Editor

9513 Posts
Babbar Sallah: Yadda Shugaba Tinubu ya halarci Sallar Idi

Babbar Sallah: Yadda Shugaba Tinubu ya halarci Sallar Idi

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun al'ummar musulmin duniya wajen gabatar da Sallar Idi ta Babbar Allah wadda aka yi a ranar Laraba, 10 ga watan Zul-Hijja wanda ya yi daidai da 28 ga watan Yunin 2023. Tinubu ya yi Sallar Idinsa ne a filin Idi da ke Obalende a Dodan Barracks, Victoria Island, Legas. Imam Suliman Abuo-Nolla shi ne wanda ya jagoranci gabatar da sallar mai raka'o'i biyu. Ga ƙarin hotuna:
Read More
Marigayi Mamman Shata: Shekaru shekaru 24 da rasuwarsa

Marigayi Mamman Shata: Shekaru shekaru 24 da rasuwarsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A rana mai kamar ta yau (18 ga watan Yuni 1999) Allah Ya yi wa shahararren mawaqin Hausa Dr. Mamman Shata Katsina Rasuwa. Bayani Kaɗan A Kan Shata: An dai haifi Marigayi Alhaji Dr. Mamman shata a garin Musawa, A Shekarar 1923, kuma ya girma a katsina wato Jihar Katsinan Tarayyar Nijeriya. Ya yi ƙaura zuwa garin kano ya kuma rasu a ranar 18 Yunin Shekarar 1999 an binne shi a garin Daura kamar yadda yabar wasiya, To a lokacin da Marigayi Dr. Mamman Shata ya ke a raye akwai tambayoyi makamanta waxanda Malam Ɗan’zumi ya…
Read More
Shahara da karɓuwa ce babbar nasarar kowanne jarumi – Baba Ɗan Audu

Shahara da karɓuwa ce babbar nasarar kowanne jarumi – Baba Ɗan Audu

Daga AISHA ASAS A kowacce irin sana’a da mutum zai yi, yakan yi fatan samun nasara da kuma ɗaukaka, kamar yadda masu azancin magana ke cewa, “ka nemi sa’a ba iyawa ba, domin sa’a ta fi iyawa.” Da wannan ne ake samun wasu su fi wasu a harkokin da suka sa a gaba. Da yawa sun fahimci nasara daga Allah ce, duk ƙoƙarinka za ka iya tarar da wanda bai fi ka ba ya zama sama da kai, wannan ne ke taimako wurin yaƙar shaiɗan wurin hana shi sanya ma ka hassadar waɗanda suka fi ka. Hakazalika, akan samu wasu…
Read More
Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun kwana biyu

Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun kwana biyu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba, 28 da Alhamis, 29 ga Yunin 2023 a matsayin ranakun hutun gama-gari ga ma'aikata albarkacin bikin Babbar Salla (Eid-El-Kabir). Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Babban Sakataren Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Oluwatoyin Akinlade, ya fitar. Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Tarayya ta bayyana Laraba, 28 da Alhamis, 29 ga Yuni, 2023 a matsayin ranakun hutu domin bikin Eid-el-Kabir. "Kuma muna taya al'ummar Musulmi na gida da waje murnar bikin." Akinlade ya yi kira ga al'ummar Musulmi da ma ɗaukacin 'yan Nijeriya da su yi sadaukarwa don cigaban ƙasa da al'ummarta. Kazalika,…
Read More
Gwamnan Kano ya dakatar da ma’aikatan da Ganduje ya ɗauka

Gwamnan Kano ya dakatar da ma’aikatan da Ganduje ya ɗauka

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da albashin ma’aikata 10,800 da tsohon Gwamnan jihar, Umar Ganduje, ya ɗauka a ƙarshen mulkinsa. Babban Akanta na jihar Kano, Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai, Ya ce gwamnan ya dakatar da biyan albashin ne har sai an tantance su domin gane waɗanda suka cancata da kuma 'yan alfarma. Abdulkadir Abdulsalam ya kuma ce duk ma’aikatan ƙananan hukumomi da tsohuwar gwamnati ta mayar ma’aikatan jiha a ƙarshen wa’adinta za su ci gaba da karɓar albashinsu na ƙaramar hukuma. Sai dai kuma ya…
Read More
Gwamnan Kano ya rantsar da kwamishinoninsa

