Editor

9513 Posts
Ku lura da tarbiyyar ‘ya’yanku, kiran Hajiya Salifat Sule ga iyaye

Ku lura da tarbiyyar ‘ya’yanku, kiran Hajiya Salifat Sule ga iyaye

Daga BASHIR ISAH Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa, Hajiya Salifat Sule, ta jaddada buƙatar da ke akwai iyaye su zamo masu saka ido matuƙa a kan tarbiyyar 'ya'yansu don amfnin al'umma baki ɗaya. Salifat ta yi wannan kira ne a jawabin da ta yi wa alhazan jihar sa'ilin da ta kai musu ziyara ranar Alhamis a Mina a ƙasar Saudiyya. Ta ce, aikin lura da tarbiyyar 'ya'ya bai kamata ya a bar shi a hannun iyaye mata kaɗai ba, don haka ta buƙaci iyaye maza da su kasance masu mara wa matan baya yadda ya kamata a fagen bai wa yara…
Read More
Dakataccen Kwamishinan Zaɓe, Hudu, zai san matsayinsa ba da daɗewa ba – INEC

Dakataccen Kwamishinan Zaɓe, Hudu, zai san matsayinsa ba da daɗewa ba – INEC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa, dakataccen Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, zai san matsayinsa nan ba da daɗewa ba. Kwamishinan INEC na ƙasa, Festus Okoye, shi ne ya sanar da hakan yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar Channels Television ranar Alhamis. Okoye ya ce 'yan sanda sun kammala bincikensu kan batun, kuma INEC tana da tarin hujjoji gamsassu wanda za ta yi amfani da su a kan Yunusa-Ari a gaban shari'a. “Ina sane cewa 'yan sanda sun kammala bincike, haka nan ina sane nan da 'yan makonni za…
Read More
Sai kun zama masu bin doka za ku iya kama masu karya doka, kiran IGP ga ‘yan sanda

Sai kun zama masu bin doka za ku iya kama masu karya doka, kiran IGP ga ‘yan sanda

Daga BASHIR ISAH Muƙaddashin Sufeto Janar na 'Yan Sanda, IGP Olukayode Egbetokun, ya umarci tawagar motocin 'yan sanda da su daina saɓa dokokin amfani da hanya. IGP ya ba da wannan umarni ne yayin ganawar da ya yi da tawagar 'yan sandan kwantar da tarzoma da kwamndojin 'yan sanda ranar Litinin a Babban Ofishin Rundunar 'Yan Sanda da ke Abuja. Egbetokun ya jaddada wa jami'an kan su sani cewa, tabbatar da bin doka da oda, kare rayuka da dukiyoyin jama'a shi ne babban aikinsu. Ya ƙara da cewa wajibi ne 'yan sanda su yi aiki daidai da dokokin aikin ɗan…
Read More
Gwamnati za ta dakatar da ɗaukar nauyin WAEC da sauransu

Gwamnati za ta dakatar da ɗaukar nauyin WAEC da sauransu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana cewa ba za a ci gaba da ware wa hukumomi da majalisun ƙwararru kaso daga asusun gwamnati ba ba kamar yadda aka saba. Gwamnati ta ce wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Janairun 2024. Darakta Janar na Ofishin Kasafi, Ben Akabueze ne ya bayyana haka a cikin wasiƙar da ya aika wa hukumomi da cibiyoyin da lamarin ya shafa. Wasiƙar mai ɗauke da lamba DG/BDT/GEN. CORR/2016/XII/3067 da kwanan wata 26 ga Yuni, 2023, ta nuna cewa an ɗauki wannan mataki ne daidai…
Read More
Dalilai bakwai da suka sa ‘yan Kwankwasiyya suke da wahalar sha’ani

Dalilai bakwai da suka sa ‘yan Kwankwasiyya suke da wahalar sha’ani

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN 1: Duk kyan abu da tsarinsa, in har ba ‘Yan Kwankwasiyya ne suka kawo shi ba, to a wajen galibin ‘yan kwankwasiyya wannan abun mammuna ne, abin ƙyama ne, sannan abun a yi watsi da shi, ko rushe shi ne. Sannan duk wani abu duk muninsa, in har Kwankwasiyya ce ta kawo shi, to a wajensu wannan abu ne mai kyau, abu ne da zai kawo ci gaba ko da kuwa cikin ƙoƙon zuciyarsu sun san ba haka ba ne. 2: A tunanin galibin ‘yan Kwankwasiyya shi ne, duk mai adawar siyasa da su, to maƙiyi…
Read More
A yi duba na tsanaki, daga ina matsalar ƙwacen waya ta samo asali?

