin kuɗin fetur, kuma duba da yanayin kasuwar canji a halin yanzu babu buƙatar ƙarin farashin man sai dai hasashe kawai. Wasu 'yan kasuwa sun…
Read More
An kama mutum 2000 kan tada tarzoma a Faransa

An kama mutum 2000 kan tada tarzoma a Faransa

Rahotanni daga ƙasar Faransa sun ce, sama da mutane dubu biyu ne aka kama a Faransa, tun bayan tarzomar da ta biyo bayan kisan da 'yan sanda suka yi wa matashi Nahel. Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Ƙasar ce ta bayyana haka a ranar Lahadi. Zanga-zangar wadda aka shafe kimanin kwana biyar ana gudanar da ita, hukumomin Faransa sun tabbatar da kama mutane 719 a ranar Asabar. Ma’aikatar ta ƙara da cewa ana samun raguwar tarzomar da aka faro tun a ranar Talatar da ta gabata. Ministan Kulada Harkokin Cikin Gida na Faransa, Gerald Darmanin, ya sanar a ranar Asabar…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe fasto a Ogun

‘Yan bindiga sun kashe fasto a Ogun

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun kai hari a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da ke Jihar Ogun inda suka kashe fasto kana suka yi garkuwa da wasu mambobin mujami'ar da ke tsaka da ibada. Majiyarmu ta ce harin ya auku ne a wannan ƙarshen makon a Abule-Ori da ke yankin Ƙaramar Hukumar Obafemi Owode a jihar. Kwamandan rundunar tsaron jihar, Soji Ganzallo, shi ne ya tabbatar da faruwan hakan ga manema labarai da safiyar Lahadi. Kwamandan ya ce jami'ansu sun kuɓutar da mambobin cocin bakwai da aka yi garkuwa da su tare da kashe mutum guda daga…
Read More
Shugaban Guinea-Bissau ya ziyarci Tinubu

Shugaban Guinea-Bissau ya ziyarci Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin takwaransa na ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo, a Legas. Embalo, wanda jigo ne a ƙungiyar ECOWAS, ya ziyarci Tinubun ne a ranar Asabar. Shugaba Tinubu ya yi hutun sallah ne a Legas tun bayan da ya dawo daga London a ranar Talata. Embalo ya zama Shugaban Ƙasa a Afirka na farko da ya ziyarci Tinubu tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin Shugaban Nijeriya na 16 a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Read More
Miyetti Allah ta sanar da ɓacewar Mataimakin Shugaba na Ƙasa, Lamiɗo

Miyetti Allah ta sanar da ɓacewar Mataimakin Shugaba na Ƙasa, Lamiɗo

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya (MACBAN), ta sanar da ɓacewar Mataimakin Shugabanta na Ƙasa, Engr. Munnir Atiku Lamido. Mai magana da yawun ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Muhammad Nura Abdullahi, shi ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a, inda ya ce, “muna sanar da al'umma da ma hukumomin tsaro cewa, Engr. Munnir Atiku Lamiɗo ya ɓace. "Engr. Munnir shi ne Mataimakin Shugaban MACBAN na Ƙasa. “Ya bar gidansa da ke Katsina a ranar Juma'a, 23 ga Yuni, 2023, da nufin zuwa Kaduna, kuma har zuwa yanzu ba a san inda…
Read More
BIDIYO: Fasto ya yanke jiki ya faɗi a filin jirgin sama a Ribas

BIDIYO: Fasto ya yanke jiki ya faɗi a filin jirgin sama a Ribas

Daga BASHIR ISAH Wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafe daban-daban ya nuna yadda mu'assasin cocin Omega Power Ministries (OPM), mai suna Apostle Chibuzor Gift Chinyere, ya yanke jiki ya faɗi ranar Juma'a a filin jirgin saman da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Majiyarmu ta ce wannan na zuwa ne bayan da wanda lamarin ya shafa ya sanar cewa ba ya jin daɗin jikinsa, kuma yana buƙatar addu'a. Bayan faruwar lamarin, daga bisani an ga cocin nasa ya yaɗa wani hoton Faston kan cewa yana asibiti yana ci gaba da karɓar magani. Haka shi ma Fasto ɗin, ya…
Read More
Sharhin littafin ‘GAWA da RAI’

Sharhin littafin ‘GAWA da RAI’

Daga BAMAI A. DABUWA KKM Sunan Littafi: Gawa da Rai.Sunan Marubuci: Yusuf Yahaya Gumel.Shekarar Bugu: 2022.ISBN: Babu.Bugu: AGK Graphics Kurna.Yanayi: Ba A Fayyace ba.Jigo: Soyayya.Salo: Cikin Fage.Mai Sharhi: Bamai A. Dabuwa Kkm.Lambar Wayar Mai Sharhi: 07037852514.Email: [email protected] GABATARWA/TSOKACI. Littafin Gawa da Rai, labari ne na wani matashi (Anas), mai fama da larurar 'Cotard Delusion'. Wata kalar cuta ce, da idan ta kama mutum sai kawai ya gamsu a ransa cewa shi matacce ne ko kuma dai ya rasa wani sashe na jikinsa, alhalin ba hakan ba ne. Tauraron ya kamu da soyayyar wata yarinya (Laila). 'Yar gidan wani hamshaƙin mai…
Read More