Gwamnan Kano ya rantsar da kwamishinoninsa

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA Gwmana Abba Kabir Yusif na Jihar Kano, ya rantsar da sabbin kwamshinoninsa su 17 a ra a ranar Litinin. Daga cikin sabbin kwamshinonin har da Hon. Umar Haruna Doguwa (Ɗan Aljanna). Cikin jawabin da ya gabatar yayin tabbatar da naɗin a gidan gwamanatin jihar Kano, Gwamna Abba Kabir ya yi kira ga sabbin kwamshinonin da su zama jakadun ƙwarai a sha'anin aikinsu, sannan su kasance masu kare mutuncin gwamnatin jihar. Ga ƙarin hotuna daga wajen taron:
Read More
Za mu samar da dabarun daƙile ƙalubalen tsaro da ke addabar makiyaya – Miyetti Allah

Za mu samar da dabarun daƙile ƙalubalen tsaro da ke addabar makiyaya – Miyetti Allah

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar makiyaya a Nijeriya ta Miyetti Allah (MACBAN), ta ce ta ɓullo da dabarun daƙile ƙalubalen tsaro da ke addabar makiyaya. A cikin wata sanarwar da ta fitar a Abuja cikin makon nan, ta ce waɗannan dabarun sune sakamakon taron da majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) ta gudanar. Sanarwar ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar ta MACBAN na ƙasa, Alhaji Hussein Bosso da sakataren ƙasa, Baba Ngelzarma. Ya bayyana cewa, taron ya tattauna ne kan ƙalubalen tsaro da makiyaya ke fuskanta a faɗin ƙasar da kuma batutuwan da suka shafi zavukan ƙasa na MACBAN mai zuwa.…
Read More
Ƙungiyar ‘Neighborhood Development Associantion’ ta gudanar da ayyukan cigaban al’umma

Ƙungiyar ‘Neighborhood Development Associantion’ ta gudanar da ayyukan cigaban al’umma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cigaba da gudanar da muradun da suka assata, Ƙungiyar 'Kwanar Bushara Neighborhood Development Associantion' da ke Unguwar Rigasa ta Jihar Kaduna ta gudanar ayyukan gyaran tituna domin jin daɗin jama'a. Ƙungiyar ta kwashe makonni biyu tana fitowa duk ranar Lahadi domin cike ramukan da suka addabi direbobi da sauran jama'a a kan babban titin Maƙarfi Road, inda suka rinƙa bi suna cike manyan ramuka da ƙanana. Wakilinmu da ya shaidi wannan aiki ya shaida mana cewa, mambobin ƙungiyar sanye da rigunan da ake alamta su ne suka rinƙa bi suna haƙewa tare da cike ramukan…
Read More
Tsofaffi na buƙatar tallafin gaggawa a Nijeriya – NSCC

Tsofaffi na buƙatar tallafin gaggawa a Nijeriya – NSCC

Shugabar Ƙungiyar Kula da Tsofoffi ta Ƙasa (NSCC), Dokta Emem Omokaro, ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa hanyoyin da tsare-tsare don tabbatar da adalci ga tsofaffi ƙasar nan. Omokaro, ta yi wannan kiran a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya yi kira da a haɗa kai don tabbatar da adalci ga tsofaffi. Taron masu ruwa da tsaki da aka yi wa laƙabi da ‘Elder Justice’, cibiyar ce ta shirya tare da haɗin gwiwar hukumar kare haƙƙoƙin Dan Adam ta ƙasa da kuma Majalisar bada agaji ta Shari’a. Kamfanin…
Read More
Dandalin shawara: Mahaifina ya ce ba zan yi aure ba har sai na mallaki gida na kaina

Dandalin shawara: Mahaifina ya ce ba zan yi aure ba har sai na mallaki gida na kaina

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. 'Yar'uwa barka da wannan lokaci. Ya iyali. Sannu da ƙoƙari. Don Allah shawara nake nema kan matsala ta. Wallahi na yi karatu har na kammala digiri na farko, na yi bautar ƙasa har yanzu na kai na samu aiki a ƙaramar hukuma, kusan shekara ɗaya da rabi kenan. To shi ne na yi ɗan tanadi da ɗan abinda nake samu na albashi zuwa 'yar buga-buga da nake yi na haɗa lefe, na tanadi kuɗi har dubu ɗari, sannan na je ga mahaifina kan sha’anin nema min aure. Anan fa…
Read More