A yi duba na tsanaki, daga ina matsalar ƙwacen waya ta samo asali?

Daga BASHIR IBRAHIM NA’IYA Guraren koya sana'o'i mallakin jahar Kano waɗanda Kwankwaso ya gina, da a ce gwamnatin da ta wuce ta dora an ci gaba da koya wa matasa sana'o'i a guraren tsawon shekara 8 din Ganduje da yanzu wata maganar a ke yi ba wannan ba. Domin in kuka kwashe shekaru 8 daga cikin shekarun yaran da ake kamawa da laifin sata ko fashin waya, za ku ga duk ba su wuce shekara 10 ba zuwa 12 ba a wancan lokacin. Kamar yadda wani ya ke gaya min, ya je wuraren koyar da sana'o'in da Kwankwaso ya giggina,…
Read More
Tallafin mai: Tsakanin gaskiya da ƙarya

Tallafin mai: Tsakanin gaskiya da ƙarya

Daga FATUHU MUSTAFA Na lura mutane har yau ba su fahimci gaskiyar abinda ke faruwa game da tallafin mai da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ke baiwa talakawa ba. Ba kuma su fahimci illar da tallafin yake wa al'amuransu na yau da kullum ba. Kamar dai yadda Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya tava faɗa ne, "Mutane sun fi damuwa da illar cire tallafin man fetur, fiye da illar barin sa". In har tallafin mai yana da wani alfanu ga talakan Nijeriya, to bai wuce na sauƙaƙa tsadar man ba, wanda in an masa kallon na tsanaki, tuni wannan dalili ya kai, saboda…
Read More
Raɗɗa ya buƙaci ‘yan Nijeriya su kawar da bambancin dake tsakanin su

Raɗɗa ya buƙaci ‘yan Nijeriya su kawar da bambancin dake tsakanin su

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya al'umar Jihar Katsina da ma ƙasar nan baki ɗaya murnar zagayowar Babbar Sallah ta shekarar 2023. A saƙonsa na Sallah, Gwamnan ya buƙaci 'yan Nijeriya da su yi amfani da bikin Babbar Sallah na wannan shekarar wajen farfaɗo da danƙon zumunci da ƙaunar juna a tsakanin su, ba tare da la'akari da bambancin addini, ƙabilanci ko wata aƙida dake a tsakanin su. Ya ce, "Ba tare da la'akari da bambancin addini ƙabilanci ko wata aƙida ba, dole mu rungumi juna a matsayin abu ɗaya, ya zama…
Read More
Rabuwar aure da ƙalubalensa

Rabuwar aure da ƙalubalensa

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da haɗuwa a wannan makon! Sannunku da jimirin karatun jaridar Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu yi magana a kan yadda wasu lokuta a rayuwar aure da zaman yake yin zafi ya ƙi daɗi, har ma su yanke shawarar su rabu da juna. Ko ɗaya ya dinga riyawa a zuciyarsa ba mafita illa ya rabu da ita ko ita ta dinga tunanin idan ba ta rabu da shi ba ba ta da sauran wani 'yanci. Eh haka ne, akwai wasu lokuta na rayuwar aure da suke zuwa ku ji sam ba kwa jin daɗin…
Read More
Babu wahala ga duk wata sana’ar da ka sa kanka – Maryam Ceetar

Babu wahala ga duk wata sana’ar da ka sa kanka – Maryam Ceetar

"Tun Ina ƙarama nake da burin neman na kaina" DAGA MUKHTAR YAKUBU A daidai lokacin da a ke ganin mata an bar su a baya wajen harkar kasuwanci da sana'o'i tare da kiraye kirayen da ƙungiyoyin kare muradun mata suke yi na mata su tashi su nemi na kan su, an samu wata jaruma a cikin mata wadda ta zama kallabi tsakanin rawuna. Maryam Isah Abubakar Ceetar mace ce da take harkokin kasuwanci da sana'o'i na kanta wadda har ta kai a yanzu tana da kamfanin gine-gine da kuma qawata gidaje, baya ga harkokin kasuwanci da take yi. Ganin yadda…
Read More